An Samu Matsala: Alkali Ya Janye Hannunsa daga Shari'o'in Malami da Hukumar EFCC

An Samu Matsala: Alkali Ya Janye Hannunsa daga Shari'o'in Malami da Hukumar EFCC

  • An samu tsaiko a shari'ar tsohon ministan shari'a kuma babban lauyan gwamnatin tarayya, Abubakar Malami da gwamnatin tarayya
  • Alkalin da ke jagorantar shari'o'i biyu da ake yi tsakanin Malami da hukumar EFCC ya janye hannunsa daga dukkan shari'o'in
  • Mai shari'a Obiora Egwuatu, alkali a babbar kotun tarayya dake Abuja, ya bayyana dalilin janyewarsa a zaman kotun na ranar Alhamis

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Mai shari'a Obiora Egwuatu, alkali a babbar kotun tarayya dake Abuja, ya janye daga jagorantar shari'o'in da suka shafi Abubakar Malami da gwamnatin tarayya.

Rahoto ya bayyana cewa Mai shari'a Obiora Egwuatu ne yake jagorantar shari'o'i biyu da ake yi tsakanin tsohon ministan shari'ar da Hukumar EFCC.

Alkali ya janye hannunsa daga shari'ar Abubakar Malami da EFCC
Abubakar Malami a babbar kotun tarayya da ke Abuja lokacin da EFCC ta gurfanar da shi. Hoto: Economic and Financial Crimes Commission
Source: Facebook

Alkali ya janye daga shari'ar Malami da EFCC

Channels TV ta rahoto cewa Mai shari'a Egwuatu ya bayyana matsayarsa ne a zaman kotun na ranar Alhamis, 12 ga Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan

Babu sauki: Sojoji sun yi raga raga da 'yan ta'addan ISWAP, an kashe tsageru da dama

Mai shari'a Egwuatu ya bayyana cewa ya yanke shawarar janye jikinsa ne saboda dalilai na kansa da kuma tabbatar da adalci a shari'ar.

A lokacin da aka karanto shari'ar da ta shafi bukatar karshe ta kwace kadarori 57 da suke da alaka da Malami, Mai shari'a Egwuatu ya ce ba zai saurare ta ba, kuma ya janye daga dukkan shari'o'in da suka shafi tsohon ministan.

An ruwaito cewa, a baya-bayan nan ne babban jojin babbar kotun tarayya, Mai shari'a John Tsoho ne ya tura shari'o'in biyu ga Mai shari'a Egwuatu.

Da farko, Mai shari'a Emeka Nwite ne yake jagorantar wadannan shari'o'i, kafin a mayar da su ga Egwuatu lokacin da aka tafi hutun Kirsimeti.

Tuhume-tuhumen da ake yi wa Malami

Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa (EFCC) tana tuhumar Malami ne da laifuffuka 16 waɗanda suka haɗa da zargin halasta kuɗaɗen haram.

A watan Disambar shekarar 2025, hukumar EFCC ta gano kadarori 57 a darajarsu ta kai Naira biliyan 212 waɗanda take zargin na tsohon ministan ne.

Kara karanta wannan

Fitacciyar ƴar siyasa, Naja'atu Muhammad ta kausasa harshe a kan siyasar Pantami

Waɗannan kadarorin, waɗanda suka haɗa da otal-otal, gidajen zama, filaye, makarantu, da kuma wuraren buga takardu, suna a sassan jihohin Kebbi, Kano da kuma birnin Abuja.

Yanzu ana jira a ga alkalin da zai ci gaba da shari'ar Malami da EFCC
Harabar babbar kotun tarayya da ke Abuja, inda ake shari'ar EFCC da Malami. Hoto: @FederalHigh
Source: UGC

'Yan Najeriya za su yi zaman jira

Binciken hukumar ya mayar da hankali ne kan lokacin da Malami ya shafe a matsayin babban lauyan Najeriya kuma ministan shari'a na tsawon shekaru takwas, in ji rahoton The Cable.

Janyewar Mai shari'a Obiora Egwuatu daga shari'o'in EFCC da Malami ya bar mutane a cikin duhu, musamman ganin a kwanan nan aka sake cafke Malami bayan samun beli.

Yanzu haka ana dakon ganin alkalin da za a miƙa wa wadannan manyan shari'o'in domin ci gaba da sauraron hujjoji da kuma kare kai daga Malami.

Malami ya dauki mataki kan EFCC

A wani labari, mun ruwaito cewa, Abubakar Malami ya bukaci kotu ta soke umarnin kwace kadarorinsa 57 yana mai cewa ya ayyana su a CCB lokacin yana mulki.

Tsohon babban lauyan gwamnatin tarayyar ya bayyana cewa wasu daga cikin gidajen gado ne da mahaifinsa ya bari, kuma EFCC ta boye wa kotu gaskiya.

A halin yanzu, ana jiran ganin matakin da kotun za ta dauka da kuma martanin da hukumar EFCC za ta yi kan wannan sabon yunkuri na tsohon ministan shari'ar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com