Bayan Turo Sojoji, Amurka Za Ta Kafa 'Tashar Jiragen Yaki' a Jihar Arewacin Najeriya

Bayan Turo Sojoji, Amurka Za Ta Kafa 'Tashar Jiragen Yaki' a Jihar Arewacin Najeriya

  • Kasar Amurka ta fara tattaunawa da Najeriya domin kafa sansanin sojoji, wanda za ta rika zuba wa jirage marasa matuka mai
  • Rahotanni sun nuna cewa Amurka ta bukaci kafa wannan wuri a Abuja ko Legas, amma gwamnatin tarayya ta ki amincewa saboda wasu dalilai
  • Wani jami'i da ke da masaniya kan lamarin ya ce a yanzu an fara duba yiwuwar bude wannan tasha a Arewa maso Gabashin Najeriya

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Duk da matsin lambar diflomasiyya da ake samu, Najeriya da Amurka sun samu matsaya guda wajen ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar soji.

A watan Disamba, Amurka ta taimaka wajen kai hare-hare kan ‘yan ta’adda a jihar Sokoto da ke Arewa maso Yamma, a wani aiki na haɗin gwiwa da Najeriya.

Shugaba Trump.
Shugaban kasar Amurka, Donald Trump da wasu jirage marasa matuka Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rahoton Daily Trust ya nuna cewa a nan gaba, rundunar sojin Amurka ta ce za ta rika samar da bayanan sirri domin taimaka wa hare-haren sama na Najeriya.

Kara karanta wannan

Hedkwatar tsaro ta jero abubuwan da sojojin Amurka 200 za su yi idan suka shigo Najeriya

Ko da yake tura sojoji 200 na nuni da ƙara faɗaɗa wannan haɗin gwiwa, Mai magana da yawun Hedikwatar Tsaro, Manjo Janar Samaila Uba, ya ce:

"Sojojin Amurka ba za su shiga yaƙi kai tsaye ko gudanar da ayyukan soji ba.”

Shirin kafa tashar jirage a Najeriya

Wani jami’i da ke da masaniya kan tattaunawa tsakanin ƙasashen biyu ya shaida wa The Cable cewa Amurka ta buƙaci a ba ta damar kafa wata tasha da za ta rika zuba wa jiragenta mai a Najeriya bayan dawowarsu daga Accra, Ghana.

Ana iya zuba mai a jiragen marasa matuƙi ta hanyoyi daban-daban, gwargwadon nau’insu da irin man da suke amfani da shi, domin tsawaita lokacin aikinsu fiye da iyakar batir ko tankin man da suke ɗauka.

Yawancin jiragen marasa matuƙa na kasuwanci ana cika musu batir ko mai ne a ƙasa a wuraren da aka tanada.

Wane wuri Amurka za ta kafa tasha a Arewa?

Rahoton ya nuna cewa tattaunawar Najeriya da Amurka ta yi nisa, kuma an ware wata jiha a yankin Arewa maso Gabas domin kafa wannan tasha.

Kara karanta wannan

Hafsun sojoji ya fadi abin da ke jiran wadanda suka kitsa juyin mulki

Majiyar ta ƙara da cewa Amurka ta fara gabatar da bukatar kafa tashar a Legas ko Abuja, amma aka ƙi amincewa da hakan saboda dalilai masu sarkakiya.

Daga bisani aka zaɓi yankin Arewa maso Gabas, kasancewar a can ne ake gudanar da ayyukan jirage mara matuƙi na Najeriya.

Ana sa ran tashar za ta ba jami’an Amurka damar tashi daga Ghana, wadda ke zama cibiyar jigilar kayan sojin Amurka a Afirka domin tsara yadda za su taimaka wa dakarun Najeriya.

Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a gidan gwamnatin Najeriya Hoto: @OfficialABAT
Source: Twitter

Ayyukan sojojin Amurka a Najeriya

A wani rahoton, kun ji cewa Hedkwatar tsaron kasa ta fito ta yi bayani yayin da aka fara nuna fargaba kan shirin Amurka na turo karin sojoji 200 zuwa Najeriya.

Mai magana da yawun Hedikwatar Tsaro ta Najeriya, Manjo Janar Samaila Uba, ya tabbatar da shirin turo sojojin Amurka 200 Najeriya,

Jami’an Najeriya da na Amurka sun ce sojojin za su taimaka ne wajen horas da dakarun Najeriya a yaƙin da suke yi da ƙungiyoyin yan tada kayar baya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262