Fasto Ya Rubuta wa Majalisar Amurka Wasika kan Jifan Kwankwaso da Zargi

Fasto Ya Rubuta wa Majalisar Amurka Wasika kan Jifan Kwankwaso da Zargi

  • Fasto kuma dan siyasa, Isaac Idahosa ya rubuta takarda ta musamman ga majalisar kasar Amurka game da Sanata Rabiu Kwankwaso
  • Isaac Idahosa ya yi magana ne bayan wasu 'yan majalisar Amurka sun bukaci a kakaba wa Rabiu Kwankwaso takunkumi da hana shi biza
  • Limamin ya bayyana cewa Amurka bata samu sahihan bayanai game da Kwankwaso ba, ya kuma fadi irin alakar da ya yi da wanda ake zargin

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Abokin takarar Sanata Rabiu Kwankwaso a zaben shugaban kasa na 2023, Fasto Isaac Idahosa ya tura takarda ga majalisar dokokin Amurka.

Fasto Isaac Idahosa ya bayyanawa majalisar Amurka cewa a matsayinsa na wanda yake jagorantar harkokin addinin Kirista, ya san Kwankwaso mutumin kirki ne.

Kara karanta wannan

Da mamaki: Bulama ya ga kuskuren amurka kan zargin kwankwaso da matsawa kiristoci

Rabiu Musa Kwankwaso da Isaac Idahosa
Rabiu Kwankwaso ya daga hannun Fasto Isaac Idahosa a taron siyasa. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanan da Faston ya yi ne a wani sako da hadimin Sanata Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a shafinsa na Facebook.

Waskikar Fasto ga majaliar Amurka

A wasikar da Idahosa ya rubuta, ya ce ya tura musu sakon ne a matsayinsa babban malamin addinin Kirista da ya jagoranci kafa coci a Najeriya.

Ya bayyana cewa:

"A matsayina na malamin addinin Kirista da ya tsaya takarar mataimakin shugaban kasa tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso a zaɓen shugaban ƙasa na 2023 a ƙarƙashin tutar jam’iyyar NNPP,"
"Ina bayyana takaici ne dangane da kudirin dokar hana biza da aka gabatar, wanda ake shirin saka sunan Sanata Kwankwaso a ciki."
"Ina da ƙwarin gwiwar cewa wannan mataki ya samo asali ne daga bayanai marasa inganci game da halayensa da nasarorinsa."

Idahosa ya ce ya tabbatar da jajircewar Sanata Kwankwaso wajen yi wa jama'a hidima da shugabanci ba tare da nuna bambanci ba.

Kara karanta wannan

Kwankwaso ya yi magana daga India ana caccaka tsinke da Amurka

Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
Jagoran NNPP, Rabiu Kwankwaso a wani taron Kwankwasiyya. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Mukaman da Kwankwaso ya rike

Ya bayyana cewa Sanata Kwankwaso gogaggen ɗan siyasa ne da ya riƙe manyan mukamai a tarihinsa na siyasa a Najeriya.

Ya ce:

"Ya rike muƙaman mataimakin shugaban majalisar wakilai, gwamna, ministan tsaro, sanata da kuma ɗan takarar shugaban kasa.
"Abin lura shi ne, ba a taɓa danganta shi da tsattsauran ra’ayin addini, kashe-kashe ko tarzoma ba,"
"Haka kuma, ba a taɓa haɗa shi da wata ƙungiya da ake kallonta a matsayin mai tsattsauran ra’ayi a ciki ko wajen Najeriya ba."

Kiran Fasto ga Amurka kan Kwankwaso

Faston ya bayyana cewa mafi yawan ‘yan Najeriya sun yi mamaki da wannan mataki kasancewar mutum ne da ba a san shi da hakan ba.

Ya ce:

"Ina kira ga majalisar dokokin Amurka da ta sake duba wannan lamari tare da cire sunan Sanata Kwankwaso."
"Ina roƙon Majalisa da ta sake nazarin wannan shawara domin tabbatar da adalci."

Kara karanta wannan

Takunkumin Amurka: Yadda Kwankwaso ya kira sunan Trump ya caccake shi

Kwankwaso ya magantu daga India

A wani labarin, mun kawo muku cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara kasar India bayan zuwa Dubai a makon da ya wuce.

Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa ya kai ziyara ne domin tattauna hanyoyin bunkasa ilimi mai zurfi a Kano da Najeriya baki daya.

An hango Kwankwaso a India ne a daidai lokacin da wasu 'yan majalisar Amurka suka fara masa barazana kan zargin tauye hakkin addini.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng