Kwankwaso Ya Yi Magana daga India ana Caccaka Tsinke da Amurka

Kwankwaso Ya Yi Magana daga India ana Caccaka Tsinke da Amurka

  • Yayin da ake magana game da Rabiu Kwankwaso kan takunkumin da Amurka ke son kakaba masa, an hango jagoran NNPP a wata jami'a a India
  • Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa ziyayar da ya kai kasar na da alaka da burinsa na inganta ilimi a Kano da ma Najeriya baki daya
  • Kafin tafiya India, Kwankwaso ya halarci wani taron 'yan Kwankwasiyya a Dubai, inda ya bukaci su cigaba da zama jakadun na gari a duk inda suke

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

India - Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya kai ziyara jami'ar Mangalayatan da ke kasar India a daidai lokacin da Amurka ke masa barazana.

A bayanin da ya yi, Sanata Kwankwaso ya bayyana cewa ziyayarsa jami'ar na da alaka da inganta ilimi a Kano da sauran sassan Najeriya.

Kara karanta wannan

Takunkumin Amurka: Yadda Kwankwaso ya kira sunan Trump ya caccake shi

Sanata Rabiu Kwankwaso a jami'ar India
Yadda aka tarbi Rabiu Kwankwaso a jami'ar India. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Legit Hausa ta tattaro bayanin da Kwankwaso ya yi ne a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Facebook a yau Alhamis, 12 ga Fabrairun 2026.

Maganar Kwankwaso daga India

Sanata Rabiu Kwankwaso ya bayyana cewa a ranar Laraba, 11 ga Fabrairun 2026 ya ziyarci jami'ar Mangalayatan da ke jihar Uttar Pradesh a India.

Da yake bayani kan dalilin ziyarar, Kwankwaso ya ce:

"A ci gaba da ƙoƙarin ɗaga darajar ilimi da faɗaɗa damar samun ingantaccen karatu a Najeriya, na samu damar ziyartar Jami’ar Mangalayatan da ke Aligarh (Beswan), Jihar Uttar Pradesh ta ƙasar India, a ranar Laraba.
"Wannan ziyara na da nufin ƙarfafa haɗin gwiwa mai ma’ana a fannonin bincike, fasaha da musayar ilimi tsakanin cibiyoyin karatu na Najeriya da takwarorinsu na India, domin bunƙasa ci gaba da ƙirƙire-ƙirƙire a matakin ilimi mai zurfi."

Kwankwaso ya godewa jami'ar India

A wani sako da hadimin Kwankwaso, Saifullahi Hassan ya wallafa a Facebook, jagoran NNPP ya mika godiya ga jami'ar Mangalayatan bisa tarbar da ta masa.

Kara karanta wannan

APC ta ajiye bambanci, ta shiga wa Kwankwaso fada da Amurka

Kwankwaso ya bayyana cewa:

"Ina miƙa godiya ta musamman ga daukacin al’ummar Jami’ar Mangalayatan, musamman shugaban jami’ar, da mataimakin shugaban jami’ar,"

Kwankwaso ya kara mika godiya ga wasu shugabannin jami'ar da suka hada da shugaban majalisar jami’ar da sauran ma’aikata saboda tarba mai cike da karamci, kyakkyawar liyafa da girmamawa da suka nuna masa.

Sanata Rabiu Kwankwaso a jami'ar India
Rabiu Kwankwaso na tattaunawa da jami'an jami'ar India. Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

Bai ce komai kan Amurka ba

A cikin sakon da Kwankwaso da hadiminsa, Saifullahi Hassan suka wallafa, babu wani martani ga 'yan majalisar Amurka da suka fara masa barazanar kakaba takunkumi.

Jama'a da dama na jiran jin ta bakin Kwankwaso da kansa, duk da cewa wasu kungiyoyi, jam'iyyun siyasa da mutane na fitowa suna ba shi kariya.

Amurka: Kwankwaso ya caccaki Trump

A wani labarin, kun ji cewa an fara magana kan dalilan da suka sanya wasu 'yan majalisar Amurka fara barazana ga Rabiu Musa Kwankwaso.

Farfesa Farooq Kperogi ya yi ikirarin cewa wata magana da Kwankwaso ya yi a kan shugaban Amurka, Donald Trump a 2025 ce ta jawo batun.

A lokacin da Trump ya yi zargin kisan Kiristoci a Najeriya, Sanata Rabiu Kwankwaso ya fito karara ya bayyana cewa sam ba haka abin yake ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng