Jaafar Jaafar Ya Ja Hankalin Amurka, Ya Nuna Shaidar da Kiristoci Suka Yi wa Kwankwaso
- Wasu fitattun ‘yan Najeriya sun soki kudirin dokar Amurka da ya ambaci Rabiu Kwankwaso a cikin masu muzgunawa kiristoci
- Jaafar Jaafar, fitaccen dan jarida ya aika wa Rilley Moore sakonnin wasu Kiristoci daga Kano a kan Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso
- Moore da ke gaba-gaba a cikin masu bibiyar zargin kisan kiristoci a Najeriya ne ya tabbatar da aika kudiri a gaban majalisar Amurka
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wasu fitattun ‘yan Najeriya, daga ciki har da Kiristoci daga jihar Kano, sun fito kare tsohon Gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Sun yi martani a kan zargin da kwamitin majalisar Amurka ya yi na tsoma sunan Sanata Kwankwaso a cikin jerin mutanen da ke da hannu a muzgunawa kiristoci.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa kwamitin Majalisar Dokokin Amurka ya aike da kudirin doka da ke neman a sanya shi a cikin jerin mutanen da za a kakaba wa takunkumi.
Jafaar Jafaar ya yi martani ga Rilley Moore
Jaafar Jafaar ya wallafa a shafin X cewa an yi kuskuren sanya sunan Kwankwaso a cikin kudurin sanya takunkumi a kan masu muzguna wa Kiristoci a Najeriya
Sai dai a sakonni da aka wallafa a shafukan sada zumunta, wasu ‘yan Najeriya sun bayyana cewa sunan Kwankwaso bai kamata ya shiga cikin irin wannan kudiri ba.
Da yawa daga cikin waɗanda suka yi martani da suka hada da Musulmi da Kirista sun ce a zamanin mulkinsa, Kwankwaso bai muzguna wa kowane Kirista ba.

Source: Twitter
Wani mai suna Richard Joseph Ahonkhai ya ce:
“Kwankwaso ya kare Kiristoci a Kano lokacin da yake gwamna daga 1999 zuwa 2023.”
Kwankwaso: Martanin kiristoci ga kudirin Amurka
JJ Omojuwa wanda ya shahara a kafafen sadarwa na zamani ya ce babu dalilin da zai sa a zargi Kwankwaso da irin wannan laifi na zaluntar Kiristoci ta kowace fuska.
Ya ce:
“Ba tare da la’akari da siyasa ba, wannan lokaci ne da ya kamata a tsaya tare da Sanata Rabiu Kwankwaso. Babu wani dalili da zai sa sunansa ya bayyana a cikin wannan takarda."
Farfesa Moses Ochonu wanda yake karantarwa a Amurka ma ya nuna mamakinsa kan kudirin. Ya ce:
“Ban fahimci dalilin da ya sa ake son kakaba wa Kwankwaso takunkumi ba bisa batun shari’a ba."
Farfesan ya kara da cewa, a fahimtarsa, Kwankwaso ya aiwatar da wasu manufofi ne saboda matsin lambar siyasa, ba wai saboda tsattsauran ra’ayi na addini ba.
Haka kuma, wani Daniel Mikah Magaji, ya bayyana kansa a matsayin Kirista da aka haifa kuma aka taso a Kano.
Ya ce:
"Kwankwaso ba mai tsattsauran ra’ayin addini ba ne. Ni Kirista ne, babu wani gwamna da ya kare Kiristoci da wadanda ba ‘yan asalin Kano ba kamar shi.”
Magaji ya ce:
"Wa ke ba gwamnatin Amurka shawara?”
Daga bisani, Jaafar Jaafar, ya bukaci dan majalisar Amurka Riley Moore da ya sake duba bayanan da ya samu.
A cewarsa:
"Ku karanta shaidun Kiristocin Najeriya game da Kwankwaso. Kun yi kuskure.”
Jam'iyyar APC ta tsaya wa Kwankwaso
A wani labarin, kun ji cewa APC ta yi martani kan kudirin da wasu ‘yan Majalisar Dokokin Amurka suka gabatar na neman a kakaba wa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso takunkumi.
APC ta bayyana cewa ba daidai ba ne a tauye wa dan Najeriya hakkinsa bisa zarge-zargen da ba a tabbatar ba, tana mai cewa ya kamata a yi adalci.
Wasu ‘yan majalisar Amurka, ciki har da Chris Smith da Riley Moore sun gabatar da kudirin da ke neman a dauki mataki kan wasu ‘yan Najeriya bisa zargin take hakkin ‘yancin addini.
Asali: Legit.ng


