Kamfanin BUA Ya ba 'Dan Abdussamad Rabi'u Babbar Kujera
- Kamfanin BUA Foods ya nada Isyaku AbdusSamad “Khalifa” Rabiu a matsayin babban Jami’i mai kula da sayayya da sauran dabarun aiki
- Nadin ya fara aiki daga ranar 29 ga Janairu, 2026, lamarin da ya ja ra'ayin yan Najeriya a kan ci gaban kamfanin da gadon kasuwanci
- Kamfanin ya ce yana ci gaba da karfafa shugabanci domin bunkasa kasuwanci da dorewar ci gaban kamanin BUA foods a duniya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Lagos – Kamfanin BUA Foods ya sanar da sabon nadin shugabanci inda aka ba Isyaku Abdulsamad “Khalifa” Rabiu babban matsayi.
Kamfanin ya sanar da cewa an nada Khalifa, dan Shugaban rukunin kamfanin BUA a matsayin babban jami'i mai kula da sayayya da sauran dabaru.

Source: Facebook
Sakon nadin na kunshe a cikin wata wasika da Haroun Muhammed ya sanya a shafinsa na Facebook.
An nada dan Shugaban kamfanin BUA mukami
Kamfanin BUA ya fitar da sanarwar nadin a ranar 10 ga Fabrairu, 2026, a birnin Legas, yayin da ya fara aiki tun daga ranar 29 ga Janairu, 2026.
Ya bayyana cewa wannan nadin na zuwa ne a wani muhimmin lokaci da kamfanin BUA Foods ke kara fadada shirinsa na dogon lokaci domin bunkasa manyan bangarorin kasuwancinsa.
A cewar kamfanin, kara karfin shugabanci zai taimaka wajen inganta tsare-tsaren aiki, rage farashi, da kuma karfafa juriya a harkar samar da kayayyaki.
A sabon mukaminsa, Khalifa zai jagoranci dukkannin harkokin sayayya na kamfanin a matakin duniya, tare da kula da manyan tsare-tsaren ayyuka da za su bunkasa inganci da dorewar ci gaba.
Aikin da ke gaban Khalifa a kamfanin BUA
Haka kuma zai taimaka wajen karfafa tsarin samar da kayayyaki da tabbatar da cewa kamfanin na tafiya daidai da manufofinsa.
Sanarwar ta kara da cewa Khalifa ya rike mukamin daraktan ayyuka na musamman a kamfanin BUA kafin wannan sabon nadi
A lokacin da yake wannan matsayi, ya jagoranci muhimman sauye-sauye a tsarin aiki, ya karfafa alakar kamfanin da masu samar da kayayyaki, tare da samar da ingantattun sakamako a ayyukan yau da kullum.

Source: Facebook
Ya taka muhimmiyar rawa wajen tsara sayen albarkatun kasa, musamman a bangaren sayen alkama. Haka kuma ya jagoranci kafa wata masana’antar sarrafa abincin dabbobi mai karfin ton 40 a awa guda.
Ya kasance cikin wadanda suka jagoranci dawo da kayayyakin shinkafar BUA a kasuwar Najeriya, tare da tallafa wa dandalin zamani da kamfanin ke amfani da su.
BUA ya tona masu jawo wa kasuwa matsala
A baya, mun wallafa cewa Shugaban kamfanin BUA Foods Plc, Alhaji Abdul Samad Rabiu, ya yi magana kan matsalar tsadar kaya da hauhawar farashi a Najeriya.
Alhaji Abdul Samad Rabiu ya tabo wannan batu ne yayin da yake jawabi a wani taron kamfaninsa na BUA a birnin Abuja a watan Satumba na shekarar 2024.
A jawabinsa, attajirin ya yabawa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, kan matakin da ya dauka na barin a rika shigo da kayan abinci daga waje domin samar da sauki a kasuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

