Bidiyo: Rigima Ta Kaure tsakanin Sanatan Kano da Wani Abokin Aikinsa a Majalisar Dattawa

Bidiyo: Rigima Ta Kaure tsakanin Sanatan Kano da Wani Abokin Aikinsa a Majalisar Dattawa

  • Rigima ta kaure tsakanin Sanata Rufai Hanga (Kano) da Sanata Onyekachi Nwaebonyi (Ebonyi) yayin wani zaman kare kasafin kudi
  • Tun ana cacar baki har ta kai ga buga guduma a kan tebur, yayin da Hanga ya gargadi Nwaebonyi da ya daina matsa tsawa
  • A wani bidiyo, an ga su Sanata Ali Ndume suna shiga tsakani domin dawo da natsuwa a dakin taron bayan kacamewar sanatocin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Rikici mai zafi ya barke tsakanin Sanata Rufai Sani Hanga da Sanata Onyekachi Nwaebonyi yayin da ake gudanar da zaman kare kasafin kudi na ma'aikatar ayyuka.

Zaman, wanda Sanata Hanga ya jagoranta a matsayinsa na mataimakin shugaban kwamitin, ya fara gudana cikin natsuwa, inda Ministan Ayyuka, David Umahi ke bayani.

Rigima ta barke a majalisar dattawa tsakanin Sanatan Kano da na Ebonyi
An samu yamutsi a majalisar dattawa lokacin da Sanata Jarigbe ya yi wasu zarge-zarge a ranar Talata, 12 ga Maris, 2024. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Sanata Rufai Hanga ya fusata Sanatan Ebonyi

Kara karanta wannan

Sanata Natasa ta tayar da kura a Majalisar Dattawa, ta fadawa sanata kalamai masu zafi

Takaddamar ta fara ne lokacin da Sanata Hanga ya katse Nwaebonyi yayin da yake yaba wa ministan tare da kira ga abokan aikinsa su yi hakan, in ji rahoton The Cable.

Cikin fushi da wannan magana ta Hanga, Sanata Nwaebonyi ya ce:

“Ba za ka iya hana ni magana ba bayan ka bar Sanata Adams Oshiomhole ya yi magana na mintuna 15 cif.
“Kada ka sake katse ni saboda ka bar Sanata Oshiomhole ya kwashe akalla mintuna 15 yana bayar da shawarwari da tambayoyi ba tare da an tsayar da shi ba.
“Ban ma yi ko mintuna biyar ba kana ce mani in yi sauri in kammala. Ba zan yi ba, kuma ka sani cewa, a matsayina na babban jami'i, zan iya karbe jagorancin zaman nan.”

Rigima ta kaure tsakanin sanatoci 2

Sanata Hanga, wanda shi ne mataimakin shugaban marasa rinjaye a majalisar, ya mayar da martani cewa Nwaebonyi ba shi da ikon karbe zaman, inda ya buga guduma ya umarce shi da ya yi shiru.

Cacar bakin ta tsananta lokacin da Nwaebonyi ya ce:

“Ni babban sanata ne na jam’iyya mai mulki wanda sanatan marasa rinjaye ba zai iya tsawatar masa ba. Ba za ka gaya mini abin da zan fada ba.”

Kara karanta wannan

Daminar bana: Kano da Jihohi 14 da za su fara samun ruwan sama da wuri a Najeriya

Sanata na Kano ya mayar da martani da cewa kuri’un da suka kawo shi majalisar sun ninka na Nwaebonyi har sau 10 idan aka kwatanta da abin da ya samu a Ebonyi.

Ya kuma zargi Nwaebonyi da "lashe takalmin maigidansa," yana nufin alakar siyasar sanatan da ministan, duba da cewa duka mutanen biyu sun fito ne daga jihar Ebonyi, in ji rahoton Vanguard.

An samu hayaniya a majalisar dattawa tsakanin Sanatan Kano da na Ebonyi.
Sanata Godswill Akpabio yana jagorantar zaman majalisar dattawa a Abuja. Hoto: Nigerian Senate
Source: Facebook

Bidiyon rigimar sanatan Kano da na Ebonyi

A wani bidiyo dake yawo, an ji Nwaebonyi yana daka wa Hanga tsawa. Hanga ya amsa da cewa, “Kada ka kuskura ka kara daka mini tsawa,” yayin da lamarin ya kara rincibe wa.

Nwaebonyi ya bayyana cewa, “Zan iya jagorantar wannan zaman,” kalaman da suka sa Hanga mayar da martani da cewa, “Baka isa ba, ni ma jami’i ne mai ikon jagorantar zaman.”

Wannan sabani ya dakatar da zaman na dan lokaci kafin aka samu daidaito aka ci gaba da tattaunawa kan abubuwan da aka sanya a gaba a zaman.

An samu daidaito ne bayan shiga tsakanin Sanata Ali Ndume, da Sanata Adamu Aliero, da kuma Akin Alabi wanda shi ne shugaban kwamitin ayyuka na majalisar wakilai.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun riƙewa minista wuta a kan 'bacewar' kayan Gwamnatin Tarayya

Kalli bidiyon a nan kasa, wanda Punch ta wallafa a shafinta na X:

Rigima ta kaure a zaman majalisar dattawa

A wani labari, mun ruwaito cewa, sanatoci sun barke da hayaniya a yayin muhawara kan dokar tura sakamakon zabe ta intanet kai tsaye daga rumfunan zabe.

Rahoto ya nuna cewa an dan samu hatsaniyar ne bayan shugabam Majalisar dattawa, Godswill Akpabio ya karanto wasu shawarwarin da aka gabatar.

Ana ci gaba da ce-ce-ku-ce kan gyaran dokar zabe da Majalisar dattawa ta yi a makon jiya, inda ta ki amincewa da wajabta tura sakamako nan-take ta intanet.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com