Ba Sauki: Sojoji Sun Yi Raga Raga da 'Yan Ta'addan ISWAP, an Kashe Tsageru da Dama

Ba Sauki: Sojoji Sun Yi Raga Raga da 'Yan Ta'addan ISWAP, an Kashe Tsageru da Dama

  • Dakarun sojojin Najeriya na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), sun yi arangama da 'yan ta'addan ISWAP a jihar Borno
  • Hazikan sojojin sun nuna bajinta ta hanyar tura 'yan ta'adda da dama zuwa inda ba a dawowa bayan an tafka gumurzu
  • Sojojin sun kuma samu nasarar ceto mutanen da 'yan ta'addan suka yi garkuwa da su tare da kwato tarin makamai da kekuna

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Borno - Dakarun hadin gwiwa na rundunar Operation Hadin Kai (OPHK), sun kashe ’yan ta’addan ISWAP a jihar Borno.

Dakarun sojojin sun hallaka 'yan ta'adda 16 a hanyar Gidan Kaji da ke kan titin Maiduguri zuwa Damboa a jihar Borno.

Sojojin Najeriya sun kashe 'yan ta'addan ISWAP a Borno
Babban hafsan sojoji kasa na Najeriya, Laftanar Janar Waidi Shaibu Hoto: @HQNigerianArmy
Source: Twitter

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami’in yada labarai na hedkwatar dakarun hadin gwiwa na Arewa maso Gabas, Laftanar Kanal Sani Uba, ya fitar ranar Talata, 10 ga watan Fabrairun 2026 a shafin X.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe bayin Allah, sun sace babban malami da wasu mutane 10

Sojoji sun yi nasara kan 'yan ISWAP

Haka kuma, dakarun sun kwace kekuna fiye da 20, da dumbin kayayyaki, makamai, da sauran kayan masarufi wadanda ake amfani da su.

Laftanar Kanal Sani Uba ya bayyana cewa an ceto mutane 11 da aka yi garkuwa da su a wurare daban-daban.

Ya kara da cewa an kama wasu mutane da ake zargi da kai wa kungiyar 'yan ta'addan SWAP kayayyaki, wadanda suke jigilar dumbin kwayoyi da nufin kai wa ’yan ta’addan a kewayen yankin Bukarti.

Sojoji sun gwabza da 'yan ta'addan ISWAP

“Dakarun hadin gwiwa na Operation Hadin Kai (OPHK) sun sake nuna bajinta ta hanyar dakile harin da ISWAP ta kai musu cikin gaggawa, tare da kaddamar da gagarumin harin ramuwar gayya.”
“Wannan mataki na bajinta ya rage karfin ’yan ta’addan sosai, ya dagula musu tsarin samar da kayan bukata, sannan ya kara tabbatar da kudurinh OPHK na ganin an ruguza dukkan sansanonin ’yan ta’adda a fadin Arewa maso Gabas.”

Kara karanta wannan

Ana jimamin harin Kwara, 'yan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya

- Laftanar Kanal Sani Uba

An kashe 'yan ta'addan ISWAP

Sanarwar ta cigaba da cewa:

"A ranar 5 ga watan Fabrairu, 2026, gab da tsakar dare, ’yan ta’addan ISWAP sun kai wani harin da bai yi nasara ba a sansanin sojoji da ke Auno.”
“Dakarun sashe na 1 sun fatattaki maharan ta hanyar amfani da dabarun yaki masu tsari. Biyo bayan wannan nasara, a ranar 9 ga watan Fabrairu, 2026, dakarun tare da hadin gwiwar dakarun sa-kai (CJTF), sun kaddamar da harin ramuwar gayya a hanyar Komala da ke karamar hukumar Konduga a jihar Borno.”
“Dakarun sun bi sawun ’yan ta’addan da suka gudu har zuwa yankin Gidan Kaji, inda suka kashe ’yan ta’adda 16, yayin da wasu da dama suka tsere da munanan raunuka.”
“Haka kuma dakarun sun kwace kekuna fiye da 20, da dumbin kayayyaki, makamai, da sauran kayayyakin da ke da muhimmanci ga ayyukan ’yan ta’addan.”
Sojoji sun ragargaji 'yan ta'addan ISWAP
Taswirar jihar Borno, tarayyar Najetiya Hoto: Legit.ng
Source: Original

'Yan ta'addan ISWAP sun yi sabon kwamanda

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun shiga uku, sojoji sun sha alwashi kan harin Kwara

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan ta'addan ISWAP sun nada sabon kwamanda bayan dakarun sojoji sun kashe shugabansu.

Majiyoyi sun an nada Abu Khalifa a matsayin sabon kwamanda kungiyar ISWAP a yankin Tumbuktu Triangle bayan kisan Julailib.

Kisan da sojoji suka yi wa Julailib ya sa aka gudanar da tattaunawar cikin gida kafin amincewa da sunan Abu Khalifa a matsayin sabon jagoransu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng