IFAD: Ministan Tinubu Ya Samu Gagarumar Nasara, An ba Shi Babban Mukami a Duniya

IFAD: Ministan Tinubu Ya Samu Gagarumar Nasara, An ba Shi Babban Mukami a Duniya

  • An zabi Ministan Harkokin Noma na Najeriya, Sanata Abubakar Kyari a matsayin shugaban Majalisar gudanar ta hukumar IFAD
  • Abubakar Kyari, wanda a baya ya rike mataimakin shugaban Majalisar IFAD, ya samu nasarar zama shugaba ne a taron da aka gudanar a Italiya
  • Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya taya ministan murna, yana mai cewa hakan alamu ne da ke nuna kokarin da yake yi a harkar noma

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Ministan Noma na Najeriya, Sanata Abubakar Kyari, ya zama sabon shugaban majalisar gudanarwa ta International Fund for Agricultural Development (IFAD).

An zaɓe shi ne a yayin zaman majalisar IFAD karo na 49 da aka gudanar a birnin Rome na ƙasar Italiya a ranar Talata, kamar yadda wata sanarwa daga ma’aikatar noma ta bayyana.

Abubakar Kyari.
Ministan Noma na Najeriya, Abubakar Kyari, a taron majalisar gudanarwa ta IFAD Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

The Cable ta ruwaito cewa sanarwar ta ce kafin wannan nasara, Kyari ya rike mukamin mataimakin shugaban majalisar, lamarin da ya taimaka masa kaiwa ga wannan matsayi mafi girma a cikin IFAD.

Kara karanta wannan

Sanata ya shawarci Musulmi kan yadda za su kalubalanci malamai

IFAD wata hukuma ce ta musamman ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya (UN), wadda ke mai da hankali kan rage talauci a yankunan karkara da inganta tsarin samar da abinci ta hanyar saka hannun jari da haɗin gwiwar ƙasashe.

Kyari ya yi alkawarin adalci da haɗin kai

Da yake karɓar mukamin, Kyari ya bayyana cewa zai gudanar da aikin cikin adalci, haɗa kai da kuma hangen nesa mai kyau.

“Na karɓi wannan nauyi cikin tawali’u kuma zan gudanar da wannan aiki cikin adalci da haɗa kai, tare da kare mutunci da amincin IFAD,” in ji Kyari.

Ministan ya ce zaɓensa na nuna yadda Najeriya ta ƙara ƙarfi a idon duniya ƙarƙashin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Ya ce ajandar “Renewed Hope” ta gwamnati ta bai wa harkar samar da abinci da sauye-sauyen noma muhimmanci, tare da daga kimar Najeriya a harkokin wadatar abinci na duniya.

Kyari ya kuma gode wa Karamin Ministan Noma, Aliyu Abdullahi; Babban Sakataren Ma’aikatar Noma, Marcus Ogunbiyi; da sauran jami’an ma’aikatar bisa goyon bayan da suka ba shi.

Tinubu ya taya Abubakar Kyari murna

Shugaba Bola Tinubu ya taya Abubakar Kyari murna kan wannan nasara, inda ya bayyana hakan a matsayin alamar amincewa da gyare-gyaren da yake jagoranta a fannin noma.

Kara karanta wannan

Magana ta fito: Sheikh Pakistan ya fadi dalilin murabus daga shugabancin NAHCON

A sanarwar da kakakin shugaban kasa, Bayo Onanuga ya wallafa a shafin X, Tinubu ya ce:

“Zaɓen Ministan Noma ya nuna amincewa da ƙwarewarsa da sauye-sauyen da yake aiwatarwa a harkar noma da samar da abinci a Najeriya,” in ji Tinubu.
Shugaba Tinubu.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a fadar gwamnatin Najeriya Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Yan Majalisa sun taso Ministan Noma

A wani labarin, kun ji cewa 'yan majalisar dokoki ta kasa sun matsa wa karamin Ministan noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi a kan jinkirin rabon taraktoci 2,000 ga manoma.

Sanatocin da 'yan majalisar wakilai na kwamitin hadin gwiwa sun tistiye shi domin ya yi bayani kan inda taraktoci 2,000 da gwamnatin tarayya ta kaddamar suka shiga.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne lokacin da ministan ya je majalisa domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa na shekarar 2026.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262