Bam Ya Tashi a Sakatariyar Jihar Bayelsa, An Dakatar da Ayyukan Gwamnati
- Rundunar yan sandan Jihar Bayelsa ta kama mutum daya bayan fashewar wani bam a sakatariyar gwamnatin jihar
- Kwamishinan yan sanda ya tabbatar da cewa babu wanda ya rasa ransa sannan an gano wani bam din da bai fashe ba
- Gwamnatin jihar ta dakatar da ayyukan ofis domin ba jami'an tsaro damar tantance lafiyar daukacin ma'aikatan sakatariyar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bayelsa - Wani abun fashewa da ake zargin bam ne ya tarwatse da safiyar yau Laraba a babbar sakatariyar jihar Bayelsa dake birnin Yenagoa.
Fashewar, wadda ta faru da misalin karfe 6:00 na safe, ta janyo tsoro da fargaba tare da dakatar da dukkan ayyukan gwamnati na dan lokaci.

Source: Getty Images
Bam ya tashi a sakatariyar Bayelsa
Kwamishinan yan sandan jihar, CP Iyamah, ya tabbatar da cewa babu mutumin da ya rasa ransa kuma ba a samu asarar dukiya mai yawa ba, in ji rahoton Vanguard.
CP Iyamah ya ce:
"Rundunar yan sandan Jihar Bayelsa tana sanar da jama'a cewa an samu fashewar wani abu da ake zargin nakiya ce a saiyar yau.
"A halin yanzu da nake magana daku, jami'anmu na musamman sun riga sun shawo kan lamarin kuma komai ya koma daidai yanzu a sakatariyar."
Kwamishinan ya ce jami'an sashen kwance abubuwan masu fashewa (EOD) sun gano wani bam din wanda bai fashe ba a wurin, sannan suka yi maza suka lalata shi.
An kama mutum 1 kan tashin bam
Rundunar yan sandan ta samu nasarar damke wani Pentecost Elijah, mai shekaru 60 daga karamar hukumar Southern Ijaw dake cikin jihar.
"An kama Pentecost Elijah ne a daidai wurin da lamarin ya faru, kuma yanzu haka yana hannun jami'an binciken manyan laifuffuka," in ji CP Iyamah.
CP Iyamah ya tabbatar da cewa za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kotu da zaran an kammala gudanar da cikakken bincike, in ji rahoton Punch.
Gwamnatin jihar ta ba da umarnin rufe sakatariyar na tsawon sa'o'i domin ba jami'an tsaro damar bincikar dukkanin sassan wurin baki daya.

Source: Original
Matakan da gwamnati ta dauka
Sakataren gwamnatin jihar, Dr Wisdom Ebiye Sawyer, ya dakatar da ma'aikata daga shiga wurin aiki na dan lokaci domin tabbatar da tsaron rayukansu.
DR. Wisdom Sawyer ya ce:
"Mun bada wannan umarni ne domin kiyaye rayukan ma'aikatanmu sama da 6,000 da ke gudanar da ayyukansu a wannan babban rukunin sakatariyar."
Jami'an hana fashewar bama-bamai sun toshe dukkan hanyoyin da ke kaiwa zuwa sakatariyar da kuma gidan gwamnatin jihar yayin da ake gudanar da bincike.
Bam ya tarwatse da mutane a Adamawa
A wani labari, mun ruwaito cewa, an tabbatar da tashin wani abu da ake kyautata zaton cewa bam ne a ƙaramar hukumar Hong da ke jihar Adamawa.
Shugaban Hong, Usman Inuwa, ya ce aƙalla mutane shida ne suka samu rauni sakamakon fashewar wani bam din da Boko Haram ta dasa
Wannan harin na zuwa ne mako guda bayan da ’yan ta’addan suka kai wani mugun hari a ƙauyen Mubang, inda suka hallaka mutane 14 a farkon Janairu, 2026.
Asali: Legit.ng

