Shiri Ya Baci: 'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda da Fararen Hula a Benue

Shiri Ya Baci: 'Yan Bindiga Sun Kashe 'Yan Sanda da Fararen Hula a Benue

  • 'Yan bindiga dauke da makamai sun yi yunkurin kashe mutanen da ba su san hawa ba, ba su san sauka ba a jihar Benue
  • Tsagerun 'yan bindigan sun kai farmaki a wata kasuwa da ke kauyen Tse-Kaseve a karamar hukumar Katsina-Ala
  • Jami'an tsaro sun yi artabu da su tare da fatattakarsu, an kashe 'yan sanda tare da wasu fararen hula hudu yayin harin

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Benue - 'Yan bindiga sun kashe jami'an 'yan sanda da wasu fararen hula yayin wani hari a jihar Benue.

'Yan bindigan sun kashe ’yan sanda biyu da fararen hula hudu yayin wani harin da suka kai a kauyen Tse-Kaseve da ke gundumar Anyagba, a karamar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a Benue
Shugaban 'yan sandan Najeriya, Kayode Egbetokun Hoto: @PoliceNG
Source: Facebook

Masani kan harkokin tsaro a yankin Tafkin Chadi da Arewacin Najeriya, Zagazola Makama, ya bayyana hakan a shafinsa na X.

Kara karanta wannan

Hankula sun tashi bayan 'yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro a Katsina, an yi kisa

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda

Majiyoyi sun bayyana cewa lamarin ya faru ne ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairun 2026 da misalin ƙarfe 4:00 na yamma.

An bayyana cewa ’yan bindigan dauke da makamai sun mamaye yankin ne a kan babura kusan 100.

Majiyoyin sun ce maharan sun yi kokarin mamaye kasuwar kauyen domin kashe mazauna mutane, inda dakarun hadin gwiwa na jami’an tsaro suka fafata da su.

“Jami’an rundunar ’yan sanda ta tafi-da-gidanka (PMF) da ke aiki na musamman a garin, tare da haɗin gwiwar dakarun tsaro na sa-kai na jihar Benuwai, sun yi artabu da maharan tare da fatattakar su."

- Wata majiya

An kashe fararen hula

Sai dai yayin artabun, ’yan bindigan sun yi wa jami’ai biyu kwanton bauna, Sufeta Adams Saidu da Sufeta Edem Endimon, inda suka harbe su har lahira sannan suka tafi da bindigogin aikinsu.

Rundunar ta ce an kuma kashe fararen hula hudu a harin, yayin da wani mutum daya ya samu raunuka kuma aka garzaya da shi babban asibitin Katsina-Ala domin yi masa magani.

Kara karanta wannan

Ana wata sai ga wata: 'Yan bindiga sun sake kai hari coci, sun sace masu ibada

Bayan faruwar lamarin, an tura dakarun sojojin Najeriya tare da karin wasu tawagogin jami’an tsaro na musamman da ’yan banga zuwa yankin.

“Ana ci gaba da bincike a cikin daji domin kamo wadanda ake zargi da kai harin tare da kama su."

- Wata majiya

'Yan bindiga sun kashe 'yan sanda a Benue
Taswirar jihar Benue, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Karanta wasu labaran kan 'yan bindiga

'Yan bindiga sun farmaki jami'an tsaro

A wani labarin kuma, kun ji cewa 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin kwanton bauna kan jami'an tsaro a jihar Katsina.

'Yan bindigan sun hallaka jami'in tsaro na rundunar C-Watch tare da jikkata wani bayan sun kai harin musu kwanton ɓauna a ƙaramar hukumar Musawa.

Tsagerun sun hallaka wani jami'i daya na rundunar tsaron (C-Watch), tare da jikkkata wasu jami'ai bayan harbinsu da bindiga.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng