Abin da Hukumar INEC Ta Fadawa Majalisar Dattawa kan Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet

Abin da Hukumar INEC Ta Fadawa Majalisar Dattawa kan Tura Sakamakon Zabe Ta Intanet

  • Sanata Seriake Dickson ya bayyana cewa Majalisar dattawa ta samu tabbaci cewa INEC na da karfin da za ta tura sakamako ta intanet kai tsaye
  • Ya nuna takaicinsa kan yadda Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da tanadin da zai wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura tun a matakin farko
  • Tsohon gwamnan, wanda ke wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar dattawa, ya ce yana daga cikin wadanda suka sa aka sake zama kan dokar

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja, Nigeria - Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma, Sanata Seriake Dickson, ya yi bayanin abin da Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta fadawa Majalisar dattawa kan dokar tura sakamako ta intanet.

Sanata Dickson ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa Hukumar INEC na da cikakken ƙarfin tura sakamakon zaɓe kai tsaye daga rumfunan zaɓe a fadin ƙasar nan.

Kara karanta wannan

'Yan majalisa sun yi hayaniya, an buga muhawara a kan aika sakamakon zabe

Sanata Dickson.
Sanata mai wakiltar Bayelsa ta Yamma a Majalisar dattawa, Seriake Dickson Hoto: Seriake Dickson
Source: Facebook

Tsohon Gwamnan na jihar Bayelsa ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata, 10 ga watan Fabrairun 2026.

Ya nuna takaicinsa kan yadda Majalisar Dattawa ta ƙi amincewa da tanadin da zai wajabta tura sakamakon zaɓe ta na’ura kai tsaye tun a matakin farko.

Sanata Dickson ya yabi Majalisar Wakilai

Sanatan ya ce ya yi matuƙar baƙin ciki lokacin da ya ji labarin yayin da yake zaman makoki a Bayelsa sakamakon rasuwar ɗan’uwansa, mataimakin gwamna.

Dickson ya kuma yaba wa Majalisar Wakilai ta Tarayya bisa amincewa da kudirin kamar yadda aka tsara tun farko.

Ya ce:

“Mun shafe sama da shekaru biyu muna aiki kan wannan batu. Majalisar Wakilai ta amince da abin da muka tsara. Ina gode wa Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, da shugabannin kwamitin da sauran ‘yan majalisar bisa yin abin da ya dace."

Abin da INEC ta fada wa Majalisar dattawa

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Majalisar Dattawa ta sauya matsaya kan tura sakamako ta yanar gizo

Sanatan ya jaddada cewa hukumar INEC ta tabbatar wa Majalisar dattawa cewa tana da ƙarfin tura sakamako kai tsaye ta na'ura a duk faɗin ƙasar nan.

'Dan majalisar ya bayyana cewa an kirkiri shafin tattara sakamako (IReV) ne domin bai wa jama’a damar ganin sakamakon zaɓe kai tsaye daga rumfunan zaɓe.

Ya ce IReV ba ya tattara sakamako na ƙarshe ko ayyana wanda ya ci zaɓe, amma yana ƙara gaskiya da bayyana sakamakon yadda aka kada ƙuri’a.

Dalilin INEC na kirkiro shafin IReV

“IREV yana nuna sakamakon zaɓe kai tsaye daga rumfunan zaɓe. Ba shi ke ayyana wanda ya yi nasara ba, amma yana taimaka wa wajen tabbatar da gaskiya,” in ji shi.

Dickson, wanda ya halarci zaman majalisa na farko bayan zaman makokinsa, ya ce ya tattauna da shugabannin majalisar kan lamarin, wanda daga bisani aka gabatar da kudirin sake duba matsayar.

Sai dai ya ce sabon tanadin ya ƙunshi sharadin amincewa da sakamakon takarda a wuraren da matsalar sadarwa ta hana tura sakamakon zaben.

Sanata Dickson.
Sanata mai wakiltar Yammacin jihar Beyelsa, Sanata Seriake Dickson Hoto: Seriake Dickson
Source: Facebook

An yi hayaniya a zaman Majalisar dattawa

A wani rahoton, kun ji cewa sanatoci sun barke da hayaniya a yayin muhawara kan dokar tura sakamakon zabe ta intanet kai tsaye daga rumfunan zabe.

Kara karanta wannan

Dokar zabe: Rikici ya barke a zaman Majalisar Dattawa kan wasu kalaman Akpabio

Rahoto ya nuna cewa sanatoci sun barke da hayaniya da ka-ce-na-ce a tsakaninsu a zaman gaggawa da suka gudanar ranar Talata, 10 ga watan Fabrairu, 2026.

Sanatoci sun nuna fushinsu ne lokacin da Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta shawarwarin da aka gabatar domin gyara ga Sashe na 60(3).

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262