Jirgi Ya Samu Matsala a Sama bayan Dauko 'Yan Najeriya kusan 100
- Jirgin Arik ya samu matsalar inji yayin da ya dauko fasinjoji da ma'aikata kusan 100 daga Legas zuwa garin Fatakwal
- Rahotanni sun nuna cewa jirgin ya yi saukar gaggawa a Benin bayan gano ya samu matsala a sararin samaniya
- Har zuwa lokacin hada wannan rahoton ba a samu sanarwa daga hukumar da ke kula da haduran jiragen sama ba
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Benin - Fasinjojin wani jirgin Arik Air daga suka taso daga Legas zuwa Fatakwal sun shiga fargaba bayan da aka sauya alkiblar jirgin sakamakon matsalar injin da ya samu.
Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya sa matuƙan jirgin suka yi saukar gaggawa a filin jirgin saman birnin Benin da ke jihar Edo.

Source: UGC
Jirgi ya sauka bayan samun matsala
Punch ta wallafa cewa kamfanin jirgin ya tabbatar da cewa jirginsa zai sauka a filin jirgin saman Fatakwal da ke Omagwa kafin samun matsalar.
Har yanzu ana jiran bayani da daga hukumomin Najeriya, musamman wadanda ke lura da haduran jiragen sama da masu kula da filayen jiragen sama.
Bisa ka’idojin tsaro da aka tanada, nan take matuƙan jirgin suka yanke shawarar karkatar da shi zuwa filin jirgin sama mafi kusa a matsayin matakin kariya.
Daga bisani jirgin ya sauka lafiya a filin jirgin saman Benin ba tare da ƙarin matsala ba, Arik Air ya ce dukkan fasinjoji 80 da ma’aikatan jirgin da ke cikinsa sun fita lafiya, kuma ba a samu rahoton jikkata ba.
Kamfanin jirgin saman ya dauki mataki
Kamfanin jirgin saman ya ce ya dauki matakan jigilar fasinjojin zuwa inda suka dosa a Fatakwal domin kammala tafiyarsu.
Shugaban sashen hulda da jama’a na kamfanin, Adebanji Ola, ya nemi afuwar fasinjojin da lamarin ya shafa, yana mai jaddada cewa tsaron fasinjoji ne mafi muhimmanci a gare su.

Kara karanta wannan
Hankali ya tashi: NSIB ya fitar da jawabi da jirgi ya samu matsala a sararin Samaniya
A cewarsa:
“Tsaro da jin dadin fasinjojinmu muka sa a gaba a Arik Air. Muna ba da hakuri ga fasinjojin da tafiyarsu ta samu tsaiko,”
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa ana sa ran injiniyoyi za su gudanar da cikakken binciken fasaha kan jirgin kafin a ba shi izinin komawa aiki.

Source: UGC
Hukumar Binciken Hatsarin Sufurin Jiragen Sama ta Najeriya (NSIB), wadda ke da alhakin binciken hadura da matsalolin jiragen sama ba ta fitar da wata sanarwa kan lamarin ba har yanzu.
Ana sa ran hukumar za ta fitar da sanarwa ta musamman a nan gaba, musamman domin kara kira a rika kula da lafiyar jirage domin kauce jefa rayuwar al'umma a hadari.
An samu jirgin saman da ya bata
A wani labarin, mun kawo muku cewa hukumomin kasar Indiya sun bayyana cewa an samu wani jirgin sama da ya bata tsawon shekaru 13.
Rahotanni sun nuna cewa an ajiye jirgin ne a wani filin jirgin sama kuma aka manta da shi sai bayan shekaru aka gano shi a wajen.
Biyo bayan lamarin, hukumar da ke kula da filayen jiragen sama ta Indiya ta ci taron kamfanin jirgin kudin gadi na tsawon shekarun da ya yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
