Hafsun Sojoji Ya Fadi Abin da ke Jiran Wadanda Suka Shirya Juyin Mulki

Hafsun Sojoji Ya Fadi Abin da ke Jiran Wadanda Suka Shirya Juyin Mulki

  • Hafsun sojin saman Najeriya, Air Mashal Sunday Aneke ya gargadi sojoji kan duk wani yunkurin hambrar da gwamnatin farar hula
  • Air Mashal Sunday Aneke ya ce shirin kifar da Bola Tinubu abin kunya ne da takaici, kuma wadanda aka kama za su fuskanci hukunci
  • Sama da mutum 40 suna tsare kan zargin yunkurin juyin mulki a shekarar 2025, daga cikinsu akwai sojoji da sauran farar hula

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja– Hafsun sojin saman Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke, ya bayyana cewa mutanen da aka kama da yunkurin juyin mulki za su ji a jikinsu.

Sojan ya bayyana cewa duk wani jami’in rundunar sojin kasar da aka samu da laifin kokarin kifar da gwamnatin dimokuradiyya zai fuskanci cikakken hukuncin da doka ta tanada.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kausasa harshe kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya dauki mataki

Hafsun sojan sama ya ce za a hukunta wadanda suka shirya juyin mulki
Hafsun sojan saman Najeriya, Air Marshal Sunday Aneke Hoto: Nigeria Airforce HQ
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa Aneke ya yi wannan bayani ne a ranar Laraba, 11 ga watan Fabrairu, 2026 yayin wani taron a hedikwatar rundunar sojin sama ta Najeriya da ke Abuja.

Hafsun soja ya magantu kan juyin mulki

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa Air Marshal Sunday Aneke ya ce zargin shirin juyin mulki da wasu jami’an soja suka kitsa a kan gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu abin kunya ne.

Da yake jawabi kafin a sanya labule a taron, Air Marshal Aneke ya ce ba za a lamunci duk wani yunkuri na rusa tsarin dimokuradiyya ba.

Hafsun sojin Najeriya ya yi tir da shirin juyin mulki
Shugaban Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Ya ce:

“Ina yin tir da wannan yunkuri na shirya kifar da gwamnati da nufin karya tsarin dimokuradiyya domin kwace iko da gwamnati."

Ya tunatar da kwamandojin tsaro nauyin da ya rataya a wuyansu na tabbatar da cewa sun yi tsayin daka wajen kare martabar Najeriya da hadin kan kasa.

Kara karanta wannan

Malami da fararen hula 4 da aka kama da zargin hannu a yunkurin juyin mulki a Najeriya

Ana shirin hukunta wasu sojoji

Babban hafsan ya jaddada cewa babban aikin rundunar soji shi ne tallafawa hukumomin farar hula tare da kare kundin tsarin mulkin kasa.

Rahotanni sun nuna cewa adadin jami’an soja da fararen hula da aka kama dangane da zargin shirin juyin mulki na watan Oktoban 2025 ya haura 40.

Ana zargin mutanen da shirya kifar da gwamnatin da aka zaba ta hanyar dimokuradiyya, lamarin da ya janyo muhawara a fadin kasar.

Sai dai iyalan wasu daga cikin wadanda ake zargin sun bukaci a yi musu sassauci tare da ba su damar shari’a cikin adalci.

An kama tsohon janar kan zargin juyin mulki

A wani labarin, mun wallafa cewa jami'an tsaro sun kara fadada bincike kan yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, inda aka kama wani tsohon Janar

Rahotanni sun nuna cewa ana zargin tsohon Janar din da alaka ta kusa da wanda ake zargi a matsayin jagoran yunkurin, duk da rashin shaida a hannu da zai alakanta shi da batun.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwa 5 da bincike ya gano kan shirin juyin mulkin da aka yi a Najeriya

Hakan na zuwa ne bayan rundunar tsaro ta tabbatar da yunkurin juyin mulki bayan karyata batun ana shirin kifar da gwamnati a wata sanarwa da ta fitar a shekarar 2025 da ta wuce.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng