Ukraine: Rasha Ta Yi Bayani kan Daukar 'Yan Najeriya Su Shiga cikin Sojojinta

Ukraine: Rasha Ta Yi Bayani kan Daukar 'Yan Najeriya Su Shiga cikin Sojojinta

  • Gwamnatin Rasha ta fito ta yi magana kan rade-radin da ake yi cewa tana daukar 'yan Najeriya su je taya ta yaki a matsayin sojoji
  • Jakadan kasar Rasha a Najeriya, Andrey Podyolyshev ne ya bayyana haka bayan an yada wasu rahotanni a baya kan lamarin
  • Batun ya kara daukar hankali ne bayan bullar wani labari da ke nuna wani matashi daga Kano ya rasu yana taya Rasha yaki

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Jakadan kasar Rasha a Najeriya, Andrey Podyolyshev, ya musanta cewa akwai wani shiri na gwamnati da ke daukar ‘yan Najeriya domin su je su yi yaki a Ukraine.

Da yake magana a Abuja ranar Talata, Podyolyshev ya mayar da martani kan rahotannin da ke cewa an dauki wasu ‘yan Najeriya da sunan ayyukan tsaro a Rasha, amma daga bisani aka tura su yaki bayan horo na makonni.

Kara karanta wannan

Wata sabuwa: Bayan turo sojoji, an hango abin da Amurka za ta yi a zaben Najeriya na 2027

Shugaban kasar Rasha a ofis
Shugaban Rasha, Vladimir Putin zaune a ofis. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Rasha na daukar sojoji daga Najeriya?

Rahoton Punch ya nuna cewa ya yi magana yana mai jaddada cewa idan akwai irin wannan aiki, to ba ya da alaka da gwamnatin Rasha.

Ya ce:

“Babu wani shiri da gwamnati ke yi na daukar ‘yan Najeriya domin su yi yaki a Ukraine.
"Idan akwai wasu kungiyoyi ko mutane da ke kokarin daukar ‘yan Najeriya ta hanyoyin da ba su dace ba, wannan ba shi da alaka da gwamnatin Rasha,”

Jakadan ya kara da cewa Moscow a shirye take ta binciki duk wata sahihiyar shaida da za a gabatar mata a kan cewa suna daukar matasan Najeriya.

“Idan wani yana da irin wannan bayani, a shirye muke mu mika wa hukumomin tsaro na Rasha domin su binciki lamarin,”
Dan Najeriya da aka ce ya rasu a Rasha
'Dan Najeriya, Anas Adam da aka ce ya rasu cikin sojojin Rasha. Hoto: Jafar Jafar|Anas Adam
Source: Facebook

Martanin kasar Rasha ga 'yan jarida

Podyolyshev ya kuma nuna shakku kan rahotannin kafafen yada labarai na kasashen Yamma, ciki har da wani bincike na CNN, wanda ya yi ikirarin cewa an yaudari wasu ‘yan Najeriya aka sa su shiga yaki.

Kara karanta wannan

Ana zargin yaran Turji sun yi ajalin liman da basarake, jama'a sun tarwatse

“Bayanan da ku ke samu daga kafofin yada labarai na Yamma ne. Babban aikinsu shi ne su bata sunan Rasha. Idan ku na son sanin hakikanin abin da ke faruwa, ku tura ‘yan jarida zuwa Rasha domin su fahimci ainihin halin da ake ciki,”

- In ji shi

Duk da amincewa cewa akwai wasu ‘yan Najeriya da ka iya kasancewa a yankin da ake rikicin, ya ce babu hannun gwamnati wajen kai su wurare masu hadari.

Daily Trust ta rahoto ya ce:

“Idan akwai wasu hukumomi, har ma da na Rasha, da ke karya dokokin Rasha, a shirye muke mu isar da wannan bayani ga hukumomin tsaro domin daukar mataki,”

Game da hadin gwiwar tsaro da harkokin soja tsakanin kasashen biyu, Podyolyshev ya ce Rasha da Najeriya na tattaunawa kan kara dankon zumunci a fannin tsaro, ciki har da samar da makamai da horas da jami’an soja.

Rasha ta harba makamai Ukraine

A wani labarin, kun ji cewa kasar Rasha na cigaba da harba manyan makamai zuwa yankunan Ukraine yayin da yakin da suke yi, ya ki karewa.

Rahotanni sun nuna cewa dakarun Rasha sun harba wasu manyan makamai daga cikinsu akwai wani makami mai karfin nukiliya.

An bayyana cewa tun a kwanakin baya gwamnatin Rasha ta gwada makamin amma ba ta fara aiki da shi ba kai tsaye sai a wannan karon.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng