'Yan Majalisa Sun Riƙewa Minista Wuta a kan 'Bacewar' Kayan Gwamnatin Tarayya
- 'Yan majalisar dokoki sun matsa wa karamin Ministan noma, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi a kan jinkirin rabon taraktoci 2,000
- Sun bayyana cewa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta sayi taraktocin domin amfanin manoman kasar nan amma an ji shiru
- Tun bayan da aka sayi kayan a shekarar 2025, har yanzu ba a samu labarin an fara raba su ga manoman da suke bukata ba A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Kwamitocin hadin gwiwa na Majalisar Dattawa da ta Wakilai kan harkar noman amfanin gona sun gayyaci karamin Ministan aikin noma da wadatar abinci, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi.
Sanatocin da 'yan majalisar wakilai sun tistiye shi domin ya yi bayani kan inda taraktoci 2,000 da gwamnatin tarayya ta kaddamar.

Source: Facebook
Daily Trust ta wallafa cewa wannan tambaya ta taso ne yayin da ministan ya je majalisa domin kare kasafin kudin ma’aikatarsa na shekarar 2026.
'Yan majalisa sun sako minista a gaba
Trust radio ta wallafa cewa a ranar 23 ga Yunin 2025 ne Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya kaddamar da taraktocin tare da wasu kayayyakin noma a Sheda, a Abuja.
Shugaban Najeriya ya jaddada kudurin gwamnatinsa na bunkasa noma da tabbatar da wadatar abinci a kasa.

Source: Facebook
Sai dai kusan watanni takwas bayan kaddamar da shirin, har yanzu ba a ga an rarraba taraktocin ga manoma ba. Dan majalisar wakilai daga jihar Ribas, Awaji Inombek, ya nuna damuwa kan jinkirin, yana mai cewa ya dace a fayyace inda taraktocin suke.
Martanin Minista ga kwamitin Majalisar tarayya
A bayaninsa, Sanata Aliyu Sabi Abdullahi ya ce an yi jinkirin ne da gangan domin kada a maimaita kura-kuran da aka yi a baya. Ya ce:
“Tambayar abin da ke faruwa da taraktocin tana da muhimmanci kwarai. Muna kokari sosai wajen shimfida tsari da zai hana abin da ya faru a baya.”
Ministan ya tuna cewa a baya an raba taraktoci ga wadanda ba manoma ba, lamarin da ya sa manoman gaske ke samun matsala wajen samun kayan aiki.
Ya bayyana cewa an sayo taraktocin masu karfin doki 75 da 85, tare da injinan girbi, kayayyakin noma sama da 9,000 da sauransu.
A cewarsa, an shirya kafa cibiyoyin ba da sabis na injinan noma a shiyyoyi shida na kasar nan domin amfanin manoma.
'Dan majalisa ya tallafawa dalibai 2000
A baya, mun wallafa cewa dan majalisar wakilai mai wakiltar mazabar Gada-Goronyo ta tarayya a jihar Sakkwato, Hon. Bashir Usman Gorau, ya tallafa wa 'daliban yankinsa.
A ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairu, 2026, Gorau ya raba Naira miliyan 101.4 a matsayin tallafin karatu ga ɗalibai sama da 2,000 da ke karatu a manyan makarantun kasar nan.
A bayanin da ya gabatar, Hon. Gorau ya kara da bayyana cewa wannan na daga cikin alkawurran da ya dauka na tallafa wa matasa da bunkasa ilimi a mazabarsa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

