Shekarau: Yayan Tsohon Gwamnan Kano Ya Riga Mu Gidan Gaskiya bayan Jinya
- Allah ya karɓi ran Malam Dahiru Shekarau, yayan tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau, a daren Talata 10 ga Fabrairu, 2026
- An shirya gudanar da sallar jana’izarsa a safiyar Laraba da misalin ƙarfe da safe a Masallacin Juma’a na Giginyu a karamar hukumar Nassarawa
- A lokacin da yake raye, marigayin ya taɓa rike mukamin babban sakatare a Hukumar Makarantun Kimiyya da Fasaha ta jihar Kano
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wasu rahotanni da muke samu sun tabbatar da cewa Allah ya karbi ran yayan tsohon gwamnan Kano, Malam Ibrahim Shekarau.
Majiyoyi sun bayyana cewa marigayin da ake kira Malam Dahiru Shekarau ya rasu a daren ranar Talata 10 ga watan Faburairun 2026.

Source: Facebook
Rahoton Premier Radio ya tabbatar da labarin rasuwar marigayin inda ya bayyana cewa tuni aka shirya sallar jana'izar yayan tsohon gwamnan.
Yaushe za a yi jana'izar yayan Shekarau?
An tabbatar da cewa za a yi jana'izar sa a safiyar yau Laraba 11 ga watan Faburairun 2026 da muke ciki da misalin karfe 10:00 na safe a masallacin Juma'a na Giginyu a karamar hukumar Nassarawa da ke jihar.
Marigayin ta yaba rike mukamin babban sakatare na hukumar makarantun kimiyya da fasaha a jihar Kano, cewar rahoton Leadership Hausa.
A cikin wata sanarwa da kakakin tsohon gwamnan, Sule Yau Sule ya fitar, ya tabbatar da rasuwar marigayin wanda ya ce ya bar duniya bayan fama da jinya.
Wasu rahotanni sun tabbatar da cewa marigayin shi ne babban yayan tsohon gwamnan Kano kuma mafi kusa da shi cikin danginsu gaba daya.
Mutane da dama sun bayyana marigayin a matsayin mutumin kirki wanda ya ba da gudunmawa ga al'umma da jihar Kano baki daya.

Source: Facebook
Tsohon Akanta-janar na tarayya ya yi ta'aziyya
Tsohon Akanta-janar a Najeriya, Alhaji Ahmed Idris ya nuna jimami game da rashin dattijon inda ya ce tabbas an yi rashin da maye gurbinsa zai yi wahala.
Hakan na cikin wani rubutu da Musa Sulaiman Autan Sardaunan Kano ya wallafa a Facebook a yau Laraba 11 ga watan Faburairun 2026.
Ya ce a wannan lokaci na jimami, yana tuna sadaukarwar da marigayin ya yi ga al'umma wurin ba su gudunmawar da ta dace.
Ya ce:
"Ni, Alhaji Ahmed Idris (Ajiyan Hausa), tsohon Akanta Janar na Tarayya, ina miƙa ta’aziyyata da ta zuciya ga Mai Girma Sanata Ibrahim Shekarau, tsohon Gwamnan Jihar Kano, da daukacin iyalansa bisa rasuwar ɗan’uwansa babba, Malam Dahiru Shekarau, wanda ya yi ritaya a matsayin Babban Sakatare na dindindin."
Kwankwaso ya tabbatar da rasuwar shugaban Kwankwasiyya
Mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun tabbatar da rasuwar wani daga cikin shugabannin tafiyar Kwankwasiyya a jihar Katsina wanda ya ba da gudumawa sosai.
Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya nuna takaici bayan samun labarin rasuwar marigayin inda ya yaba da jajircewarsa kan siyasa.
Mutane sun yaba da jajircewarsa, sadaukarwarsa da rawar da ya taka wajen bunƙasa tafiyar Kwankwasiyya da walwalar al’umma.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

