Dangote Ya Fitar da Sabon Farashin Mai bayan Rage Kudin Litar Fetur
- Matatar Dangote ta rage farashin man fetur daga N799 zuwa N774 kan kowace lita kuma an gano matakin ya fara aiki nan take a fadin Najeriya
- Hakan na zuwa ne bayan Aliko Dangote ya sanar da kara kudin mai a lokacin da aka kammala bukukuwan karshen shekarar 2025 aka shiga 2026
- Masana harkar mai sun ce matakin na nuna sabon tsari a kasuwar man fetur yayin da Dangote ya fara maganar zuba jari a kasar Burundi
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Legas – Matatar Dangote ta sanar da rage farashin man fetur da N25 kan kowace lita, inda ta sauko da farashin daga N799 zuwa N774 kan kowace lita.
Sanarwar ta fito ne a ranar Talata, 10, Fabrairu, 2026, inda aka aika wa ‘yan kasuwa da bayanin sauyin farashin tare da jaddada cewa sabon farashin zai fara aiki ba tare da bata lokaci ba.

Source: Facebook
A sakon da matatar ta fitar a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa rage farashin ya nuna yadda ta himmantu wajen inganta harkokin mai a Najeriya.
Farashin man fetur a matatar Dangote
A cikin wata sanarwa da matatar Dangote ta fitar, ta ce an rage farashin man fetur daga N799 zuwa N774 kan kowace lita ga 'yan Najeriya.
Jaridar Punch ta rahoto cewa sanarwar ta bukaci ‘yan kasuwa su fara aiki da sabon farashin da ya fara aiki nan take ba tare da bata lokaci ba.
Masana harkar mai sun bayyana matakin a matsayin sake fasalin dabarun farashi, musamman a shekarar 2026 da ake fuskantar sauye-sauye a kasuwar mai ta cikin gida da waje.
Dakatar da tallafin dakon mai
Baya ga rage farashin, matatar Dangote ta sanar da kawo karshen tsarin biyan alawus na lodi da take bai wa ‘yan kasuwa.
Matatar ta sanar da 'yan kasuwar cewa dakatar da ba su tallafin zai tsaya da misalin karfe 12:00 na dare a ranar 10, Fabrairu, 2026.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Bayan turo sojoji, an hango abin da Amurka za ta yi a zaben Najeriya na 2027
Masana sun ce rage farashi da dakatar da tallafin na nuna cewa matatar Dangote na komawa kan tsari mai dorewa a harkar mai.

Source: Getty Images
An ce rage N25 da Dangote ya yi ya nuna karuwar gasa daga sauran masu samar da mai ciki har da masu shigo da kaya daga waje da kuma sauran kananan matatu.
Kasuwancin Dangote ya ratsa kasar Burundi
A halin yanzu, Aliko Dangote na nazari kan yiwuwar zuba jari a kasar Burundi, matakin da zai kara fadada tasirinsa a nahiyar Afrika da duniya.
Rahotanni sun nuna cewa Dangote ya ziyarci kasar Burundi tare da rakiyar tsohon shugaban kasar Najeriya, Olusegun Obasanjo.
Gargadi kan tashin farashin mai
A wani labarin, kun ji cewa 'yan kasuwar man fetur sun yi gargadi da cewa farashin litar mai za ta iya tashi har zuwan N1000.
'Yan kasuwar sun yi gargadi ga gwamnatin Najeriya ne bayan matatar Dangote ta kara kudin litar man fetur da aka shiga 2026.
Sun bayyana cewa karin kudin litar mai a halin yanzu zai jefa 'yan Najeriya da dama cikin karin wahalhalu da tsananin rayuwa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
