Tinubu Ya Yi Sababbin Nade Nade, Mutane 9 Sun Samu Manyan Mukaman Gwamnati

Tinubu Ya Yi Sababbin Nade Nade, Mutane 9 Sun Samu Manyan Mukaman Gwamnati

  • Shugaba Bola Tinubu ya nada Adesayo Michael a matsayin sabon shugaban hukumar NEMSA domin kula da ayyukan lantarki a Najeriya
  • An nada Magaji Aliyu a matsayin shugaban SHESTCO domin jagorantar ayyukan bincike da bunkasa fasahar nukiliya a kasar nan
  • Tinubu ya kuma yi wasu nade nade bakwai yayin da ya aika sunaye ga majalisar dattawa don tantancewa da amincewa da nadin

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya naɗa Adesayo Michael a matsayin babban manaja kuma babban jami’in gudanarwa na hukumar kula da ayyukan lantarki ta Nijeriya (NEMSA).

Hukumar NEMSA tana da alhakin tabbatar da ƙa’idojin fasaha, dokoki, da kuma gudanar da bincike da gwajin na’urorin lantarki da mita a cikin masana’antar samar da wutar lantarki ta Nijeriya (NESI).

Kara karanta wannan

EFCC ta kama mai karyar nemo aiki bayan cinikin kujerar shugaban NNPCL a N600m

Shugaba Bola Tinubu ya nada sababbi shugabanni da kwamishinoni a hukumomi 3
Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya na rattaba hannu kan wata takarda a Abuja. Hoto: @officialABAT
Source: Twitter

Tinubu ya nada sabon shugaban NEMSA

Mai magana da yawun shugaban ƙasa, Bayo Onanuga, ne ya sanar da wannan naɗin a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Talata a shafinsa na X.

"Shugaba Tinubu ya nada Injiniya Adesayo Olusegun Michael a matsayin babban manaja kuma babban jami'in gudanarwa na hukumar kula da ayyukan lantarki ta Nijeriya (NEMSA)."

- Bayo Onanuga

Sanarwar Bayo Onanuga ta yi nuni da cewa Adesayo Michael ya maye gurbin Aliyu Tahir, wanda shi ne shugaban hukumar kafin wannan lokaci.

Sauran naɗe-naɗe a hukumar NEMSA

Baya ga shugaban hukumar, Tinubu ya naɗa wasu jami’ai da mambobin hukumar kamar haka:

  • Aliyu Abdulazeez: Babban daraktan fasaha (EDT).
  • Ikechi Nwosu: Shugaban hukumar na shiyyar Kudu maso Gabas.
  • Zubair Idris: Mamba a hukumar.
  • Igba Elizabeth: Mamba mai wakiltar shiyyar Arewa ta Tsakiya.
  • Sani Shehu: Mamba mai wakiltar shiyyar Arewa maso Gabas.
  • Adeyemi Adetunji: Mamba mai wakiltar shiyyar Kudu maso Yamma.
  • Emmanuel Nkpe: Mamba mai wakiltar shiyyar Kudu maso Kudu.
  • Charles Asogwa: Wakilin shiyyar Kudu maso Gabas.

Kara karanta wannan

Gwamna ya hango hadari, ya rufe kasuwanni da tashoshin mota a jiharsa

Sababbin naɗe-naɗe a SHESTCO Da RMAFC

Shugaban kasa ka yi muhimman nade nade a hukumomi 3
Mai magana da yawun shugaban kasa, Bayo Onanuga a wurin taro a Aso Rock Hoto: @aonanuga1956
Source: Twitter

Shugaba Tinubu ya kuma naɗa Magaji Da’u Aliyu a matsayin shugaban hukumar kula da ayyukan kimiyya da fasaha ta Sheda (SHESTCO) dake Abuja.

"Ita dai wannan hukuma tana da alhakin gudanar da bincike da bunƙasa fasaha, gami da kula da cibiyar binciken nukiliya," in ji Bayo Onanuga.

Haka kuma, shugaban ya zaɓi mutane biyu a matsayin kwamishinoni a hukumar rarraba kason kuɗaɗen shiga da kasafin kuɗi (RMAFC):

  • Amina Gamawa: Wakiliyar jihar Bauchi.
  • Abdullahi Muktar: Wakilin jihar Kaduna.

Tuni shugaban ƙasar ya aika da sunayen Amina Gamawa da Abdullahi Muktar zuwa ga majalisar dattawa domin tantancewa da kuma amincewa da naɗin nasu.

Karanta sanarwar Bayo Onanuga a nan kasa:

An dauke wuta a wasu yankunan Arewa

A wani labari, mun ruwaito cewa, Kamfanin TCN ya sanar da daukewar wutar lantarki a birnin Minna da wasu sassan Abuja saboda gyara da za a yi.

Kara karanta wannan

Bayan Abba ya shiga APC, Shugaba Tinubu zai yi aikin titin Naira biliyan 19 a Kano

Wasu yankuna na cikin Minna da kuma Suleja za su shiga duhu na rashin wuta na dan lokaci kafin jami'an TCN su kammala dukkan ayyukan gyaran.

A cikin sanarwar da TCN ya fitar, ya lissafa yankuna 20 da rashin wutar zai shafa da kuma bayani game da lokacin da ake sa ran za a dawo da wutar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com