Sanata Ya Shawarci Musulmi kan yadda Za Su Kalubalanci Malamai
- Tsohon shugaban majalisar dattawa, Ahmed Lawan ya ce al’ummar Musulmi na da babban gudunmawa da za su bayar wajen dakile rashin tsaro
- Ahmed Lawan wanda ya shafe shekaru a majalisar tarayya ya jaddada cewa ba gwamnati ba ce ya kamata ta jagoranci hakan, illa Musulmi da kansu
- 'Dan majalisar na Arewacin jihar Yobe ya yi gargadi cewa barin koyarwar tsattsauran ra’ayi na taimakawa tashin hankali da kashe-kashe a kasa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja – Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya yi magana game da karuwar ta'addanci a Najeriya.
Ahmed Lawan ya ce wajibi ne al’ummar Musulmi su dauki matakin dakile rashin tsaro ta hanyar tinkarar malamai da ke yada koyarwar da ba su da tushe a Musulunci.

Source: Facebook
Ta'addanci: Ahmed Lawan ya shawarci Musulmi
Lawan ya bayyana hakan ne yayin zaman majalisa, inda ya ce alhakin dakatar da koyarwar da ke haddasa tashin hankali ya fi rataya a wuyan Musulmi, ba wai gwamnati ba, cewar TheCable.
A cewarsa, barin wasu mutane suna yada koyarwar da ba ta cikin littattafan Musulunci na taimakawa yawaitar rikici da rashin zaman lafiya a Najeriya.
Lawan, wanda ke wakiltar mazabar Yobe ta Arewa, ya ce:
“Al’ummar Musulmi ma suna da alhaki. Wadanda ke koyar da abin da ba Musulunci ba dole al’umma ta dauki mataki a kansu, domin idan muka bar su, wannan hali zai ci gaba.”
Ya kara da cewa Musulmi sun fi kowa fahimtar addininsu fiye da jami’an gwamnati, saboda haka sun fi dacewa su gano tare da kalubalantar irin wadannan koyarwar.
“Ba ina nufin gwamnati ba, al’ummar Musulmi nake nufi, domin ba kowa a gwamnati ne ke fahimtar abin da ke faruwa ba. Amma mu Musulmi mun sani, don haka ya kamata mu kare mutane daga gurgun tunani.”
- In ji Ahmed Lawan

Source: UGC
Ahmed Lawan ya fadi haramcin kisa a Musulunci
Ahmed Lawan ya kuma jaddada cewa Musulunci ya haramta kashe rayuka ba tare da dalili ba, yana mai cewa kisan kai ga ko Musulmi ko wanda ba Musulmi ba babu wani dalilin da zai halasta shi, cewar Sahara Reporters.
Ya ce:
“A Musulunci, kashe mutum daya ba tare da hakki ba kamar ka kashe duk duniya ne. To ta ya ya za a kashe wani mutum, Musulmi ko ba Musulmi ba? Wannan ba ya halatta.”
Sanatan ya bukaci shugabannin addini da cibiyoyin Musulunci su tabbatar da cewa koyarwa da ake yadawa sun dace da Alkur’ani da koyarwar addini, yana gargadin cewa rashin yin hakan zai bai wa tsattsauran ra’ayi damar cigaba da yaduwa.
'Tinubu zai samu kuri'a a Arewa' - Ahmed Lawan
Kun ji cewa tsohon Shugaban majalisar dattawan Najeriya, Sanata Ahmed Lawan, ya yi tsokaci kan zaben shugaban kasa na shekarar 2027.
Sanata Ahmed Lawan ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu zai samu kuri'u masu tarin yawa a yankin Arewacin Najeriya.
Tsohon shugaban majalisar dattawan ya yi hasashen tagomashin da Tinubu zai samu idan aka zo kada kuri'a a zaben 2027.
Asali: Legit.ng

