Daminar Bana: Kaduna da Wasu Jihohi 12 da Za Su Fi Samun Ruwan Sama a 2026
- Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NiMet) ta yi hasahen yadda damina za ta zo a jihohin Najeriya a shekarar da muke ciki watau 2026
- NiMet ta bayyana jihohin da za samu damina mai tsayi da wadanda kuma ba za a jima ana ruwan sama ba a bana
- Ta gargadi manoma da su duba littafin hasashen 2026 da ta fitar domin sanin abubuwa da dama da suka shafi yanayin damina mai zuwa a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Kula da Yanayi ta Kasa (NiMet) ta yi hasashen cewa za a samu damina mai tsawo fiye da yadda aka saba gani a jihohin Najeriya 13 a shekarar 2026.
Festus Keyamo, Ministan Sufurin Jiragen Sama da Ci gaban Sararin Samaniya, ne ya bayyana hakan yayin gabatar da Hasashen Yanayi na Shekara-shekara (SCP) na 2026 a birnin Abuja ranar Talata.

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Bayan turo sojoji, an hango abin da Amurka za ta yi a zaben Najeriya na 2027

Source: Facebook
Jihohin da za a fi samun ruwan sama a 2026
Vanguard ta ruwaito cewa jihohi 13 da za su fu samun ruwan sama a 2026 sun hada da Legas, Benue, Enugu, Ebonyi, Ogun, Oyo, Nasarawa, Anambra, Kwara, Kebbi, Kaduna, Gombe da Taraba.
Keyamo ya ce NiMet ta bayyana cewa ana ran samun saukar ruwan farko da wuri a damina mai zuwa a jihohin Bayelsa, Rivers, Akwa Ibom, Cross River, Benue, Kogi, Nasarawa, Oyo.
Haka zalika ruwan zai sauka aa sassan Kebbi, Niger, Jigawa, Katsina, Kano, Adamawa da Taraba.
Jihohin da za a dauke ruwa da wuri
A hasashen da ta yi, NiMet ta ce:
"Yayin da ake sa ranar jinkirin damina a jihar Borno, ana sa ran daukewar ruwan sama da wuri fiye da yadda aka saba a sassan jihohin Ogun, Osun, Ondo, Imo, Rivers, Akwa Ibom, Kogi, da Niger.

Kara karanta wannan
Akpabio: El Rufa'i ya zargi Shugaban Majalisa da zama alaƙaƙai wajen gyara dokar zabe
"Sai dai, ana sa ran jinkirin daukewar ruwan sama a jihohin Legas, Ogun, Anambra, Enugu, Cross River, Benue, Nasarawa, da Kaduna."
A gefe guda kuma, hukumar ta bayyana cewa ana sa ran za a samu gajeren lokacin damina fiye da yadda aka saba a sassan jihohin Borno, Yobe, da Niger
"Za a samu yawan ruwan sama na shekara-shekara kamar yadda aka saba a mafi yawan sassan Najeriya idan aka kwatanta da matsakaicin ruwan da ake samu a kowace damina," in ji NiMet.
Jihohin da za a samu fari a bana
Hukumar ta kuma yi gargadin yiwuwar samun tsananin fari da zai dauki fiye da kwanaki 15 a sassan jihohin Oyo da Ogun tsakanin watan Maris zuwa Mayu.
Ta ce:
"Bugu da kari, a tsakanin watannin Yuni, Yuli, da Agusta, ana hasashen ruwa zai dauke na kwanaki 21 a sassan jihohin Bauchi, Borno, Gombe, Jigawa, Katsina, Kano, Kebbi, Kwara, Nasarawa, Niger, Oyo, Plateau, Sokoto, Yobe, da Zamfara."

Source: Getty Images
Za a yi zafi mai tsanani a Najeriya
A cewar hukumar, yanayin zafin rana da na dare ana sa ran zai fi yadda aka saba a mafi yawan sassan kasar a watannin Janairu, Fabrairu, Maris, da Mayu duk a 2026, in ji Guardian.
"Don haka, ana shawartar wadanda ke harkar noma da sauran ayyukan da suka dogara da ruwan sama a Najeriya da su duba lokacin da ake hasashen damina za ta shiga wanda aka wallafa a cikin littafin hasashen yanayi na 2026 ko su tuntubi NiMet," in ji hukumar.
Dubban manona za su daina noma a Najeriya
A wani labarin, kun ji cewa manoman shinkafa 3,500 a Najeriya na shirin barin aikin noma bayan tafka asarar Naira biliyan 93 sakamakon shigo da shinkafar waje.
Wani kwamitin fadar shugaban ƙasa kan manufofin noma (NAPM) ne ya bayyana hakan a wani rahoto da ya fitar kan yawan kayan abincin da ake shigo da su daga waje.
Sakamakon faduwar farashin shinkafa a gida, manoma da dama sun fara sauya sheka zuwa noman amfanin gona da ake futarwa zuwa ketare, waɗanda suka fi riba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
