An Dauke Wutar Lantarki a Wasu Yankuna 20 a Arewacin Najeriya, TCN Ya Yi Bayani

An Dauke Wutar Lantarki a Wasu Yankuna 20 a Arewacin Najeriya, TCN Ya Yi Bayani

  • Kamfanin TCN ya sanar da daukewar wutar lantarki a birnin Minna da wasu sassan Abuja sakamakon aikin gyaran taransifomomi
  • Birnin Minna da kewayen Suleja za su shiga duhu na rashin wuta na dan lokaci kafin jami'an TCN su kammala dukkan ayyukan gyaran
  • A cikin sanarwar da TCN ya fitar, ya lissafa yankuna 20 da rashin wutar zai shafa da kuma bayani game da lokacin da za a dawo da wutar

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja - Kamfanin rarraba wuta na TCN ya bayyana cewa za a samu daukewar wutar lantarki a sassa daban-daban na birnin Minna da ke jihar Niger.

Hakazalika, kamfanin ya kuma sanar da cewa za a samu tsaiko samar da wutar lantrki a wasu yankuna na Suleja sakamakon aikin gyaran taransifomomi.

Kara karanta wannan

EFCC ta kama mai karyar nemo aiki bayan cinikin kujerar shugaban NNPCL a N600m

Kamfanin TCN ya sanar da dauke wutar lantarki a wasu sasan Abuja da Niger
Karamar tashar rarraba wutar lantarki ta Wumba–Lokogoma. Hoto: @TCN_NIGERIA
Source: Twitter

An dauke wuta a sassan Abuja, Neja

A birnin Minna, an fara aikin gyaran taransifoma mai ƙarfin 30MVA, 132/33kV tun da misalin ƙarfe 9:30 na safe, inda ake sa ran kammalawa da ƙarfe 4:00 na yamma, in ji rahoton Punch.

Haka kuma, a Suleja, za a gudanar da aikin gyaran taransifomomi guda biyu (45MVA da 30MVA) a yau Talata, 10 ga Fabrairu, 2026, tsakanin ƙarfe 10 na safe zuwa 12 na rana.

Hukumar ta bayyana cewa wannan gyara ya zama dole domin tabbatar da ingancin kayayyakin rarraba wutar lantarki da kuma ba da damar haɗa tsarin SCADA.

Ya zuwa yanzu, wa'adin da TCN ya dauka na yin wannan gyara ya wuce, sai dai Legit Hausa ba ta iya tantance ko an mayar da wuta a yankunan da abin ya shafa ba.

Yankunan da aka dauke wa wuta

A cikin wata sanarwa da TCN ya fitar a shafinsa na X, kamfanin ya ce AEDC ba zai iya rarraba wuta ga waɗannan yankuna masu zuwa ba:

Kara karanta wannan

Kanin Ado Aliero ya kai hari Katsina, sojoji sun gwabza fada da 'yan bindiga

  • A Minna: Tunga, Shiroro, makarantar sakandaren 'yan sanda, sansanin sojojin sama, Maikunkele, Tudun Fulani, Beji, Chanchaga, Tungan Goro, FGC, Bosso Low-Cost, Okada Road, wani yanki na London Street, Kateregi, da Sabon Daga.
  • A Suleja/Abuja: Abuja Steel, Zuba, Madalla, FCT COE, Anagada, da kuma Tungan.
Kamfanin TCN ya ce za a dawo da wuta a yankunan da abin ya shafa da zarar an gama gyara.
Ma'aikatan kamfanin TCN suna magana da 'yan jarida a kusa da karamar tashar wuta ta Wumba–Lokogoma. Hoto: @TCN_NIGERIA
Source: Twitter

Matakin gwamnati da kokarin dawo da wuta

Kamfanin TCN, ta bakin babban manajansa, bangaren hulda da jama'a, Ndidi Mbah, ta nemi afuwar mazauna yankunan bisa wannan rashin jin daɗi da tsaikon zai haifar.

An ba wa jama'a tabbacin cewa za a maida wutar lantarki nan take da zarar ma'aikatan PC&M da NARI sun kammala aikinsu a tashoshin.

Wannan aikin yana cikin tsarin kamfanin na tabbatar da cewa tsofaffin injuna suna samun kulawa akai-akai domin guje wa lalacewar su baki ɗaya.

Dauke wutar kwana 4 a Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, TCN zai gudanar da aikin gyaran wuta a tashar Ife da Ondo daga Litinin zuwa Alhamis domin inganta rarraba lantarki a yankin.

Yankunan Okitipupa da garin Ondo za su shiga duhu tsakanin karfe 8:00 na safe zuwa karfe 3:00 na yammacin kowace rana.

Wannan aikin gyaran na daya daga cikin kokarin gwamnati na karfafa rumbun adana wutar lantarki na kasa domin samar da tsayayyiyar wuta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com