Majalisar Dattawa Ta Zauna, Ana Son Gwamnati Ta Cire Tallafin Wutar Lantarki

Majalisar Dattawa Ta Zauna, Ana Son Gwamnati Ta Cire Tallafin Wutar Lantarki

  • Kwamitin kasafin kudi na Majalisar Dattawan Najeriya ya bukaci a cire tallafin wutar lantarki gaba daya a kasar nan
  • ‘Yan majalisa sun ce tallafin na jawo wa gwamnati mummunan asara tare da hana aiwatar da manyan ayyuka
  • Majalisar ta kare shirin gwamnatin tarayya na karbar bashi domin cike gibin kasafin kudin 2026 don aikin kasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – 'Yan kwamitin Majalisar Dattawa kan Kasafin Kudi sun yi kira da a soke tallafin wutar lantarki gaba daya.

'Yan kwamitin sun bayyana cewa matakin zai taimaka wajen kara yawan kudaden shiga da rage nauyin da ke kan kasafin kudin gwamnatin tarayya.

Kwamitin majalisar dattawa ya nemi a cire tallafin wutar lantarki
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio da wasu Sanatoci a zauren majalisa Hoto; The Nigerian Senate
Source: Twitter

Jaridar Premium Times ta wallafa cewa ‘yan majalisar sun bayyana hakan ne a ranar Litinin yayin zaman jin ra’ayin jama’a kan kudirin kasafin kudin shekarar 2026 da aka gudanar a Majalisar Kasa.

Kara karanta wannan

Akwai kura: Dan majalisa ya tsallake rijiya da baya bayan fusatattun matasa sun farmake shi

'Yan majalisa sun waiwayi tallafin wutar lantarki

A cewa 'yan majalisa, duk da kokarin da ake yi na gyaran bangaren wutar lantarki, tallafin da ake biya na ci gaba da zama babban kalubale ga tattalin arzikin kasa.

Da yake jawabi a taron, Shugaban kwamitin majalisar kasafin kudi, Sanata Adeola Olamilekan, ya ce ba za a iya cimma cikakken gyara a bangaren wutar lantarki ba muddin ana ci gaba da biyan tallafi.

Kwamitin majalisa ya ce tallafin wutar lantarki ba shi da amfani
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio Hoto: The Nigerian Senate
Source: Facebook

Ya bayyana tallafin a matsayin nauyi mai girman gaske da ke rage damar gwamnati na daukar nauyin muhimman ayyuka.

Sanata Olamilekan, wanda ke wakiltar mazabar Ogun ta Yamma, ya jaddada cewa duk da an rarraba bangaren wutar lantarki tare da bai wa jihohi damar samar da wuta, ana ci gaba da biyan tallafi.

'Yan majalisa na son kudin gwamnati ya karu

Sanata Olamilekan ya bayyana cewa har yanzu kudin tallafi na ci gaba da fita daga aljihun gwamnati ba tare da ana ganin amfanin hakan ba.

Kara karanta wannan

2027: Magoya baya sun matsa, ana son Obi da Kwankwaso su hadu a kayar da Tinubu

Ya ce:

“Dole ne mu kammala rarrabawa da kuma cire tallafi a bangaren wutar lantarki. Yanzu jihohi suna da ikon samar da wuta, amma tallafin da ke bangaren har yanzu babban nauyi ne ga aljihun gwamnati. Dole ne a magance shi gaba daya. Wannan zai ba mu damar samun karin kudin shiga."

Sanatan ya ce kasafin kudin Najeriya ba ya wadatar da bukatun hukumomin gwamnati da dama, yana mai cewa ci gaba da biyan tallafi na kara tsananta gibin kasafi.

'Dan majalisar dokoki ya sha da kyar

A baya, mun wallafa cewa wasu fusatattun matasa a karamar hukumar Gassol, da ke jihar Taraba sun kai hari kan dan majalisar dokokin jihar, Hon. Abdullahi Muwalid.

Rahotanni sun nuna cewa 'dan majalisar ya tsallake rijiya da baya daga wani yunkurin kisan gilla da aka yi masa, bayan ayarin motocinsa sun fada hannun matasan da suka fusata.

Lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 7 ga watan Fabrairu, 2026, inda ake zargin harin ya samo asali ne daga korafe-korafen cewa wakilinsu ya gaza aikin da aka tura shi majalisa na kare muradunsu,

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng