Akwai Kura: Dan Majalisa Ya Tsallake Rijiya da Baya bayan Fusatattun Matasa Sun Farmake Shi

Akwai Kura: Dan Majalisa Ya Tsallake Rijiya da Baya bayan Fusatattun Matasa Sun Farmake Shi

  • Wasu fusatattun matasa sun kai farmaki kan ayarin motocin wani dan majalisar dokokin jihar Taraba kwanan nan
  • 'Dan majalisar mai wakiltar mazabar Gassol 1, Hon. Abdullahi Muwalid, ya tsallake rijiya da baya, bayan da matasan suka farmake shi
  • Majiyoyi sun bayyana cewa ba don jami'an tsaro sun yi saurin kawo daukin gaggawa ba, da lamarin ya munana matuka

​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Taraba - An shiga yanayin firgici a garin Gassol, hedkwatar karamar hukumar Gassol da ke jihar Taraba, yayin da wasu fusatattun matasa suka farmaki dan majalisa.

Fusatattun matasan sun kai harin ne kan ayarin motocin dan majalisar jiha, Hon. Abdullahi Muwalid, inda ya tsallake rijiya da baya daga yunƙurin kashe shi.

An farmaki dan majalisa a Taraba
Dan majalisar dokokin Taraba da fusatattun matasa suka farmaka Hoto: Ibrahim Nawa Tella
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta kawo rahoton cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar, 7 ga watan Fabrairu, 2026, sakamakon zargin rashin kokari da kuma rashin wakilci na gari a majalisar.

Kara karanta wannan

Majalisar dattawa ta zauna, ana son gwamnati ta cire tallafin wutar lantarki

'Dan majalisa ya je daurin aure a Taraba

Hon. Muwalid, wanda ke wakiltar mazabar Gassol I a majalisar dokokin jihar Taraba, ya je garin Gassol ne domin halartar taron bikin daya daga cikin abokan tafiyarsa na siyasa, sa’ilin da ziyarar tasa ta koma rikici.

Fusatattun matasan sun dade suna bin sawun dan majalisar domin kunyata shi ko kuma kawo karshen siyasarsa.

Matasa sun farmaki 'dan majalisa

An bayar da rahoton cewa, jim kadan bayan Hon. Muwalid ya isa Gassol, taron matasa dauke da sanduna da duwatsu suka auka wa ayarin motocinsa, inda suka fasa motocin, lamarin da ya tilasta masa tserewa domin tsira da rayuwarsa.

Shaidun gani da ido sun yi ikirarin cewa, ba don saurin kai daukin gaggawa da sojoji da jami’an ’yan sanda da aka tura yankin suka yi ba, da yanzu dan majalisar ya mutu.

“An ceto shi ne sakamakon daukin da jami’an tsaro suka kai, wadanda suka amsa kiran gaggawa kuma suka raka shi har wajen garin Gassol.”

Kara karanta wannan

Liman da ke hannun 'yan sanda ya fadi yadda matashi ya mutu a masallaci

- Wata majiya

An yi wa motoci barna

Shafin Taraba DailyGraph ya kawo cewa motoci da dama a ayarin nasa sun lalace sosai, inda aka ce guda daya ma ta tashi daga aiki kwata-kwata, ko da yake babu wanda ya ji rauni a lamarin.

A cewar mazauna yankin, matasan sun ci gaba da rera taken “Ba tazarce, Ba tazarce,” ma’ana ba sa goyon bayan Hon. Muwalid ya sake tsayawa takara a karo na biyu.

Sun zargi dan majalisar da yin watsi da mazabarsa da kuma rashin kula da korafe-korafen da aka gabatar masa daga yankin.

Hakazalika, sun yi zargin cewa, tun bayan zabensa sama da shekaru biyu da suka gabata, bai taba gabatar da ko da kudiri daya ba, sannan bai taba yin wani abin kirki ga mutanen mazabarsa ba.

Matasa sun farmaki dan majalisar dokoki a Taraba
Taswirar jihar Taraba, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Me hukumomi suka ce kan lamarin?

Daga karshe, jami’an tsaro sun tarwatsa taron mutanen kuma suka raka dan majalisar zuwa wajen garin.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An samu gawarwakin mawakan yabon addini 4 a wani irin yanayi

Duk kokarin jin ta bakin dan majalisar ko na hannun damarsa a lokacin tattara wannan rahoto ya faskara.

Haka kuma, ba a samu jin ta bakin jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sanda, ASP Victor Mshelizah ba, domin tabbatar da rahoton daga Gassol.

An yi wa gwamna ihun ba ma yi

A wani labarin kuma, kun ji cewa an yi yunkurin kunyata Gwamnan jihar Adamawa, Ahmadu Umaru Fintiri, a wajen wani taron jam'iyyar PDP.

Wasu matasa a gefe sun yi ta ihu da cewa 'ba mu yi' yayin da gwamnan ke jawabi a taron da aka gudanar a kauyen Ganye na jihar Adamawa.

Ihun ya hasala Gwamna Fintiri, inda ya mayar da martani da cewa dama ba can ba a ce su yi ba, kuma babu zai ce su yi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng