Karfin Hali: Matashi Ya Saka Hedikwatar EFCC a Kasuwa zai Sayar Ya Ci La'ada
- Hukumar EFCC ta maida martani ga wani mai amfani da shafin X da ya wallafa hoton babban ofishinta a Abuja a matsayin wani otel da zai sayar
- Sakon da aka wallafa ya ja hankalin jama’a sosai, inda EFCC ta yi martani a karkashin sakon, abin da ya kara nuna irin karfin halin wannan mutum
- Martanin ya jawo karin tsokaci daga masu amfani da kafafen sadarwa, inda wasu suka yi barkwanci, wasu suka yi tambayoyi kan farashinsa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja– Hukumar EFCC ta shiga tattaunawa a kafafen sada zumunta bayan wani mai amfani da shafin X ya wallafa hoton babban ofishinta da ke Abuja, yana bayyana shi a matsayin wani otel da zai sayar.
Sakon ya yadu cikin sauri, inda EFCC da kanta ta shiga tattaunawar wajen amfani da shafinta, ta mayar da martani da kalmar barkwanci wadda ta kara daukar hankalin jama’a a shafin.

Source: Twitter
Lamarin ya faru ne bayan mai amfani da shafin X @osere_x ya wallafa hoton ginin EFCC tare da bayanin cewa otel ne da ke Abuja da zai sayar.
Yadda sakon ya yadu a shafin X
A sakon da matashin ya wallafa yana neman mai sayen babban ofishin hukumar EFCC da ke Abuja, ya rubuta cewa:
“Ga otel na sayarwa a Abuja. Farashinsa N800m. Kudin dillali N120m. Masu niyyar saye da gaske su tuntube ni.”
Wannan mutumi ya nuna tamkar shi dillali ne wanda zai tashi da la'adar N120m idan ciniki ya fada.
Rubutun da ya yi ya jawo martani daga dubban mutane a cikin kankanin lokaci, musamman bayan martanin hukumar EFCC.
Zuwa ranar 9 ga Fabrairun 2026, mutane 800 sun yada shi, fiye da mutum 500 sun yi tsokaci a kansa, mutanen da suka kalle shi kuma sun kai 433,000.

Source: Twitter
The Cable ta wallafa cewa yawan wadannan alkaluma ya nuna yadda sakon ya dauki hankalin jama’a a kafar sadarwa ta X.
Martanin hukumar EFCC ga matashin
Daya daga cikin manyan abubuwan da suka kara tayar da muhawara shi ne martanin da EFCC ta bayar kai tsaye a karkashin sakon.
Hukumar ta rubuta: “Hmmm…. Lallai ka gawurta,”
Wannan martani daga hukumar ya kara jawo hankalin jama’a game da tsaurin idon shi, inda aka samu karin tsokaci da barkwanci daga masu amfani da kafar.
Ra’ayoyin jama’a a kafar X
Wasu masu amfani da shafin X sun kara tsokaci kan lamarin. Ibrahim Tijjani Ibrahim Gamawa ya bayyana mamakinsa yana dariya, yana cewa da mamaki mutum ya yi kokarin sayar da ofishin EFCC.
Wani mai suna Tommyc Coal ya yi barkwanci yana tambayar EFCC nawa za ta biya shi idan ya taimaka wajen gano wanda ya wallafa sakon.
A nasa bangaren, Halliru AIsa kuwa ya tambaya ko akwai ragi a farashin, yana cewa yana da mai saye a halin yanzu.
Jami'an EFCC sun kama dan damfara
A wani labarin, kun ji cewa jami'an hukumar EFCC sun kama wani mutum da ake zargi yana damfarar mutane da sunan zai sama musu aiki.
Rahotanni sun nuna cewa EFCC na zargin mutumin da amfani da wasu takardun bogi da ke nuna yana da alaka da Fadar shugaban kasa.
Bayan bincike da aka fara an gano cewa mutumin ya yi cinikin kujerar shugaban kamfanin man Najeriya na NNPCL a shirin sayar da ita a kan N600m.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


