Majalisa za Ta Sake Zama bayan 'Yan Najeriya Sun Hura Wuta a kan Dokar Zabe
- 'Yan Najeriya na ci gaba da matsa wa Majalisar Tarayya lamba a kan ta amince da aika sakamakon zabe ta na’ura kai tsaye zuwa iREV
- Sanatoci sun shirya komawa zaman gaggawa a zauren majalisa yayin da jama’a ke nuna bacin rai kan gyaran Dokar Zaben kasar
- A dokar zaben da aka gyara, an cire kalmar aika sakamakon zaben kai tsaye, lamarin da ya jawo wasu na zargin cewa magudi aka shirya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Ana ci gaba da matsa wa Majalisar Tarayya lamba da ta amince da wajabcin aika sakamakon zabe ta na’ura a ainihin lokacin zabe.
Ana son a rika tura sakamakon zaben rumfunan kada kuri’a zuwa dandalin iREV na Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC), a cikin tsarin gyaran Dokar Zabe da ake yi a halin yanzu.

Source: Facebook
Jaridar Daily Trust ta wallafa cewa wannan na zuwa ne yayin da sanatoci ke shirin komawa zaman gaggawa a yau, Talata 10 ga watan Fabrairu, 2025.
Ana matsawa Majalisa a kan dokar zabe
Jaridar Punch ta wallafa cewa za a koma zaman ne sakamakon karuwar bukatar jama’a da kungiyoyi su ga an saka aika sakamakon zabe ta na’ura cikin gyaran Dokar Zabe kai tsaye.
Majalisar Dattawa ta dakatar da zamanta na tsawon makonni biyu a ranar Laraba da ta gabata, bayan ta amince da kudirin gyaran Dokar Zabe.
Sanarwar kiran zaman gaggawar na kunshe ne cikin wata takarda mai dauke da kwanan wata 8 ga Fabrairu, 2026 wacce aka rarraba wa sanatoci.
Magatakardar Majalisar Dattawa, Emmanuel Odo, ne ya sanya hannu a takardar domin a ci gaba da zama a kan lamarin.
Majalisa ta yi kiran taron gaggawa
A cewar takardar, Odo ya ce yana yin hakan ne bisa umarnin Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio. Sai dai takardar ba ta fayyace dalilin kiran zaman gaggawar ba.

Source: Facebook
Duk da haka, akwai alamun karara da ke nuna cewa zaman na da nasaba da fushin jama’a kan kudirin gyaran Dokar Zabe da Majalisar ta amince da shi a makon da ta gabata.
Ko da yake an gyara sassa da dama na dokar, hankalin jama’a ya fi karkata ne kan wani sashe da ya jawo cece-kuce.
Wannan sashe da ya jawo magana shi ne kin amincewa da tilas aika sakamakon zabe ta na’ura kai tsaye daga rumfunan kada kuri’a zuwa dandalin iREV na INEC.
A makon jiya, Majalisar Dattawa ta amince da Kudirin Gyaran Dokar Zabe ta 2022 na shekarar 2026, bayan karatu na uku.
Babban abin da ke jawo cece-kuce a kudirin shi ne cire kalmar tura sakamakon kai tsaye daga tanade-tanaden da suka shafi aika sakamakon zabe ta na’ura.
Ana son tsige Shugaban majalisa kan dokar zabe
A wani labarin, kun ji cewa ana ci gaba da ce-ce-ku-ce da kai komo kan gyaran Kundin Dokar Zaben Najeriya da Majalisar Dattawa ta amince da shi a makon da ya wuce.
Babban abin da ya fi daukar hankali kuma ya tayar da kura shi ne batun tura sakamakon zabe ta intanet kai tsaye daga kowace rumfar zabe a fadin Najeriya zuwa dandalin INEC.
Jigo a jam’iyyar ADC, Kenneth Okonkwo, ya fito karara ya soki Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, kan rawar da ya taka wajen amincewa da kudirin.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


