Tinubu Ya Sake Shiga tsakani kan Takaddamar Wike da Fubara, an Ji Abin da Ya Faru

Tinubu Ya Sake Shiga tsakani kan Takaddamar Wike da Fubara, an Ji Abin da Ya Faru

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kara kiran Gwamna Siminalayi Fubara da Nyesom Wike kan rikicin siyasar jihar Rivers
  • Mai girma Bola Tinubu ya kira jagororin ne domin samun maslaha kan rikicin da ya dade yana addabar jihar mai arzikin man fetur
  • Wannan dai ba shi ne karo na farko da Shugaba Tinubu ya shiga tsakani kan takaddamar da ke faruwa tsakanin Wike da Gwamna Fubara

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike.

Shugaba Tinubu ya gana da Ministan harkokin Abuja Wike da tsohon yaronsa Gwamna Fubara ne kan rikicin siyasar da ya addabi jihar Rivers.

Tinubu ya sake shiga tsakani kan rikicin siyasar Rivers
Nyesom Wike, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da Gwamna Siminalayi Fubara Hoto: @GovWike, @DOlusegun, @SimFubaraKSC
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta kawo rahoton cewa shugaban kasar ya yi ganawar ne da su a daren ranar Lahadi, 8 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kausasa harshe kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya dauki mataki

Akwai yiwuwar Wike ya sasanta da Fubara

Wasu majiyoyi sun bayyana cewa Wike da Gwamna Fubara sun bar fadar shugaban kasa a cikin mota ɗaya a daren Lahadi bayan wata ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A cewar jami’an, duk da cewa mutanen biyu sun isa fadar daban-daban, sai dai bayan shiga tsakanin da shugaban kasa ya yi kan rikicin, Fubara ya tafi tare da Wike a mota ɗaya.

Sun bayyana hakan a matsayin alamar sulhu da ke nuna yiyuwar kawo ƙarshen rikicin siyasa da ya daɗe a tsakaninsu.

“Ba tare suka zo ba. Fubara ne ya zo da fari, daga baya Wike ya zo. Amma a ƙarshe, dukkansu sun bar fadar tare a mota ɗaya. Shin wannan ba alamar cewa sun sasanta ba ce?”

- Wani jami'i

Wata majiya daban ta kuma tabbatar da ganawar, inda fa ce:

“Eh, gaskiya ne, ya gana da su a daren jiya. Sun sasanta. Ya yi magana da su duka, amma ba zan iya faɗin abin da ya ce ba.”

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura bataliyar sojoji Kwara bayan kashe Musulmai sama da 100

Shugaba Tinubu ya sa labule da Wike, Fubara

Jaridar The Nation ce ta fara ruwaito labarin ganawar tun da safiyar Litinin, inda ta ce Fubara ya raka Wike har gidansa da ke Guzape, Abuja, bayan sun bar fadar shugaban ƙasa.

Wannan ganawa na iya zama sabon sauyi a rikicin siyasar Rivers, wanda ya gurgunta harkokin mulki a jihar mai arzikin man fetur tsawon kusan shekaru biyu.

Rikicin da ke tsakanin Wike da Gwamna Fubara, ya fara ne jim kaɗan bayan Fubara ya hau karagar mulki a karshen watan Mayun 2023.

Tinubu ya sha shiga tsakani a rikicin Rivers

A watan Disamban 2023, Shugaba Tinubu ya shiga tsakani, inda aka cimma wata yarjejeniya ta wucin gadi da ta haifar da sulhu, wadda a cikinta Fubara ya ba da wasu muƙaman siyasa ga magoya bayan Wike.

Wike na takun saka da Gwamna Fubara
Gwamnan jihar Rivers, Siminalayi Fubara da Ministan Abuja, Nyesom Wike Hoto: @GovWike, @SimFubaraKSC
Source: Twitter

Sai dai daga baya yarjejeniyar ta rushe, rikicin ya sake tashi, lamarin da ya kai ga Shugaba Tinubu ayyana dokar ta-baci a jihar a ranar 18 ga Maris, 2025.

Kara karanta wannan

2027: Gwamna Radda ya yi karatun ta natsu, ya gano amfanin sake zaben Tinubu

Daga bisani shugaban kasa ya sake shiga tsakani, ya kwantar da hankula, wanda hakan ya kai ga kawo karshen dokar ta-baci a watan Satumban 2025.

Sai dai har yanzu, rikici ya ci gaba tsakanin Fubara da majalisar dokokin jihar Rivers ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Martin Amaewhule, inda Majalisar ta kai ga fitar da sanarwar yunkurin fara tsige gwamnan daga muƙaminsa.

Jam'iyyar APC ta magantu kan Wike

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban jam'iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya yi magana kan rikicin siyasar jihar Rivers.

Farfesa Nentawe ya bayyana cewa Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ba matsala ba ne ga APC, domin shi dan jam’iyyar PDP ne.

Shugaban na APC ya kara da cewa ce-ce-ku-ce kan shirin tsige gwamnan Rivers ya shafi ‘yan jam’iyyar APC ne kawai da ke majalisar dokokin jihar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng