EFCC Ta Kama Mai Karyar Nemo Aiki bayan Cinikin Kujerar Shugaban NNPCL a kan N600M
- Hukumar yaki da rashawa ta EFCC ta gurfanar da mutum guda kan zargin damfarar nemo aiki a kamfanin mai na kasa NNPCL
- EFCC ta yi zargin cewa mutumin da ake zargi ya yi amfani takardar bogi daga Fadar Shugaban kasa domin nemo aikin Shugaban NNPCL
- A yayin gurfanar da wanda ake zargi a gaban kotu, hukumar yaki da rashawa ta ce ya karbi sama da Naira miliyan 600 a matsayin ladan samo aiki
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa ta Najeriya (EFCC) ta gurfanar da Gidado Ibrahim a gaban Kotun Babban Birnin Tarayya (FCT) da ke Maitama, Abuja.
Hukumar EFCC ta tusa keyarsa zuwa kotu saboda zargin damfarar kuɗi masu yawa da sunan samar da mukami a Kamfanin Man Fetur na Ƙasa (NNPCL).

Source: Facebook
EFCC ta wallafa a shafinta na X cewa ana zargin Gidado da abokan aikinsa sun karbi N603,400,000, yayin da ake neman wata Halimat Adenike Tejusho.
EFCC na shari'a da 'yan damfara'
A sakon da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa Halimat Adenike Tejusho da ake zargin tana hannu a cikin badakalar ta tsere.
Duk da haka, EFCC ta gurfanar da wanda ke hannunta a kotu a ranar 9 ga Fabrairu, 2026, a gaban Mai Shari’a H. Mu’azu.

Source: Facebook
Hukumar ta gabatar da tuhume-tuhume guda shida, waɗanda suka shafi damfara, karɓar kuɗi ta ƙarya da kuma ƙirƙirar takardun bogi.
Lauyan gwamnati, Y. Tarfa, ya shaida wa kotu cewa an shirya sababbin tuhume-tuhumen ne domin a karanta wa wanda ake tuhuma ya amsa laifi ko ya musanta.
Tuhume-tuhumen EFCC a kotu
A cewar takardar tuhuma, ana zargin Gidado Ibrahim da Halimat Adenike Tejusho sun karɓi kuɗin ne daga Oluseye Yomi-Sholoye tsakanin watan Agusta da Oktoban 2024.

Kara karanta wannan
Ta fashe: An cafke malaman Musulunci 2 kan zargin jibgar almajiransu har da makami
Ana zargin sun karbi kudin da sunan za su taimaka mata ta samu naɗin mukamin shugaba a kamfanin mai na kasa, NNPCL.
EFCC ta ce wannan iƙirari ƙarya ce tsantsa, kuma wanda ake tuhuma ya san hakan tun farko amma ya yi biris.
A wani ɓangare na shari’ar, an kuma zargi Gidado da amfani da wata takarda ta bogi mai taken 'Presidential Villa State House, Office of the National Security Adviser.'
Ana zargin ya gabatar da takardar a matsayin sahihiya, alhali ya san ko ya kamata ya sani cewa ta bogi ce.
EFCC ta ce wannan aiki ya saɓa wa sashe na 366 na Dokar Penal Code, tare da hukunci a sashe na 364.
Lokacin da aka karanto masa tuhume-tuhumen guda shida, Gidado Ibrahim ya musanta laifuffukan da ake zarginsa da aikatawa.
Mai Shari’a Mu’azu ya yanke hukuncin ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 17 ga Fabrairu, 2026, domin sauraron bukatar beli, tare da umarnin a kai Gidado Ibrahim gidan gyaran hali na Kuje.
EFCC ta kama jaruma kan wulakanta Naira
A wani labarin, mun wallafa cewa hukumar EFCC reshen jihar Kano, ta cafke fitacciyar jarumar Kannywood, Samha M. Inuwa, bisa zargin cin zarafi da wulaƙanta Naira.
An kama jarumar ne a ranar Talata, 3 ga watan Fabrairu, 2026, bayan wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, wanda ake zargin ya nuna ta face hanci da Naira.
Hukumar ta ce bidiyon ya ja hankalinta ne bayan ganin yadda ake zargin jarumar ta yi amfani da takardun Naira wajen aikata abin da ke nuna raini da rashin girmamawa.
Asali: Legit.ng

