NAHCON: Shugaban Hukumar Alhazan Najeriya, Sheikh Abdullahi Pakistan Ya Yi Murabus
- Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya yi murabus daga matsayin shugaban hukumar kula da harkokin alhazai ta Najeriya (NAHCON)
- Wannan mataki da Sheikh Pakistan ya dauka na zuwa ne a lokacin da ake zargin matsalar cin hanci da rashawa ta dabaibaye NAHCON
- A kwanakin baya ne aka samu labarin cewa wasu daga cikin kwamishinonin hukumar NAHCON aun bukaci Shugaba Tinubu ya Sheikh Pantami
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Rahotannin da ke fitowa a daren nan na nuna cewa shugaban hukumar alhazan Najeriya, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan ya yi murabus daga mukaminsa.
Duk da babu wata sanarwa a hukumance kawo yanzu amma bayanai sun nuna cewa Sheikh Pakistan ya yi murabus ne a daidai lokacin da yake fuskantar matsin lamba daga wasu jami'an NAHCON.

Source: Facebook
Shugaban hukumar NAHCON ya yi murabus
Shafin Independant Hajj Reporters of Nigeria ya tabbatar da murabus din Sheikh Pakistan a wani gajeren sako da ya wallafa a Facebook a daren yau Litinin, 9 ga watan Fabarairu, 2026.
DW Hausa ta tabbatar da labarin murabus din Sheikh Pakistan, inda ta bayyana cewa hakan ba zai rasa nasaba da zarge-zargen cin hanci da rashawa da suka dabaibaye NAHCON a baya-bayan nan.
"Shugaban Hukumar Aikin Hajji ta Najeriya NAHCON, Farfesa Abdullahi Saleh Pakistan, ya yi murabus daga mukaminsa, sakamakon matsin lamba daga zargin cin hanci da rashawa da ya dabaibaye ayyukan hukumar," in ji rahoton.
Ita ma jaridar Aminiya ta samu labarin cewa Farfesa Abdullahi Usman Saleh ya ajiye mukaminsa, a daren Litinin, 9 ga watan Afrilu, 2026.
Lamarin dai ya zo a daidai lokacin da hukumar NAHCON ke kokarin kammala duk wasu shirye-shiryen gudanar da aikin Hajjin bana.
Dalilin ajiye aikin Farfesa Pakistan
Wani babban jami’i a hukumar NAHCON ya bayyana cewa ajiye mukamin Farfesa Pakistan na da alaƙa kai tsaye da takardar korafi da Majalisar Kwamishinonin hukumar ta aikewa Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Kwamishinonin sun shaidawa Shugaba Tinubu cewa suna zargin Farfesa Abdullahi da aikata wasu abubuwan da ba su dace ba a yayin gudanar da aikinsa a hukumar NAHCON.

Source: Twitter
A cewar jami’in, takardar korafin da aka gabatar ce ta sa Shugaban Ƙasa ya ɗauki matakin tilasta masa ajiye mukamin.
“Takardar korafin da aka aikewa Shugaban Ƙasa a kansa ce ta haddasa wannan mataki. Kowa ya san cewa tun bayan nadinsa, hukumar ke fama da takaddama da rikice-rikice daban-daban,” in ji jami’in.
NAHCON ta fara lallaba kasar Saudiyya
A dazu, kun ji cewa Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON) ta tabbatar da rufe karbar kudin kujerun Hajjin 2026, inda ta gargadi yan Najeriya su gujewa 'yan yaudara.
Ta sanar da jama’a cewa hukumomin Saudiyya, ta hannun Ma’aikatar Hajj da Umrah ta kasar, ta riga ta rufe shafin shigarwa da tantance bayanan maniyyatan ikin Hajjin 2026.
NAHCON ta nemi Saudiyya ta tsawaita wa'adin don ba wa hukumomin jin daɗin alhazzai na Najeriya damar kammala sanya bayanan maniyyatan da ba a riga an ɗora su a dandalin Nusuk Masar ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

