Hajji: Matsala Ta Tunkaro Wasu Maniyyatan Najeriya, NAHCON Ta Roki Saudiyya Alfarma
- Hukumar Alhazan Najeriya (NAHCON) ta tabbatar da rufe karbar kudin kujerun Hajjin 2026, inda ta gargadi yan Najeriya su gujewa 'yan yaudara
- NAHCON ta kuma bayyana cewa ta shigar da bukatar tsawaita lokacin rijistar maniyyata a shafin mahukuntan Saudiyya domin a iya sauke farali
- Hakan na zuwa ne bayan Ma'aikatar Hajji ta Umrah ta Saudiyya ta rufe shafin Nusuk Masar, wanda ake shigar da bayanan kowane maniyyaci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Hukumar Jin Daɗin Alhazzai ta Ƙasa (NAHCON) na ci gaba da shirye-shiryr domin tabbatar da aikin Hajjin 2026 ya gudana cikin nasara.
Hukumar NAHCON ta gargadi masu niyyar sauke farali a Hajjin 2026 da kada su biya kuɗi ga kowane mutum, ƙungiya, ko kamfani, tana mai bayyana cewa an riga an rufe karɓar kuɗaɗen aikin na bana a hukumance.

Source: Facebook
Saudiyya ta rufe shafin rijistar mahajjata
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Mataimakiyar Daraktan Yaɗa Labarai da Hulɗa da Jama’a ta hukumar NAHCON, Fatima Sanda Usara ta fitar, kamar yadda Daily Trust ta kawo.
Ta sanar da jama’a cewa hukumomin Saudiyya, ta hannun Ma’aikatar Hajj da Umrah ta kasar, ta riga ta rufe shafin shigarwa da tantance bayanan maniyyatak aikin Hajjin 2026.
NAHCON ta roki kasar Saudiyya alfarma
Sai dai kuma, NAHCON ta ce ta garzaya zuwa Saudiyya tare da neman a tsawaita lokacin don ba wa hukumomin jin daɗin alhazzai na Najeriya damar kammala sanya bayanan maniyyatan da ba a riga an ɗora su a dandalin Nusuk Masar ba.
Fatima Sanda ta ce:
"Hukumar NAHCON na fatan cewa za a amince da wannan bukata tata, kuma tana tabbatar wa jama’a cewa za ta bayar da sababbin bayanai da zarar an samu wata sanarwa daga Saudiyya."
Hukumar alhazan ta kuma buƙaci daukacin al'umma musamman maniyyata su riƙa bibiyar sahihan kafofinta na sadarwa don samun duk wani bayani da ya dace.
Sakon NAHCON ga 'yan Najeriya
Daga karshe, NAHCON ta gode bisa goyon baya da hadin kan da take samu daga yan Najeriya, tana mai cewa za ta yi duk abin da ya dace don tabbatar da an yi Hajjin bana cikin nasara.
Sanarwar ta ƙara da cewa:
"NAHCON tana godiya ga dukkan masu ruwa da tsaki bisa fahimta da haɗin kan da suke ba ta yayin da take aiki kafada-da-kafada da hukumomin Saudiyya don tabbatar da maniyyatan Najeriya sun gudanar da aikin Hajji cikin sauƙi."

Source: Facebook
Saudiyya za ta fara ba da bizar Hajji
A wani rahoton, kun ji cewa Ma’aikatar Hajji da Umara ta Saudiyya ta sanar da cewa za ta fara bayar da bizar aikin Hajji na shekarar 2026 daga ranar 8 ga Fabrairu 2026.
Wannan mataki yana daga cikin ƙoƙarin ma'aikatar na ganin an kammala shirye-shirye watanni kafin lokacin aikin Hajji ya yi domin sauƙaƙa wa maniyyata.
Hukumomin Saudiyya sun bayyana cewa sun fara wannan shiri ne tun ranar 8 ga watan Yunin 2025, inda aka ba ofisoshin Hajji na duniya damar tsara ayyukansu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

