Kotun Daukaka Kara Ta Raba Gardama kan Dakatarwar da Majalisa Ta Yi Wa Sanata Natasha
- Kotun daukaka kara ta zartar da hukunci a shari'ar da ke gabanta kan dakatarwar da majalisar dattawa ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan
- A hukuncin da kotun ta yanke, ta bayyana cewa shugaban majalisar dattawa na da ikon ba 'yan majalisa wuraren zama ta hanyar ba su kujeru
- Kotun ta bayyana cewa shugaban majalisar dattawa bai yi kuskure ba wajen hana Natasha yin magana yayin zaman majalisar na ranar, 20 ga watan Fabrairun 2025
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
FCT, Abuja - Kotun daukaka kara ta Abuja ta yanke hukunci kan dakatarwar da majalisar dattawa ta yi wa Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan.
Kotun ta yi hukuncin cewa majalisar dattawa ta yi aiki ne a cikin ikon da doka ta ba ta lokacin da ta dakatar da sanatar mai wakiltar Kogi Ta Tsakiya, bisa zargin rashin da’a.

Kara karanta wannan
Matar Bola Tinubu ta yi mamakin abin da Shugaba Trump ya mata a taron jama'a a Amurka

Source: Facebook
Tashar Channels tv ta kawo rahoto cewa kotun daukaka karar ta yanke hukuncin ne a ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairun 2026.
Wane hukunci kotu ta yanke kan karar Natasha?
Kotun daukaka karar, a hukuncin bai daya da kwamitin alkalai uku ya yanke, ta ce ta gamsu cewa ba a take hakkin majalisa ko hakkin kundin tsarin mulki na sanatar ba sakamakon dakatarwar da aka yi mata daga majalisar dattawa.
Sai dai kotun ta soke tarar Naira miliyan 5 da aka ci ta dangane da saƙon neman afuwa na barkwanci da ta yi wa shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio.
A cikin babban hukuncin da mai Shari’a Abba Muhammed ya karanta, kotun ta bayyana cewa shugaban majalisar dattawa bai yi kuskure ba wajen hana Sanatar Kogi damar magana a zaman majalisa na ranar 20 ga Fabrairu, 2025.
Kotu ta goyi bayan dakatar da Natasha
Alkali ya ce bai yi kuskure ba ne kasancewar ba ta zauna a kujerar hukuma da aka ware mata ba a lokacin zaman na majalisar dattawa, jaridar The Punch ta kawo labarin.
Kotun ta ƙara da cewa, dokokin Majalisar Dattawa sun bai wa shugaban majalisar ikon ware kujeru ga ‘yan majalisa, kuma doka ta tanadi cewa ɗan majalisa na da damar magana ne kawai daga kujerar da aka ware masa.
Wane hukunci kotun baya ta yanke?
A cikin hukuncinta na ranar 4 ga Yuli, alkalin babbar kotu, Binta Nyako, ta yanke cewa hakkin da dan majalisa ke da shi yana karkashin tanadin dokokin majalisar dattawa.

Source: Twitter
Ta bayyana cewa shugaban majalisar dattawa yana da ikon sauya tsarin zama na sanatoci, tare da kara wa da cewa Godswill Akpabio ya yi daidai wajen hana Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan damar yin magana a zaman majalisa.
Sai dai kotun ta soki tsawon lokacin dakatarwar da aka yi wa Sanata Natasha, tana mai bayyana shi a matsayin “ya wuce gona da iri” kuma “ya yi tsanani fiye da kima.”
Haka kuma, kotun ta umarce ta da ta biya tarar Naira miliyan 5.
Ana neman Natasha ta shiga APC
A wani labarin kuma, kun ji cewa sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan, ta yi magana kan shiga APC.
Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana cewa ba za ta taba komawa APC ba saboda wasu dalila nata na karan kanta.
Sanatar mai wakiltar Kogi ta Tsakiya ta ce har yanzu akwai wasu daga fadar shugaban kasa da ke ci gaba da yi mata tayin ta dawo APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

