Matar Bola Tinubu Ta Yi Mamakin Abin da Shugaba Trump Ya Mata a Taron Jama'a a Amurka

Matar Bola Tinubu Ta Yi Mamakin Abin da Shugaba Trump Ya Mata a Taron Jama'a a Amurka

  • Uwagidar shugaban Najeriya, Oluremi Tinubu ta yi mamakin yadda Shugaba Donald Trump ya karrama ta a taron addu'a a Amurka
  • Sanata Oluremi Tinubu ta samu jinjina da yabo daga Shugaba Trump yayin da ta kai wata ziyarar aiki kasar Amurka a makon da ya wuce
  • Wannan dai na zuwa ne a lokacin da Najeriya da Amurka ke kokarin kara karfafa dangantakar da ke tsakaninsu domin yakar ta'addanci

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Amurka - Uwargidar shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu na ci gaba da gudanar da ayyuukan da ta tsara da tattaunawa daban-daban a ziyarar aiki da ta kai kasar Amurka.

Sanata Oluremi Tinubu ta bayyana cewa ta yi matukar mamaki da irin karramawar da Shugaban kasar Amurka, Donald Trump ya yi mata a wannan ziyara da ta kai kasarsa.

Kara karanta wannan

Harin Kwara: Kungiyar CAN ta tura muhimmin sako ga Musulmi da aka hallaka

Oluremi Tinubu.
Uwargidar shugaban kasa, Sanata Oluremi Tinubu a wurin taron tallafawa mata Hoto: @SenRemiTinubu
Source: Twitter

Uwargidar shugaban kasar ta yi wannan jawabi ne yayin wata hira da ta yi da gidan talabijin na Fox News, lokacin da take ziyarar aiki a ƙasar Amurka.

Abin da ya ba uwargidar Tinubu mamaki

Sanata Oluremi Tinubu, ta bayyana cewa ta yi mamakin matuka game da yabo da karramawar da ta samu daga hannun Shugaban Amurka, Donald Trump, inda ta ce ba ta yi tsammani ba.

"Waye ya yi tunanin cewa Shugaba Donald Trump zai girmama ni kamar haka? Ina samun karramawa a matakin duniya kan dukkan waɗannan abubuwan, kuma abin da rayuwa take nufi ke nan. Idan abu zai yi kyau, yakan fara ne daga inda ba ka yi tsammani ba," in ji ta.

Wannan kalamai da ta yi sun biyo bayan halartar taron addu’o'in safe na ƙasa da aka gudanar kwanan nan a birnin Washington DC na kasar Amurka.

Karramawar da Trump ya yi wa Remi Tinubu

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya kausasa harshe kan harin 'yan ta'adda a Kwara, ya dauki mataki

A yayin babban taron na shekara-shekara, Shugaba Trump ya fito fili ya jinjina wa Uwargidan Shugaban Ƙasar ta Najeriya.

Trump ya bayyana Sanata Oluremi Tinubu a matsayin jagorar kiristoci abin girmamawa kuma mace mai daraja a ɗaya daga cikin majami’u mafi girma a Najeriya.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, taron addu'a na National Prayer Breakfast wani babban taro ne na shekara-shekara da ke haɗa mabiya addinai daban-daban a Amurka.

Taron ya kan tattaro shugabannin siyasa, ’yan majalisu, malaman addini, da baƙi daga ƙashen duniya don yin tunani da nazari kan lamurran addini, shugabanci, da haɗin kan duniya.

Remi Tinubu da Shugaba Trump.
Uwargidar shugaban Najeriya, Sanata Oluremi Tinubu da Shugaba Donald Trump na kasar Amurka Hoto: @SenRemiTinubu, @DonaldJTrump
Source: Twitter

Tsawon shekaru, wannan taro yana zama dandali na hulɗar diflomasiyya da kuma nuna karramawa ga manyan baƙi daga ƙasashen waje da suka halarci taron.

Matar Shugaba Tinubu ya yabawa Shugaba Trump, tana mai cewa ta yi mamakin karamar da ya mata a wannan taro da ke tara manya daga sassa daban-daban na duniya.

An tara wa uwargidar Tinubu N20bn

A wani rahoton, kun ji cewa uwargidar shugaban kasa, Oluremi Tinubu, ta tabbatar da cewa, 'yan Najeriya sun hada mata kudin da ya kai Naira biliyan 20.

Kara karanta wannan

Trump ya ba da mamaki da ya girmama matar Tinubu a wajen taron Amurka

An ruwaito cewa, uwargidar shugaban kasar ce da kanta ta nemi 'yan Najeriya, masu kishin kasa, su tara mata wannan kudi a lokacin bikin cikar ta shekara 65 a duniya.

Matar Shugaba Bola Tinubu ta ce za ta yi amfani da dukkanin kudin da aka tara wajen kammala gina babban dakin karatu na kasa a Abuja .

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262