Tofa: Wani Magidanci Ya Hau Dokin Zuciya, Ya Burma wa Ɗansa Wuƙa har Lahira
- Wani magidanci mai suna Iseleto ya soka wa dansa Miracle wuka har lahira a Jihar Delta bayan dan ya raba gidan mahaifinsa
- Wanda ake zargin ya yaudari dansa ne zuwa daji inda ya soka masa wuka sannan ya tsere yana barazanar kashe matarsa a waya
- 'Yan sanda sun tabbatar da faruwar kisan inda suka bayyana cewa suna cigaba da farautar uban da ya aikata wannan danyen aiki
Delta - Ana zargin wani magidanci a garin Osubi na jihar Delta ya hallaka dan cikinsa ta hanyar soka masa wuka inda yaron ya sheka lahira.
Lamarin ya yi mutukar daurewa jama'a kai, amma shaidar da aka samu daga bakin mutane ta tabbatar da cewa wanda ake zargin zai iya aikata hakan.
Wani magidanci ya burmawa dansa mai shekaru 23 wuka a cikinsa inda ya sheka lahira. Wanda ake zargin ya tsere har yanzu babu amonsa balle labarinsa.

Source: Original
Abin da ya hada uba da dansa
Magidancin da aka sani da Iseleto ya kashe ɗansa mai shekara 23, Miracle, ta hanyar soka masa wuƙa a ranar Lahadi, rahoton jaridar Punch ya ruwaito.
Lamarin ya faru ne a garin Osubi dake ƙaramar hukumar Okpe, bayan da ɗan ya yi ƙoƙarin samar da zaman lafiya a gidan na mahaifinsa.
Rahotanni sun nuna cewa Miracle ya kama wa kansa da kishiyar mahaifiyarsa wani gida daban domin su zauna su biyu don kauce wa rigima.
Wannan mataki ya tunzura Iseleto, inda ya yaudari ɗan nasa zuwa cikin daji sannan ya soka masa wuƙa sau da dama da wata babbar takobi.
Ikirarin magidancin da ake zargi da kisa
Bayan aikata wannan danyen aiki, Iseleto ya tsere daga garin, yayin da ɗansa ya yi ƙoƙarin rarrafe zuwa kan hanya kafin ya rasu.
Miracle ya rasu ne a asibiti bayan ya bayyana wa mutane yadda mahaifinsa ya yaudare shi zuwa dajin domin ya kashe shi a can.
Wanda ake zargin ya kira ƴar matarsa ta waya inda ya amince cewa shi ya kashe ɗan, sannan ya yi barazanar kashe matar tasa.

Kara karanta wannan
Attajiri lamba 1 a duniya, Elon Musk ya bayyana abin da kudi ba za su iya saye ba
Ya bayyana cewa zai kashe matarsa da ƴar tata saboda sun bar gidansa ba da izini ba, wanda hakan ya kawo ƙarshen zaman auren nasu gaba ɗaya.

Source: Facebook
Shaidar da aka yi wa mahaifin a gari
Mazauna garin sun bayyana Iseleto a matsayin mashayi kuma ma'abocin cin bashi wanda ya saba dukan matarsa idan ya bugu da giya.
Suka ce yana ƙoƙarin saduwa da matarsa ta ƙarfin tsiya a gaban ƴaƴansu a ɗaki ɗaya, idan ta ƙi kuma sai ya doke ta.
Har ila yau, an bayyana cewa Iseleto ya taɓa ƙoƙarin yin lalata da ƴar matar tasa, kuma saboda ta ƙi, ya kore ta daga gidan.
Kakakin rundunar ƴan sandan Jihar Delta, SP Bright Edafe, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa har yanzu ana farautar wanda ake zargin.
An kashe uban daba a Kano
A wani labari na daban, mun bayyana muku cewa rikicin 'yan daba a Kano ya yi sanadiyyar mutuwar wani uban daba bayan an labta masa sara a wuya yayin wani harin daukar fansa.
Jami'an yan sanda sun yi nasarar kama mutane tara tare da tarwatsa wasu 'yan daba da suka yi kokarin sake tada yamutsi a Mariri.
Rundunar tsaro ta tabbatar da cewa al'amura sun lafa a yankin Kawo yayin da ake ci gaba da neman sauran yan daban da suka tsere.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
