Shugaba Tinubu Ya Damu da Yadda 'Yan Bindiga ke Cutar da Tattalin Arzikin Najeriya

Shugaba Tinubu Ya Damu da Yadda 'Yan Bindiga ke Cutar da Tattalin Arzikin Najeriya

  • Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya nuna damuwa kan ayyukan 'yan bindiga da 'yan ta'adda a wasu jihohin Najeriya
  • Mai girma Bola Tinubu ya bayyana cewa ayyukan sun saba da al'adunmu, kuma sum cutar da tattalin arzikin kasar nan
  • Shugaban kasar ya sha alwashin daukar matakan da suka dace domin murkushe 'yan bindiga da 'yan ta'adda masu farmakar bayin Allah

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

FCT, Abuja - Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi magana kan ayyukan 'yan bindiga da 'yan ta'adda a Najeriya.

Shugaba Tinubu ya bayyana ayyukan ’yan bindiga da 'yan ta'adda a matsayin abubuwan da ba su dace da al’adar Najeriya ba, kuma babban cikas ne ga tattalin arziki da ke bukatar mafita cikin gaggawa.

Tinubu ya sha alwashin murkushe 'yan bindiga
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Jaridar The Punch ta ce Shugaba Tinubu ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da taron kwanaki biyu na Majalisar rattalin arziki ta Kasa (NEC) da aka gudanar a dakin taro na fadar shugaban kasa da ke Abuja, a ranar Litinin, 9 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun kashe bayin Allah, sun sace babban malami da wasu mutane 10

Tinubu ya sha alwashi kan 'yan bindiga

Shugaban kasar ya sha alwashin cewa gwamnatinsa za ta karfafa dakarun tsaro domin murkushe wannan barazana, jaridar Daily Trust ta kawo labarin.

Hakazalika ya kuma yi alkawarin nemo hanyoyin murkushe 'yan bindiga da 'yan ta'adda, inda ya ce ayyukansu sun hana 'yan Najeriya barci.

“Zamu nemo hanyoyin karfafa dakarunmu na tsaro domin doke ta’addanci da yaki da ’yan bindiga. Ina yi muku alkawari, wannan ne abin da ya hana mu barci da daddare, amma ina ba ku tabbacin cewa za mu yi nasara ta hanyar jajircewa da juriya.”
“Wadannan ayyukan ta'addancin da 'yan bindiga ba abin da za mu amince da shi ba ne. Ba sa cikin al’adunmu, baki ne a gare mu. Saboda haka, cikas ne ga tattalin arziki idan ba mu nemo musu mafita cikin gaggawa ba.”

- Shugaba Bola Tinubu

Tinubu ya yaba wa gwamnonin jihohi

A wajen taron, Tinubu ya jinjina wa wasu gwamnonin jihohi kan kokarin da suke yi na yaki da rashin tsaro, inda ya ambaci gwamnonin jihohin Borno da Katsina.

Kara karanta wannan

Ana jimamin harin Kwara, 'yan Boko Haram sun kashe sojojin Najeriya

“Ina jinjina muku da dama daga cikinku, musamman gwamnan jihar Borno, da na Katsina, da ma da yawa daga cikinku wadanda kuka jajirce wajen kare ’yancinmu da dukiyoyinmu."

- Shugaba Bola Tinubu

Shugaba Tinubu ya damu kan ayyukan 'yan bindiga
Mai girma Shugaba Bola Tinubu a ofis Hoto: @DOlusegun
Source: Twitter

'Yan bindiga na kai hare-hare

Kalaman shugaban na zuwa ne sakamakon hare-haren ’yan bindiga da suka yi sanadiyyar asarar rayuka a jihohi da dama.

Musamman kisan kiyashin da aka yi ranar 3 ga watan Fabrairu 2026 a garuruwan Woro da Nuku da ke karamar hukumar Kaiama a jihar Kwara, inda ake zargin wasu masu tsattsauran ra’ayin Islama sun kashe a kalla mutane 162.

Tinubu ya gana da sojojin Amurka

A wani labarin kuma, kun ji cewa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gana da wata tawagar sojojin Amurka a fadar Aso Rock Villa.

​Tawagar sojojin na Amurka ta zo ne ƙarƙashin jagorancin kwamandan rundunar sojojin Amurka a Afirka (USAFRICOM), Janar Dagvin R. Anderson, tare da wasu jami’ai.

Taron ya gudana ne tare da Mai ba shugaban kasa shawara kan tsaro (NSA), Malam Nuhu Ribadu, da shugabannin rundunonin tsaron Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng