Irin Wa'azin da Gwamnan Kaduna ke So Malamai Su Yi a Ramadan 2026

Irin Wa'azin da Gwamnan Kaduna ke So Malamai Su Yi a Ramadan 2026

  • Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya yi kira ga malamai da kafafen yaɗa labarai da su yi amfani da watan Ramadan wajen ƙarfafa zaman lafiya
  • Ya yi kiran ne a taron shekara-shekara da kungiyar Jama’atu Nasril Islam ta shirya a hedikwatarta ta ƙasa da ke Kaduna kan azumin Ramadan
  • Gwamnatin jihar Kaduna ta jaddada aniyar cigaba da haɗin gwiwa da kungiyoyin addini domin tabbatar da zaman lafiya da fahimtar juna

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kaduna – Gwamnan Jihar Kaduna, Uba Sani, ya buƙaci malaman Musulunci da kafafen yaɗa labarai da su yi amfani da watan Ramadan na 2026 wajen kira game da zaman lafiya da karfafa haɗin kan ƙasa.

Gwamnan ya yi kiran ne a taron shekara-shekara da ake kafin Ramadan na shekarar 2026 da Jama’atu Nasril Islam (JNI) ta shirya a hedikwatarta ta ƙasa da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

Za a samu sauki, Tinubu ya amince a bude iyakar Najeriya da Nijar don kasuwanci

Gwamna Uba Sani da wajen taron JNI a Kaduna
Gwamna Uba Sani a hagu, mahalarta taron JNI a Kaduna a dama. Hoto: Uba Sani|Umar Shehu Zaria
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa sakataren gwamnatin jihar Kaduna, Dr Mu’azu Meyare, ne ya wakilci gwamna Uba Sani a wajen taron da JNI ta yi.

Ramadan: Kiran Uba Sani ga malamai

Jaridar the Nation ta rahoto Dr Meyare ya ce Najeriya na buƙatar muryoyin da za su karfafa jama'a wajen hadin kai da fahimtar juna maimakon masu raba kan al'umma.

Ya buƙaci malaman Musulunci da su tabbatar cewa darussan tafsiri da sauran shirye-shiryen da za su yi su shafi wayar da kai, su ƙarfafa haɗin kai, zaman tare, adalci a cikin al’umma, da sauransu.

A cewarsa, watan Ramadan wata dama ce ta musamman da ke tunatar da mutane game da tausayi, ladabi da biyayya, kara kusanci ga Allah, tare da ƙarfafa dabi’u irin su sadaka, kishin ƙasa da addu’o’i ga ƙasa da shugabanninta.

Kira ga kafafen yada labarai

Gwamnatin Jihar Kaduna ta kuma yi kira ga gidajen rediyo, talabijin da kafafen sada zumunta da su yi aiki da ƙwarewa da taka-tsantsan wajen watsa shirye-shiryen addini a watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Tinubu ya tura Shettima Kwara da muhimmin sako bayan kisan Musulmai

Dr Meyare ya gargaɗi masu aikin jarida da su guji watsa bayanan da ka iya tayar da hankali, rashin jituwa ko rarrabuwar kai, yana mai cewa ya kamata su mayar da hankali kan hadin kai.

Mahalarta taron JNI a Kaduna
Malamai a taron JNI game da Ramadan a Kaduna. Hoto: Umar Shehu Zaria
Source: Facebook

Ya jaddada cewa hidima ga al'umma na daga cikin manyan ibadu a Musulunci, don haka ya dace masu isar da saƙo su yi amfani da kafafensu wajen ƙarfafa tausayi, zaman lafiya da mutunta juna a tsakanin al’umma.

Malamai sun nemi cire shugaban INEC

A wani labarin, mun kawo muku cewa kwamitin shari'a na Najeriya ya sake kira ga shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu kan sauke shugaban INEC.

Kwamitin ya bayyana cewa ba saboda sabanin addini ya ke nema a cire Farfesa Joash Amupitan ba, sai dai saboda ya nuna kiyayya ga Musulmai.

Sakataren kwamitin shari'a ya bayyana cewa ba su taba kira a sauke shugaban INEC ba duk da cewa Kiristoci ne suka fi rike hukumar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng