Raba Najeriya: 'Yan Biyafara Sun kai Ruwa Rana da 'Dan Majalisar Amurka

Raba Najeriya: 'Yan Biyafara Sun kai Ruwa Rana da 'Dan Majalisar Amurka

  • Haramtacciyar kungiyar IPOB ta ce hadin kan Najeriya bai kare Kiristoci daga hare-hare ba fiye da shekaru 60 da aka dade ana fama da su
  • IPOB ta bayyana cewa matsalar tsaro a Najeriya ta samo asali ne daga tsarin kasa da aka gada tun mulkin mallaka da Turawa suka yi a kasar
  • Kungiyar ta yi magana ne bayan dan majalisar Amurka da ya zo Najeriya, Riley Moore ya bayyana cewa ba ya goyon bayan raba kasar nan

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Anambra – Kungiyar IPOB ta mayar da martani ga kalaman wani dan majalisar dokokin Amurka, Riley Moore, game da hadin kan Najeriya.

IPOB ta yi zargin cewa kalaman dan majalisar sun ginu ne a kan fahimta mara zurfi game da tarihin Najeriya da halin da Kiristoci ke ciki, musamman a Arewa da wasu sassan Kudu maso Yamma.

Kara karanta wannan

Harin Kwara: Kungiyar CAN ta tura muhimmin sako ga Musulmi da aka hallaka

Nnamdi Kanu da dan majalisar Amurka
Nnamdi Kanu a hadu, dan majalisar Amurka a dama. Hoto: Riley Moore|Omoyele Sowore
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa kakakin IPOB, Emma Powerful ya ce dagewa kan hadin kan Najeriya bai haifar da tsaro ko adalci ga Kiristoci ba, sai dai ma ruruta matsalolin kasar.

Dalilan IPOB kan hadin kan Najeriya

IPOB ta yi zargin cewa fiye da shekaru 60 na karkashin tsarin da Turawan mulkin mallaka suka kirkira, amma hakan bai hana kashe-kashe, kona coci-coci da tilasta wa dubban mutane barin muhallansu ba.

A bayanin da ta yi, kungiyar IPOB ta jaddada cewa matsalar Najeriya ba karancin hadin gwiwar tsaro da kasashen waje ba ne.

IPOB ta yi zargin cewa gurbataccen tsarin kasa da ya hada al’adu da addinai da ba su dace da juna ba ne ya hana magance matsalolin.

Martani ga 'dan majalisar Amurka

Dangane da ikirarin cewa neman ‘yancin kai na iya karfafa ta’addanci, IPOB ta ce wannan fahimta ce maras kyau da mutane ke yi.

Kara karanta wannan

Tarihin yaron Shekau da ya jagoranci kashe Musulmai kusan 200 a Kwara

Ta yi ikirarin cewa ta’addanci yana bunƙasa ne a inda aka danne hankin mutane, ba wai ta hanyar kokarin neman ballewa da suke yi ba.

Martanin IPOB ya zo ne bayan More ya saki wani sako a shafinsa na X da ke cewa ba ya goyon a raba Najeriya saboda hakan zai iya zama matsala ga kasar da ma Afrika.

IPOB ta ce tarihi ya nuna cewa rabuwa a wasu lokuta ya samar da kariya ga kungiyoyin addini da ke fuskantar barazana.

A cewar Emma Powerful, gwagwarmayar da shugabansu, Mazi Nnamdi Kanu, ke jagoranta ba kira ba ne ga tashin hankali ba, suna neman a yi taron raba gardama ne ta hanyar dimokuradiyya.

Nnamdi Kanu a kotu kafin masa hukunci
Yadda aka kai shugaban IPOB, Nnamdi Kanu kotu kafin yanke masa hukunci. Hoto: Omoyele Sowore
Source: Getty Images

Hasashen IPOB kan kafa kasar Biyafara

Kungiyar ta ce dawo da Biyafara zai samar da yanayin rayuwa mai kyau ga Kiristoci da sauran addinai, tare da yiwuwar zama mafaka ga Kiristocin da ake tsanantawa a wasu sassan Najeriya.

A karshe, kungiyar ta yi gargadi da cewa kin amincewa da hanyoyin lumana na fita daga Najeriya zai kara tsawaita rashin tsaro da ake fama da shi.

Kara karanta wannan

An fara bincike ministan Tinubu da ya yi murabus bayan zargin aiki da takardun bogi

Kanu ya ba 'yan IPOB umarni

A wani labarin, mun kawo muku cewa Shugaban kungiyar IPOB da ke son ballewa a Najeriya, Nnamdi Kanu ya fitar da sanarwa daga kurkuku.

Nnamdi Kanu ya yi kira ga 'yan kungiyar da su dakatar da zaman gida da suke yi duk ranar Litinin da suka shafe shekaru suna yi.

Ya bayyana cewa za su daina zaman ne domin samun damar cigaba da zuwa makaranta, kasuwa da sauran abubuwan yau da kullum.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng