Obasanjo, Yaradua da Manyan Sojoji 4 da Aka Taba Yi Wa Hukuncin Yunkurin Juyin Mulki a Najeriya
FCT, Abuja - Hedkwatar tsaro ta kasa ta tabbatar da cewa an cafke wasu sojoji bisa zargin yunkurin juyin mulki kan gwamnatin shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Hedkwatar tsaron kasar ta bayyana cewa za a gurfanar da sojojin gaban kotu da zarar an kammala bincike kan zarge-zargen da ake yi musu.

Source: Getty Images
Legit Hausa ta tattaro manyan sojojin da aka taba yankewa hukunci kan yunkurin yin juyin mulki a Najeriya.
An sha yin juyin mulki a Najeriya
Tun samun 'yancin kai daga wajen Turawan mulkin mallaka dai, Najeriya ta fuskanci juyin mulki da yunkurin kifar da gwamnati sau da dama.
Daga shekarar 1960 zuwa 1999 an yi yunkurin juyin mulki fiye da sau 10 a Najeriya, inda wasu suka yi nasara, wasu kuma ba su yi ba.
Ga jerin manyan sojojin da aka taba hukuntawa bayan samunsu da laifi a yunkurin juyin mulki.
1. Laftanar Kanal Bukar Suka Dimka (1976)
Laftanar Kanal Bukar Suka Dimka ya jagoranci yunkurin juyin mulki a ranar Juma'a, 13 ga watan Fabrairun 1976.
Babban lamarin da ya faru sakamakon yunkurin juyin mulkin, shi ne kisan shugaban kasa na wancan lokacin, Janar Murtala Ramat Muhammed.
An harbe shi ne a Ikoyi, Legas, lokacin da yake kan hanyarsa ta zuwa ofis a Dodan Barracks ba tare da jami’an tsaro sun raka shi ba, shafin executedtoday ya kawo labarin.
Daga baya an kama Laftanar Kanal Dimka da jami'an sojoji da fararen hula sama da 100 sakamakon wannan yunkuri.
An yankewa Laftanar Kanal Bukar Suka Dimka hukuncin kisa tare da sauran sojojin da aka samu da laifi.
A ranar, 15 ga watan Maris 1975 an aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar harbi kan Dimka da sauran mambobi shida na yunkurin juyin mulkin a gidan yarin Kirikiri.
Sauran wadanda aka yankewa hukunci sun hada da:
- Maj. Gen. I. D. Bisalla
- Lt. Col. A. R. Aliyu
- Lt. Col. Ayuba Tense
- Lt. Col. T. K. Adamu
- Lt. Col. A. B. Umaru
- Col. A. D. S. Way
- Maj. M. M. Mshelia
- Maj. I. B. Ribo
- Maj. K. K. Gagraaj. Ola Ogunmekan
- Maj. J. W. Kasai
- Capt. M. Parvwong
- Capt. J. F. Idi
- Capt. S. Wakins
- Capt. Augustine Dawurang
- Capt. A. A. Aliy
- Capt. M. R. Gelip
- Lt. Mohammed
- Lt. E. L. K. Shelleng
- Lt. William Seri
- Lt. Peter Ggani
- Lt. O. Zagni/Zagmi
- Lt. S. Wayah
- Warrant Officer II Monday Monchon
- Warrant Officer II Sambo Dankshin
- Warrant Officer II Emmanuel Dakup Seri
- Staff Sgt. Richard Dungdang
- Sgt. Sale Pankshim
- Sgt. Ahmadu Rege
- Sgt. Bala Javan
- Abdulkarim Zakari (farar hula)
- Joseph D. Gomwalk
- Lt. S. Kwale
- Warrant Officer H. E. Bawa
- Col. I. Buka
- Maj. J. K. Afolabi
- H. Shaiyen
- Helen Gomwalk (matar Joseph Gomwalk)
- Capt. Peter Tembong
- Capt. C. Wuyep
- Capt. A. A. Maidobo
- Maj. A. K. Abang
- Gyang Pam
- S. K. Dimka
- D. Contulla
- Warrant Officer II E. Izah
- Sgt. I. Bupwada
- 2nd Lt. A. Walbe
- S. Anyafodu
- Capt. I. Gowon
- J. Tuwe
- Lt. Col. J. S. Madugu
2. Manjo Janar Mamman Vatsa
A watan Disamban shekarar 1985 gwamnatin Janar Ibrahim Badamasi Babangida ta zargi Manjo Janar Mamman Vatsa da hannu a yunkurin juyin mulki.

Source: Twitter
An yi zargin ne kan Mamman Vatsa tare da wasu jami'an sojoji tara na yunkurin hambarar da gwamnatin Janar Babangida.
An yanke musu hukuncin kisa ta hanyar harbi bayan da kotun sojoji da aka kafa ta same su da laifi a shekarar 1986.
Jaridar Premium Times ta ce an aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar harbi kan Mamman Vatsa da sauran sojoji tara a watan Maris na shekarar 1986.
3. Gideon Orkar (1990)
Wasu jami’an soja karkashin jagorancin Manjo Gideon Orkar, sun yi yunkurin juyin mulki a ranar, 22 ga watan Afrilun 2022.

Source: Twitter
Tashar BBC Pidgin ta ce sojojin sun kai hari a Dodan Barracks da nufin kifar da gwamnatin Janar Ibrahim Babangida a wancan lokacin.
Sai dai, yunkurin juyin mulkin bai yi nasara ba, inda aka cafke Gideon Orkar da sauran sojoji da dama ciki har da fararen hula.

Kara karanta wannan
Muhimman abubuwa 5 da bincike ya gano kan shirin juyin mulkin da aka yi a Najeriya
An yankewa Manjo Gideon Orkar hukuncin kisa ta hanyar harbi tare da sauran mutane 47 da ke da hannu a yunkurin juyin mulkin.
A ranar, 27 ga watan Yulin shekarar 1990 aka aiwatar da hukuncin kisa ta hanyar rataya ga Manjo Gideon Orkar da sauran mutanen.
Wadanda ake zargin da hannunsu ciki akwai:
- Lt. Col. Anthony Nyiam
- Major Saliba Mukoro
- Major Cyril Obahor
- Major G.T.O. Edoja
- Chief Great Ovedje Ogboru
4. Olusegun Obasanjo (1995)
Olusegun Obasanjo na daga cikin manyan sojojin da gwamnatin Janar Sani Abacha ta cafke bisa zargin shirya mata juyin mulki a shekarar 1995.

Source: Getty Images
Bayan gurfanar da shi gaban kotun sojoji wadda ta yi zamanta a sirrance, an yanke masa hukuncin kisa.
Daga wata kotun da aka kafa ta rage hukuncin zuwa shekara 30 a gidan yari, sannan aka kara rage hukuncin zuwa shekara 15.
An sake shi a shekarar 1998 bayan ya shafe shekara uku a gidan yari.
Jaridar The Nation ta ce tsohon shugaban kasar ya bayyana cewa rashin yin shiru da bakinsa ne ya sanya aka kama shi tare da tura zuwa gidan yari.
5. Shehu Musa Yar’adua (1995)
A watan Maris na shekarar 1995, gwamnatin soja ta marigayi Janar Sani Abacha ta yi zargin an yi yunkurin shirya mata juyin mulki.

Source: Twitter
Marigayi Janar Shehu Musa Yar’Adua na daga cikin manyan sojojin da aka kama bisa zargin yunkurin kifar da gwamnatin Janar Sani Abacha.
Kotun soji ta yanke masa hukuncin kisa a shekarar 1995. Daga baya aka rage hukuncin zuwa daurin rai-da-rai, amma ya mutu a gidan yari ranar 8 ga watan Disamba, 1997.
6. Laftanar Janar Oladipo Diya (1997)
A shekarar 1997 an zargi Laftanar Janar Oladipo da yunkurin kifar da gwamnatin marigayi Janar Sani Abacha.

Source: Getty Images
An yankewa Laftanar Janar Oladipo wanda ya kasance mataimakin Abacha a wancan lokacin, hukuncin kisa tare da sauran masu hannu a yunkurin.
Jaridar The Guardian ta ce daga baya an yi masa afuwa bayan rasuwar marigayi Sani Abacha a shekarar 1998.
An kama tsohon Janar kan yunkurin juyin mulki

Kara karanta wannan
Wata sabuwa: Lauya ya kawo rudani game da wadanda suka shirya yi wa Tinubu juyin mulki
A wani labarin kuma, kun ji cewa Rundunar sojojin Najeriya na ci gaba da gudanar da bincike kan yunkurin kifar da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.
Jami'an tsaro sun cafke wani tsohon Janar mai rike da sarauta, Manjo Janar Mohammed Ibrahim Gana mai ritaya.
Wata majiya ta bayyana cewa an kama tsohon Janar din ne sakamakon dadaddiyar alakar da ke tsakaninsa da wanda ake zargi da jagorantar yunkurin juyin mulkin, Kanar Alhassan Ma’aji.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


