Ana Wata ga Wata: Gwamna Bala Ya Fatattaki Kwamishinan Bauchi daga Aiki
- Mai girma Bala Mohammed ya sallami kwamishinan tsaro Alhaji Ibrahim Gambo Galadima daga mukaminsa a wani dan karamin garambawul
- Gwamnatin jihar Bauchi ta bayyana cewa an dauki wannan mataki ne domin shigo da sababbin dabarun gudanar da mulki da inganta tsaro
- Sannan gwamnati ta bai wa jama'ar Bauchi tabbacin cewa za ta sanar da sabon kwamishinan da zai maye gurbin Ibrahim nan ba da dadewa ba
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Bauchi - Gwamnan Bala Mohammed, ya tsige kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Bauchi, Alhaji Ibrahim Gambo Galadima, daga muƙaminsa.
Sanarwar sallamar kwamishinan ta fito ne ta hannun mai magana da yawun gwamnan, Kwamared Mukhtar Gidado, a safiyar ranar Litinin, 9 ga Fabrairu, 2026.

Source: Twitter
Bauchi: Gwamna ya kori kwamishina
Mukhtar Gidado ya bayyana cewa wannan mataki ya biyo bayan ɗan ƙaramin garambawul da gwamnan ya yi wa mambobin majalisar zartarwar jihar, in ji rahoton Leadership.

Kara karanta wannan
Alkawarin da Abba Kabir ya yi ga wadanda suka yi hatsari a Kano bayan jajanta musu
Korar Alhaji Ibrahim Galadima ta fara aiki ne nan take, kamar yadda sanarwar da aka raba wa manema labarai a birnin Bauchi ta nuna.
Gwamnatin jihar ta bayyana cewa ana yin irin waɗannan sauye-sauye ne lokaci zuwa lokaci domin shigo da sababbin dabarun gudanar da mulki.
Babban burin hakan shine ƙarfafa tsarin mulki da kuma tabbatar da cewa ana aiwatar da manufofin gwamnati yadda ya kamata a faɗin jihar.
Dalilin sallamar kwamishinan Bauchi
Sanarwar ta kuma cewa wannan garambawul zai taimaka wajen sake fasalin majalisar zartarwa domin inganta yadda ake isar da ayyukan raya ƙasa ga al'umma.
Gwamna Bala ya gode wa Ibrahim Galadima kan gudunmawar da ya bayar a lokacin da yake riƙe da muƙamin, sannan ya yi masa fatan alheri.
Sanarwar ta ce:
"Mai girma Sanata Bala Abdulkadir Mohammed , gwamnan jihar Bauchi, ya amince da dan karamin garambawul a majalisar zartarwarsa.
"A wannan bagire, an sallami kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida, Alhaji Ibrahim Galadima daga mukaminsa na mamban majalisar zartarwa nan take."
Gwamnatin jihar ta tabbatar wa mazauna Bauchi cewa tana nan daram kan alƙawarinta na tabbatar da zaman lafiya da tsaro, in ji rahoton Punch.

Source: Twitter
Yaushe za a maye gurbin kwamishinan Bauchi?
Sanarwar ta nuna cewa za a sanar da wanda zai maye gurbin kwamishinan da aka sallama nan ba da jimawa ba bayan an kammala tantancewa.
A halin yanzu, sauran ayyukan ma'aikatar za su ci gaba da gudana a ƙarƙashin jagorancin babban sakataren ma'aikatar har sai an naɗa sabon kwamishina.
Wannan shine garambawul na baya-bayan nan da gwamnan ya gudanar tun bayan sa hannu kan kasafin kuɗin jihar na shekarar 2026 a watan Disamba.
Gwamna Bala ya kori kwamishina
A wani labarin, mun ruwaito cewa, gwamatin Bauchi karkashin jagorancin Gwamna Bala Mohammed ta yi sauye-sauye a majalisar zartarwar jihar.
Gwamna Bala ya sallami Hajiya Zainab Baban-Takko daga mukaminta na Kwamishiniyar Harkokin Mata da Ci gaban Yara cikin gaggawa.
Hakan ya zo kwanaki bayan wasu sauye-sauye a majalisar, ciki har da tsige wasu manyan jami’ai, da kuma nadin sababbin mukarraban gwamnati.
Asali: Legit.ng
