Za a Samu Sauki, Tinubu Ya Amince a Bude Iyakar Najeriya da Nijar don Kasuwanci

Za a Samu Sauki, Tinubu Ya Amince a Bude Iyakar Najeriya da Nijar don Kasuwanci

  • Gwamnatin Tarayya ta amince da sake bude iyakar Tsamiya dake Jihar Kebbi domin ci gaba da kasuwanci tsakanin Najeriya da Jamhuriyar Nijar
  • Shugaban Kwastam Adewale Adeniyi ya bayyana cewa za a yi amfani da fasahar ICT domin sa ido kan kayayyaki da kuma tabbatar da tsaro a iyakar
  • Gwamna Nasir Idris na Jihar Kebbi ya yaba da wannan mataki inda ya yi alkawarin tallafa wa iyalan jami'an da suka rasa rayukansu a bakin aiki

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Kebbi - Shugaban Hukumar Kwastam ta Ƙasa, CG Adewale Adeniyi, ya sanar da cewa Shugaba Bola Tinubu ya amince a sake buɗe iyakar ƙasa ta Tsamiya.

Adeniyi ya bayyana hakan ne a ranar Asabar yayin wata tattaunawa da masu ruwa da tsaki, ciki har da masu fitar da kaya zuwa kasashen waje da manoman albasa.

Kara karanta wannan

Gwamna ya hango hadari, ya rufe kasuwanni da tashoshin mota a jiharsa

CG Adewale Adeniyi ya ce Tinubu ya ba da izinin bude iyakar Tsamiya da ke Kebbi
Shugaban hukumar Kwastam na kasa, Adewale Adeniyi da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @CustomsNG, @DOlusegun
Source: Twitter

Ya tabbatar wa ƴan kasuwar cewa gwamnati tana sane da mawuyacin halin da aka shiga sakamakon daɗewar da aka yi ana takaita zirga-zirga, in rahoton Tribune.

An ɗauki wannan matakin ne bayan tuntubar jami'an diflomasiyya da na tsaro tsakanin Najeriya da kuma ƙasashe maƙwabta domin samar da mafita mai dorewa.

Matakan tsaro don bude iyakar Najeriya

Shugaban Kwastam ya jaddada cewa za a gudanar da kasuwancin ne karkashin tsauraran matakan tsaro domin hana ɓata-garin da ba jami'an gwamnati ba cin moriyar hanyar.

Za a tura sabbin dabarun fasahar sadarwa (ICT) waɗanda za su haɗa ayyukan kwastam na Najeriya da na Jamhuriyar Benin da kuma Nijar.

Wannan tsari zai taimaka wajen sa ido kan kayayyaki, tabbatar da gaskiya, da kuma sauƙaƙa ayyukan bayyana kaya ba tare da bata lokaci ba.

Adeniyi ya gargaɗi direbobin manyan motoci kan kauce wa hanyoyin da aka amince da su, yana mai cewa duk motar da aka kama za a ƙwace ta.

Kara karanta wannan

Harin Kwara: Kungiyar CAN ta tura muhimmin sako ga Musulmi da aka hallaka

Muhimmancin garuruwan kan iyaka

Hukumar Kwastam ta bayyana mahimmancin raya al'ummar dake zaune a kan iyaka domin su ji cewa ana damawa da su a cikin arzikin ƙasar, in ji rahoton Punch.

Gwamna Nasir Idris ya ce zai taimaka wa gwamnati kan bude iyakar Tsamiya.
Gwamnan jihar Kebbi, Nasir Idris. Hoto: @NasiridrisKG
Source: Facebook

Adeniyi ya yaba wa Gwamnan Jihar Kebbi, Nasir Idris, kan yadda yake ba wa al'ummar kan iyaka muhimmanci da kuma kishin tsaro da yake da shi.

Gwamna Nasir Idris ya nuna gamsuwarsa da wannan mataki, inda ya bayyana shirye-shiryen jiharsa na ba wa jami'an tsaro dukkan haɗin kan da ya kamata.

Haka kuma, gwamnan ya yi alkawarin tallafa wa iyalan jami'an kwastam da aka kashe a bakin aiki kamar yadda tsarin gwamnatinsa ya tanada a halin yanzu.

Ana sa ran wannan mataki zai farfaɗo da tattalin arzikin Jihar Kebbi da ma Najeriya baki ɗaya ta hanyar sauƙaƙa safarar amfanin gona zuwa ƙasashen waje.

Amfanin bude iyakokin Najeriya

A wani labari, mun ruwaito cewa, kasuwannin hatsi na fuskantar karuwar shigo da kaya daga kasashen makwabta wanda ya shafi 'yan kasuwa da manoma a Neja.

Kara karanta wannan

Bayan kyautar N100m, gwamna Abba ya dauki matakai a kan gobara a kasuwar Kano

Farashin hatsi ya fadi sosai a Neja saboda kamfanoni na siyan kaya daga Chadi da Ghana, wanda ya kawo cikas ga manoman gida.

'Yan kasuwa da manoma sun yi kira ga gwamnatin Najeriya da ta dauki matakan da za su bunkasa hada hadar kayan hatsi na gida.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com