Liman da ke Hannun ’Yan Sanda Ya Fadi yadda Matashi Ya Mutu a Masallaci

Liman da ke Hannun ’Yan Sanda Ya Fadi yadda Matashi Ya Mutu a Masallaci

  • Wasu da ake zargi da kisan wani bawan Allah a masallacin Osogbo sun ce ba su da niyyar kashe shi kaddara ce
  • Sun bayyana cewa lamarin ya rikide ne bayan wasu fusatattun jama’a sun shiga tsakani bayan marigayin ya yi yunkurin kai wa limami hari
  • ’Yan sandan Osun sun ce an kama mutum biyar, kuma za a gurfanar da su gaban kotu bayan kammala bincike

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Osogbo, Osun – Ana ci gaba da tsare mutane biyar da ’yan sandan jihar Osun suka kama bisa zargin hannu a kisan wani bawan Allah a masallaci.

Marigayin mai suna Ahmed Adewale Najeem rasa ransa a masallacin Ummu-Hanni Adigun da ke yankin Ayedun Estate, Osogbo da aka ce ya yi yunkuri farmakin liman.

Kara karanta wannan

Abin takaici: An samu gawarwakin mawakan yabon addini 4 a wani irin yanayi

Yan sanda sun kama liman bayan kisan matashi a masallaci
Sufeta-janar na yan sanda, Kayode Egbetokun. Hoto: Nigeria Police Force.
Source: Facebook

Yadda matashi ya rasa ransa bayan salla

Mutanen da aka kama sun fadawa Tribune cewa ba su da niyyar kashe marigayin kawai wasu ne suka shiga lamarin har ya hargitse.

Wadanda ake zargin sun ce abin da suka yi kawai shi ne kokarin dakatar da Najeem ne domin kada ya cutar da limamin masallacin, Alhaji Abdulgafar Zakariyau.

Mutanen da aka kama sun hada da limamin masallacin Alhaji Zakariyau, da Abdulwasiu Olatunji, Kusamotu Akeem, Folorunso Mukaila, da Zakariyau Afeez.

Kakakin rundunar ’yan sandan jihar Osun, DSP Abiodun Ojelabi, ya tabbatar da kamen, inda ya ce lamarin ya faru ne ranar Juma’a, 30 ga watan Janairu, yayin sallar asuba.

A cewarsa, wani shugaban al’umma (Baale) ne ya kai rahoton cewa marigayin ya fara nuna wasu halayen na tsoro a lokacin sallar, inda ya lalata wasu kayayyaki a cikin masallacin, lamarin da ya sa wasu daga cikin masu ibada suka buge shi.

Kara karanta wannan

Ana zargin yaran Turji sun yi ajalin liman da basarake, jama'a sun tarwatse

An ce Najeem ya daga hannu kamar zai yi tambaya, amma sai ya yi yunkurin kwace sandar makirufo, ya cire wayoyin da ke hade da ita, sannan ya yi kokarin dukan limamin da sandar.

Liman ya magantu bayan rasa ran matashi a gefen masallacinsa
Taswirar jihar Osun da aka hallaka matashi a gefen masallaci. Hoto: Legit.
Source: Original

Yadda liman ya kare kansa yayin harin

Limamin ya kare kansa da hannu, amma Najeem ya sake yunkurin kai masa hari, lamarin da ya sa jama’a suka ruga kansa.

An ce bayan an fitar da shi daga masallacin, an jefa shi cikin magudanar ruwa, inda mutane da dama suka rika dukansa da sanduna da duk abin da suka samu a hannu.

An bayyana cewa kyamarorin CCTV da ke masallacin sun dauki dukkan abin da ya faru, lamarin da ya taimaka wa ’yan sanda wajen gano mutanen da ke da hannu a lamarin.

Limamin masallacin, Alhaji Zakariyau, ya bayyana cewa bai taba sanin marigayin ba a baya, kuma abin da ya faru ya girgiza shi matuka.

Ya ce ya gargadi jama’a da kada su doke shi, amma hayaniyar jama’a ta hana muryarsa fitowa, cewar Punch.

Wani daga cikin masu ibada, Mukaila, ya ce shi kawai ya buga Najeem da sanda a kafada ne domin rage masa karfi kafin isowar ’yan sanda, amma daga bisani wasu mutane suka shiga lamarin suka wuce gona da iri.

Kara karanta wannan

Malami da fararen hula 4 da aka kama da zargin hannu a yunkurin juyin mulki a Najeriya

Shi ma wani da ake zargi, Kusamotu, ya ce marigayin ya cije shi sau da dama yayin kokarin rike shi, lamarin da ya sa shi ma ya buge shi da sanda saboda fushi da radadin da ya ji.

DSP Ojelabi ya ce bayan kammala bincike, za a gurfanar da dukkan wadanda ake zargi a gaban kotu domin fuskantar hukunci bisa doka.

Yan sanda sun kama liman a masallaci

Kun ji cewa yan sanda sun kama liman da wasu mutane bayan lakadawa wani bawan Allah mai suna, Najeem Hammed duka har lahira.

Laamarin an ce ya faru ne a kusa da wani masallacin Juma'a a jihar Osun wanda ake zargin marigayn ya yi yunkurin kai farmaki kan liman.

Rahotanni sun nuna cewa lamarin ya auku ne lokacin da mutumin ya je sallar asubah, 'yan sanda sun kama limamin masallacin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.