'Ba Ruwan Gwamna': Gwamnatin Sokoto Ta Magantu kan ba Ƴar TikTok Gida da Mota

'Ba Ruwan Gwamna': Gwamnatin Sokoto Ta Magantu kan ba Ƴar TikTok Gida da Mota

  • Gwamnatin Jihar Sokoto ta yi magana bayan yada wani bidiyo da aka ba wata yar TikTok kyautar mota da shago
  • Gwamnatin ta nesanta Gwamna Ahmed Aliyu daga kyautar mota da shago da aka ba matashiya Rahama Saidu
  • Mai magana da yawun gwamnan, Abubakar Bawa, ya ce kyautar aikin kai ne na wani mutum, Sanin Jaman, domin nuna goyon baya ga Ahmed Aliyu

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Sokoto - Gwamnatin Jihar Sokoto ta bayyana cewa Gwamna Ahmed Aliyu ba shi da wata alaka da kyautar mota da shago da aka ba yar TikTok.

Kyautar da aka ba Rahama Saidu ya jawo maganganu musamman da ake alakanta kyautar da Gwamna Ahmed Aliyu.

Gwamnan Sokoto ya musanta ba yar TikTok kyautar mota, shago
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto. Hoto: Sokoto state Government.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da kakakin gwamnan, Abubakar Bawa, ya fitar, ya ce kyautar aikin kai ne na wani mai suna Sanin Jaman kawai, wanda aka wallafa a shafin gwamnatin jihar.

Kara karanta wannan

Harin Kwara: Kungiyar CAN ta tura muhimmin sako ga Musulmi da aka hallaka

An yi maganganu kan ba Rahama mota

Wannan lamari ya jawo maganganu a kafofin sadarwa yayin da wasu ke cewa an yi amfani da kudin talakawa ana raba wa yan TikTok.

Hakan ya dauki hankalin al'umma da dama inda suke bayyana rashin jin dadi game da yadda ake fifita wasu irin mutane da ke lalata tarbiyyar mutane.

Rahama Saidu: Sanarwar gwamnatin jihar Sokoto

Sanarwar ta ce an yi kyautar ne domin nuna jin dadi ga salon mulkin gwamnatin Ahmed Aliyu a Jihar Sokoto.

Gwamnatin ta jaddada cewa babu wata alaka tsakanin kyautar da ofishin gwamna ko kuma gwamnatin Jihar Sokoto gaba daya.

Ta gargadi mutane da su guji yin duk wata kyauta ko aiki da sunan gwamna ko gwamnati ba tare da tuntuba da izini ba.

Sanarwar ta sake nanata cewa kyautar lamari ne na kashin kai tsakanin mai bayarwa da Rahama Saidu da aka bai wa kyautar.

Gwamnatin Sokoto ta barranta kanta da kyauta ga Rahama Saidu
Gwamna Ahmed Aliyu na jihar Sokoto da yar TikTok, Rahama Saidu. Hoto: Sokoto state Government, Rahama Saidu.
Source: Facebook

Gwamnatin tana maraba da tallafin yan kasa

Kara karanta wannan

Tarihin yaron Shekau da ya jagoranci kashe Musulmai kusan 200 a Kwara

Gwamnatin ta ce tana maraba da tallafin ‘yan kasa nagari, amma ya kamata a bi hanyoyin da suka dace da manufofin ci gaban gwamnati.

Ta lissafa muhimman bangarori a cikin ajandar gwamnan, ciki har da tsaro, tarbiyya, bunkasa matasa, tsaftar muhalli da ilimi.

Sauran bangarorin sun hada da kiwon lafiya da kuma tallafa wa marayu, zawarawa da masu bukata ta musamman a fadin jihar.

Sanarwar ta kuma bayyana damuwar gwamnati kan halin da ‘yan gudun hijira ke ciki sakamakon hare-haren ‘yan bindiga a Sokoto.

Gwamnatin ta ce har yanzu akwai damar daidaiku da kamfanoni su taimaka wajen karfafa kokarin gwamnati na tallafa wa wadanda abin ya shafa.

Gwamnatin Sokoto na zargin Tambuwal da badakala

Mun ba ku labarin cewa kwamitin bincike a Sokoto ya zargi gwamnatin tsohon gwamna Aminu Waziri Tambuwal da almundahanar fiye da ₦117bn.

Rahoton ya nuna karya dokokin saye da sayarwa, cin zarafin ofis da gazawar wurin bin ka’idojin kudade a lokacin mulkinsa.

Gwamna Ahmed Aliyu ya ce za a kafa kwamiti na musamman domin daukar mataki cikin adalci, yana jaddada cewa binciken ba siyasa ba ne.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.