Abin Takaici: An Samu Gawarwakin Mawakan Yabon Addini 4 a Wani Irin Yanayi
- An shiga wan irin yanayi a Lagos bayan samun gawar fitaccen mawakin yavon addini da wasu ma'aikatansa guda uku
- ’Yan sanda sun ce babu alamun tashin hankali a jikin gawarwakin, kuma an kai su dakin ajiye gawa domin a yi binciken gawar
- An mika binciken lamarin ga sashen CID na jihar Legas, yayin da abokai da ’yan uwa ke neman a tabbatar da adalci
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Lagos – An samu gawar fitaccen mawakin wakokin bishara, Matthew Ogundele, tare da wasu mambobin tawagarsa guda uku.
Majiyoyi suka ce an same su sun mutu a cikin wani shagon rera wakoki a yankin Abraham Adesanya da ke Ajah, a jihar Lagos.

Source: Facebook
Mawakan yabon addini 4 sun mutu
Jaridar Punch ta ruwaito cewa an gayyaci mamatan ne domin gudanar da waka, a wani bangare na shirin yabon ranar haihuwa na kwanaki uku da wata mawakiya ta bishara, Olanireti Akinbola, ta shirya.
Rahotanni sun bayyana cewa sauran mutanen da suka rasu sun hada da Itunu Ogundele, Joseph Sanya, da kuma wani mai amfani kafar sadarwa mai suna Matthew Awosanya, wanda aka fi sani da JoesTv.
Wata majiya daga ’yan sanda ta ce bayan sun kammala wakar da daddare, tawagar ta yanke shawarar kwana a cikin shagon, inda aka gano gawarwakinsu washegari.
Majiyar ta ce:
“An gayyaci mawakan bishara da dama domin gudanar da hidima a wannan taron. Segun Praise ya zo da tawagarsa, kuma saboda sun yi latti, suka yanke shawarar kwana a studio. Washegari ne aka samu labarin cewa an same su sun mutu.”

Source: Original
Martanin rundunar yan sanda kan lamarin
Majiyoyi suka ce mamatan sun kasa komawa gidajensu ne saboda nisan hanya, shi ya sa suka kwana a wurin, inda aka ce sun mutu a cikin barcinsu.
Hotunan mamatan da ke yawo a kafafen sada zumunta sun nuna alamun jini a hanci, kunne da baki, lamarin da ya haifar da ce-ce-ku-ce kan musabbabin mutuwarsu.
Kakakin ’yan sandan Lagos, Abimbola Adebisi, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce mai shagon, Akintayo Akinbola, shi ne ya kai rahoton.
Ta ce Akintayo ya bayyana cewa ya bar mawakan a shago bayan ya sayo musu abinci, amma da ya dawo da safe sai ya tarar kofar a kulle daga ciki, bayan an fasa kofar ne aka gano gawarwakin mutum hudu a ciki.
Adebisi ta kara da cewa babu wata alamar ciwo a jikin gawarwakin, kuma an kai su Asibitin Mainland da ke Yaba, inda likita ya tabbatar da mutuwarsu, kafin a ajiye su a dakin ajiye gawa domin yin bincike, cewar Daily Post.
Mawakiyar yabon addini ta rasu
Kun ji cewa shahararriyar mawakiyar addini, Bunmi Akinaanu wadda aka fi sani da Omije Ojumi ta rasu a asibitin Legas tana da shekaru 46.
Mawakiyar ta rasu ne bayan shafe dogon lokaci tana fama da rashin lafiya da ya shafi kafarta, duk da tarin gudunmawar kudi da ta samu.
Masoya da yan uwa mawaƙa sun shiga jimami yayin da aka fito da wasu kyawawan halayenta da yadda wakokinta suka taba Kiristoci.
Asali: Legit.ng

