Gwamnatin Tinubu Ta Raba Kayan Abinci ga Jihohin Arewa 10 domin Rage Radadi
- Gwamnatin Tarayya ta ce shirin agajin abinci da gina jiki na gaggawa na Shugaba Bola Tinubu ya shafi jihohi 10 da rikice-rikice suka fi shafa
- Ministan jin kai, Dr. Bernard Doro, ya bayyana cewa shirin martani ne na kasa baki daya kan matsalolin tsaro da matsin tattalin arziki
- An kaddamar da rabon kayan abinci da magunguna a Maiduguri, inda Borno ta kasance cikin jihohin da suka fi cin gajiyar shirin
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Maiduguri, Borno - Ministan Harkokin Jin Kai da Rage Talauci, Dr. Bernard Doro, ya kaddamar da shirin rabon abinci ga jihohi 10.
Doro ya bayyana cewa shirin gaggawa na rarraba abinci da gina jiki na Shugaba Bola Tinubu ya shafi jihohi 10 da rikice-rikicen jin kai suka fi shafa a Najeriya.

Source: Twitter
An fara rabon kayan abinci a Najeriya
Ministan ya bayyana hakan ne a Maiduguri yayin kaddamar da rabon kayan abinci da wadanda ba na abinci ba ga wadanda rikicin Boko Haram ya shafa a Borno wanda shafin ma'aikatar ya wallafa a Facebook.
A cewarsa, jihohin da shirin ya kunsa sun hada da Borno, Adamawa, Yobe, Benue, Niger, Plateau, Katsina, Zamfara, Sokoto da Kebbi, inda al’umma ke fama da matsanancin kalubale sakamakon rikice-rikice da matsin rayuwa.
Dr. Doro ya ce shirin wani tsari ne na hadin gwiwar kasa baki daya domin tinkarar matsaloli daban-daban da suka hada da tashe-tashen hankula, sauyin yanayi da kuma matsin tattalin arziki da ke addabar ‘yan kasa.
Ya kara da cewa Gwamnatin Tarayya ta amince tare da samar da dimbin kayan abinci da na gina jiki a fadin kasar nan, ciki har da shinkafa, wake, gero, masara, man girki, kayan gina jiki masu kara kuzari da kuma muhimman magunguna daban-daban.

Source: Facebook
Dalilin fara rabon kayan abinci a Borno
Ministan ya jaddada cewa Jihar Borno na daga cikin jihohin da suka fi samun fifiko, sakamakon dogon lokacin da aka shafe ana gudun hijira da kuma rugujewar tattalin arziki da zamantakewa da rikici ya haddasa.
Ya ce wannan shiri ba wai na gaggawar agaji kadai ba ne, illa kokari ne na kare rayukan jama’a, dawo da martabar su, da kuma shimfida tubalin dogaro da kai, samar da abinci a cikin gida da gina juriyar tattalin arziki.
A nasa bangaren, mukaddashin gwamnan Jihar Borno, Dr. Umar Usman, ya ce tallafin ya zo a kan lokaci mai matukar muhimmanci, inda zai taimaka wajen rage radadin rayuwa da wahalhalun da ‘yan gudun hijira da iyalai masu rauni ke fuskanta.
Sanata ya raba tirelar abinci 490
Mun ba ku labarin cewa Sanata Abdulaziz Yari ya raba kayan abinci ga mabukata a fadin jihar Zamfara domin saukaka musu wahala a watan Ramadan.
Kayan abincin da suka hada da shinkafa, gero, masara da sukari za a rabawa jama'a a kananan hukumomi 14 da ke Zamfara.
Biyo bayan lamarin, jama’a sun nuna godiya ga Sanata Yari, tare da bukatar sauran ‘yan siyasa su yi koyi da shi wajen raba tallafi.
Asali: Legit.ng


