Harin Kwara: Kungiyar CAN Ta Tura Muhimmin Sako ga Musulmi da Aka Hallaka
- Kungiyar CAN ta Arewa ta yi kakkausar suka kan kisan gillar da aka yi a Kwara, tana bayyana harin a matsayin rashin tausayi
- Kiristocin sun jaddada cewa lamarin bala’i ne na kasa baki ɗaya, ba na addini ko kabila ba, CAN tana kira da a guji nuna bambanci
- CAN ta yabawa Shugaba Bola Tinubu da jami’an tsaro kan daukar matakin gaggawa, amma ta bukaci gwamnati ta kara tsaurara matakai
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kwara - Kungiyar Kiristoci ta Najeriya (CAN) a jihohin Arewa 19 da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja ta yi magana kan hari a Kwara.
Kungiyar ta yi kakkausar suka kan kisan gillar da aka yi wa wasu Musulmai kusan 200 a jihar Kwara wanda ya tada hankula.

Source: Facebook
CAN ta magantu kan harin Kwara
Shugaban CAN a Arewacin Najeriya, Rabaran Joseph John Hayab, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce kungiyar ta shiga jimami tare da al’ummar Kwara kan asarar rayukan da aka yi, cewar The Sun.
Kungiyar ta bayyana harin a matsayin abin tausayi da rashin imani, tare da nuna cikakken goyon baya ga al’ummar Musulmi da kuma iyalan wadanda suka rasa rayukansu sakamakon wannan mummunan lamari.
Rahotanni sun nuna cewa mutane da dama sun mutu yayin da ’yan bindiga suka kai hari wasu al’ummomi a karamar hukumar Kaiama, lamarin da ya jikkata mutane da dama tare da lalata gidaje da gonaki.
Ya ce:
“Wannan hari mugunta ce, mara dalili kuma yana nuna irin manyan kalubalen tsaro da ke addabar kasarmu. Muna Allah-wadai da shi matuka, muna kuma jimami tare da iyalan da suka rasa ’yan uwansu.”

Source: Original
Kungiyar CAN ta taya Musulmi jimami a Kwara
Rabaran Hayab ya jaddada cewa CAN ta Arewa na tare da al’ummar Musulmi, yana mai cewa wadanda aka kashe bayin Allah ne marasa laifi da aka katse rayuwarsu ta hanyar rashin imani.
Ya ce:
“Muna tare da ’yan uwammu Musulmi da kuma daukacin al’ummar jihar Kwara a wannan lokaci na bakin ciki. Wannan radadi ba na bangare guda ba ne, bala’i ne na kasa baki daya.”
Shugaban CAN ya ce babu wani addini da ke koyar da kashe rayukan bayin Allah marasa laifi, yana mai gargadin cewa bambance-bambancen addini ko kabila bai kamata ya zama dalilin zubar da jini ba, cewar Vanguard.
Har ila yau, Rabaran Hayab ya yabawa Shugaba Bola Tinubu da hukumomin tsaro bisa daukar matakin gaggawa, musamman tura rundunar sojoji zuwa jihar karkashin 'Operation Savannah Shield'.
'Yan ta'adda sun yaudari Musulmi da kiran sallah
Mun ba ku labarin cewa mazauna garuruwan Woro da Nuku a jihar Kwara na ci gaba da bayyana abin da suka gani lokacin da 'yan ta'adda suka kai kasu farmaki.
Majiyoyi sun nuna cewa maharan sun kashe sama da mutum 100 a harin kuma duk Musulmai saboda sun ki karbar sabuwar akida.
Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan sun yi amfani da masallaci wajen yaudarar jama'a su fito ta hanyar kiran sallah.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

