Buhari: Watanni bayan Rasuwarsa, Jami'a Ta Karrama Tsohon Shugaban Kasa

Buhari: Watanni bayan Rasuwarsa, Jami'a Ta Karrama Tsohon Shugaban Kasa

  • Marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ya samu digirin karramawa daga jami'ar Umaru Musa Yar'adua da ke Katsina
  • An karrama marigayi tsohon shugaban Najeriyan ne a yayin bikin yaye daliban jami'ar karo na 14 da aka gudanar a birnin Katsina
  • Mahukuntan jami'ar sun bayyana cewa marigayin ya samu karramawar ne saboda gudunmawar da ya ba da wajen bunkasa fannin ilmi a lokacin da yake raye

​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Katsina - Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU), Katsina, ta karrama marigayi shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Jami'ar UMYUK ta karrama marigayi Buhari ne da digirin girmamawa na digirin digir a fannin Kimiyyar Siyasa bayan rasuwarsa.

Jami'ar UMYUK ta karrama marigayi Buhari
Tsohon shugaban kasar Najeriya, marigayi Muhammadu Buhari Hoto: Muhammadu Buhari
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ce an karrama Buhari ne a lokacin bikin yaye dalibai karo na 14 na jami'ar da aka gudanar ranar Asabar, 7 ga watan Fabrairun 2026 a Katsina.

Kara karanta wannan

Tashin hankali: An gano wani bam da 'yan bindiga suka dasa wa mutane a Zamfara

Jami'ar UMYUK ta karrama Muhammadu Buhari

Karramawar da aka yi wa tsohon shugaban kasar ta samu amincewar majalisar gudanarwa ta jami'ar.

Mahukuntan jami’ar sun ce an yi wannan karramawa ne domin girmama jajircewar marigayi shugaban kasar tsawon rayuwarsa wajen cigaban siyasar Najeriya, da nagartaccen shugabanci, da kuma ƙoƙarinsa na tabbatar da haɗin kan ƙasa da cigaba.

Sun bayyana cewa tarihin Buhari, musamman gudumawarsa mai yawa wajen bunƙasa da ƙarfafa bangaren ilimin manyan makarantu a ƙasar, ya sa ya cancanci wannan girmamawa bayan rasuwarsa.

Meyasa aka karrama marigayi Buhari?

A cewar jami’ar, an yanke shawarar karrama tsohon shugaban kasar ne domin tunatar da al’umma manyan nasarorin da ya samu a harkokin mulki da gina kasa.

Jami’ar ta ce wadannan nasarori za su zama darasi da abin koyi ga shugabannin Najeriya na yanzu da masu zuwa nan gaba.

An ba daliban da jami'ar ta yaye shawara

Da yake jawabi a madadin sauran waɗanda aka karrama, tsohon shugaban hukumar leken asiri ta kasa (NIA), Ambassada Ahmad Rufa’i, ya shawarci daliban da suka kammala karatu da su kasance masu kaunar kasa, gaskiya da sadaukarwa ga hidimar kasa ba tare da son kai ba.

Kara karanta wannan

Tun kafin a yi nisa, an sauke gwamna daga matsayin shugaban kwamitin taron APC na kasa

Jami'ar UMYUK ta karrama Buhari da digirin digir
Gwamna Dikko Radda na Katsina, Hadi Sirika da wasu manyan mutane a wajen yaye daliban UMYUK Hoto: Ibrahima Kaulaha Mohammed
Source: Facebook

Ambassada Ahmad Rufa’i ya kuma bukaci daliban da su yi amfani da ilimin da suka samu wajen gina al’umma mai haɗin kai, inda kowa zai rayu cikin mutunci, zaman lafiya da samun damarmaki a rayuwa.

Bikin yaye daliban ya kuma shaida bayar da digiri da takardun shaidar kammala karatu ga dalibai daga fannoni daban-daban, tare da karrama wasu mutane da digirorin girmamawa saboda gagarumar gudummawarsu ga ci gaban ƙasa.

Aisha Buhari ta ziyarci Atiku Abubakar

A wani labarin kuma, kun ji cewa uwargidar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ta ziyarci Alhaji Atiku Abubakar.

Aisha Buhari ta kai wa tsohon mataimakin shugaban kasar ziyarar ban girma ne a kasar Saudiyya yayin da suke aikin Umrah.

Tsohuwar uwargidan shugaban kasar na Najeriya ta samu rakiyar wasu daga cikin iyalanta, ciki har da ɗiyarta, Hanan Muhammadu Buhari zuwa masaukin Atiku a kasa mai tsarki.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng