'Yan Bindiga Sun Kashe Bayin Allah, Sun Sace Babban Malami da Wasu Mutane 10

'Yan Bindiga Sun Kashe Bayin Allah, Sun Sace Babban Malami da Wasu Mutane 10

  • Yan bindiga sun kai farmaki garin Karku da ke karamar hukumar Kauru a Jihar Kaduna, inda suka kashe akalla mutane uku
  • Rahotanni sun tabbatar dacewa 'yan ta'addan sun yi awon gaba da babban limamin Katolika na garin, Rabaran Nathaniel Asuwaye tare da mutum 10
  • A wata sanarwa da cocin ya fitar, ya bukaci mabiyanta da sauran al'umma su dage da addu'a domin kubutar da wadanda aka sace

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna, Nigeria - Wasu mahara da ake zargin 'yan bindiga ne sun yi garkuwa da wani babban limamin coci na darikar Katolika, Rabaran Nathaniel Asuwaye, tare da wasu mutane 10 a jihar Kaduna.

Maharan sun yi awon gaba da malamin cocin ne a wani hari da suka kai garin Karku da ke karamar hukumar Kauru a Jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Rashin imani: Yadda 'yan ta'adda suka kira Sallah, suka kashe duk wanda ya zo Masallaci

Jihar Kaduna.
Taswirar jihar Kaduna da ke Arewacin Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren cocin Katolika na Kafanchan, Rev. Fr. Jacob Shanet, ya fitar ranar Asabar, kamar yadda Leadership ta kawo.

'Yan bindiga sun kashe mutane 3 a Kaduna

Ya bayyana cewa mazauna garin sun kwatanta maharan a matsayin gungun 'yan ta'adda, wadanda suka far wa garin cikin wani tsari na daban.

Sanarwar ta bayyana cewa harin ya yi sanadin mutuwar mutane uku (3), wadanda aka gano sunayensu kamar haka: Mista Jacob Dan’azumi, Mista Maitala Kaura da Alhaji Kusari

Bayan halaka wadannan mutane, yan bindigan sun kuma kwashe mutane 11 zuwa cikin daji ciki har da limamin cocin Katolika.

Kamar yadda sanarwar ta nuna, lamarin ya faru ne a sa'o'in farko na ranar Asabar, 7 ga Fabrairu, 2026, da misalin karfe 3:20 na asuba a gidan limamin.

An yi garkuwa da limamin Katolika a Kaduna

Bayanai sun nuna cewa Rabaran Asuwaye shi ne limamin cocin Holy Trinity Catholic Church da ke Karku wacce ke karkashin cocin Kafanchan a jihar Kaduna.

Kara karanta wannan

Matasa sun taru sun kashe tsohon mai gadin fadar mai martaba Sarki, sun kona gawarsa

Cocin Katolika ta nuna matukar alhininta kan wannan lamari, inda ta yi kira ga sauran limamai, mambobin coci, da daukacin mutanen kirki da su dukufa da addu'o'i domin ganin an sako Fabaran Asuwaye da sauran wadanda aka sace cikin koshin lafiya.

Haka kuma, ta yi addu'ar samun sauki da rahama ga wadanda suka rasa rayukansu a lokacin wannan harin, kamar yadda Punch ta ruwaito.

Gwamnan Kaduna.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani yayin tattaunawa da kwamishinoni Hoto: Uba Sani
Source: Twitter

Sanarwar ta ƙara da sanya waɗanda abin ya shafa a addu'a ta musamman mai albarka, yayin da take kira da a ci gaba da yin addu'a a yayin da yanayin tsaro ke ƙara taɓarɓarewa a sassan Jihar Kaduna.

Mahara sun sace limamin Juma'a a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa yan bindigan sun sace babban limamin masallacin Juma'a na kauyen Janjala, Malam Bello Abdullahi da ke karamar hukumar Kagarko ta jihar Kaduna.

Rahoton ya nuna cewa 'yan bindigan sun sace Malam Bello Abdullahi ne tare da wani jagoran Fulani a yankin, Alhaji Shehu Bello da kuma wata mata.

Wani shugaban al’umma da ke yankin ya tabbatar da aukuwar harin na 'yan bindiga a ranar Laraba, 4 ga watan Fabrairun 2026.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262