Gwamna Na cikin Matsala bayan Taso Shi a Gaba Sai Ya Yi Murabus, an Ji Dalili

Gwamna Na cikin Matsala bayan Taso Shi a Gaba Sai Ya Yi Murabus, an Ji Dalili

  • Wata kungiya daga jihar Kogi ta taso Gwamna Ahmed Usman Ododo da ya yi murabus daga kan mukaminsa
  • Kungiyar ta nuna cewa gwamnan ya kasance dan amshin shatan magabacinsa, Yahaya Bello wanda yake fuskantar shari'a
  • Ta yi zarge-zargen da ke nuna cewa bai kamata gwamnan ya ci gaba da jan ragamar mulkin jihar Kogi ba

​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Kogi - Kungiyar Movement for the Emancipation of Kogi State (MEKSTA) ta bukaci Gwamnan jihar Kogi, Usman Ododo, da ya yi murabus.

Kungiyar MESKTA ta zargi Gwamna Ododo da hannu a cikin zargin cin hanci da rashawa da ake dangantawa da gwamnatin tsohon gwamna Yahaya Bello.

Kungiya na son Gwamna Ododo ya yi murabus
Gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Usman Ododo Hoto: Alhaji Yahaya Usman Ododo
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta kawo rahoton cewa hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kungiyar fitar ranar Asabar, 7 ga watan Fabrairun 2026.

Kara karanta wannan

Bayan jiran kusan shekaru 50, Uba Sani ya kaddamar da hanya a kauyukan Kaduna

Meyasa ake so Gwamna Ododo ya yi murabus?

Kungiyar ta MEKSTA ta bayyana Gwamna Ododo a matsayin dan amshin shatan tsohon gwamna Yahaya Bello.

Ƙungiyar ta ce rawar da Ododo ya taka a baya a matsayin mai binciken kudi na kananan hukumomi a lokacin mulkin Yahaya Bello ta haifar da manyan tambayoyi kan gaskiyarsa da jajircewarsa wajen gaskiya da rikon amana.

A cewar MEKSTA, ci gaba da zaman Ododo a kan karagar mulki na raunana bin diddigi, inda ta yi zargin cewa almundahana ta yi yawa a kudaden kananan hukumomi a lokacin da yake rike da mukamin mai binciken kudi.

Ƙungiyar ta kuma ce an dade ana tauye adalci a jihar, tana zargin masu rike da madafun iko da watsi da nauyin kundin tsarin mulki domin cin hanci, lamarin da ta ce ya hana ci gaba tare da raunana amincewar jama’a ga gwamnati.

An yi zargi kan Gwamna Ododo

MEKSTA ta yi zargin cewa zaman Gwmana Ododo a matsayin zabin Yahaya Bello a zaben shekarar 2023 na da nufin kare ayyukan da ake ta cece-kuce a kansu tare da boye barnatar da kudade, shafin Kogireports ya kawo labarin.

Kara karanta wannan

Tambuwal ya shiga uku, gwamnatin Sokoto ta taso shi a gaba kan 'badakalar' da N117bn

Haka kuma, ƙungiyar ta yi zargin cewa Ododo na kokarin tasiri kan bincike da shari’o’i da ke gudana da suka shafi Ali Bello, shugaban ma’aikatansa kuma dan uwan tsohon gwamnan.

“Waɗannan ayyuka suna nuna mummunan yanayin mulki a jihar Kogi, kuma suna haifar da muhimman tambayoyi kan gaskiya, adalci da shugabanci."

- Kungiyar MEKSTA

Kungiyar MEKSTA ta bukaci Gwamna Ododo ya yi murabus
Gwamna Ahmed Usman Ododo na jihar Kogi Hoto: Alhaji Ahmed Usman Ododo
Source: Facebook

Kungiya na son Ododo ya yi murabus

MEKSTA ta ce ya kamata Gwamna Ododo ya yi murabus domin maslahar adalci da walwalar al’ummar jihar Kogi.

“Duba da wannan mummunan yanayi, MEKSTA ta dauki matsaya tare da kiran gwamnan da ya yi murabus."
"Idan da gaske gwamnan na tsayawa kan tabbatar da jin dadin jama’a, to murabus shi ne hanyar mutunci da ta gare masa."

- Kungiyar MEKSTA

Sanarwar ta samu sa hannun Obafemi Medaiyese, Joseph Mebatonije, Yusuf Kpareke, Jimoh Ozovehe, Nurudeen Adaviriku, Isiaka Momoh, Ojonimi Adegbe, Mark Onucheyo da Husseini Saidu, wakilan mazabun tarayya daga sassa daban-daban na jihar.

Gwamna Ododo ya umarci rufe makarantu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin jihar Kogi karkashin jagorancin, Yahaya Usman Ododo, ta ba da umarnin rufe makarantu.

Kara karanta wannan

An biyo kan masu shara: Gwamna ya yi barazanar korarsu kan rijistar zama yan APC

Gwamnatin ta Kogi ta sanar da rufe dukkan makarantu na firamare da sakandare na jihar nan take saboda dalilai na tsaro.

Daukar wannan matakin ya biyo bayan umarnin gaggawa da gwamnati ta bayar domin kiyaye rayukan ɗalibai da malamai a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng