Rashin Imani: Yadda 'Yan Ta'adda Suka Kira Sallah, Suka Kashe duk Wanda Ya Zo Masallaci
- Mazauna garuruwan Woro da Nuku a jihar Kwara na ci gaba da bayyana abin da suka gani lokacin da 'yan ta'adda suka kai kasu farmaki
- Rahoto ya nuna cewa maharan sun kashe sama da mutum 100 a harin kuma duk musulmai saboda sun ki karbar sabuwar akida
- Bayanai sun nuna cewa yan ta'addan sun yi amfani da masallaci wajen yaudarar jama'a su fito ta hanyar kiran sallah
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kwara, Nigeria - Bayanai na ta kara fitowa kan yadda yan ta'adda suka yi wa mutane sama da 100 kisan rashin imani a kauyukan Woro da Nuku a jihar Kwara.
Wasu rahotanni sun nuna cewa lamarin ya faru ne da yammaci lokacin da manoma suka fara dawowa daga gona, yayin da wasu ’yan kasuwa ke kokarin rufe shagunansu.

Source: Original
A rahoton The Nation, wani malamin makaranta mai shekaru 26, Umar Bio Kabir, ya ce mutane na kokarin komawa gida, kuma wannan lokacin ne matasa suka saba fara wasan tamola.
Yadda yan ta'adda suka mamayi mutane
Kwatsam, sai ga ayarin wasu mutane dauke da makamai a kan babura suka kutsa kai cikin garin Woro, da ke karamar hukumar Kaiama a Jihar Kwara, a ranar Talatar da ta gabata.
Mazauna garin sun ce babu bukatar wani gargadi ko tantama; nan take kowa ya gane ko su wanene wadannan baki da kuma abin da suka zo nema.
A cewar mazauna yankin, cikin kankanin lokaci, kasuwa ta rude, filin wasan kwallo ya watse, sannan tituna suka cika yayin da jama’a ke gudun ceton rai.
Umar Kabir, mai shekaru 26, ya ranta a na kare tare da abokansa don tsira daga harsashin bindiga, amma ya ce wasu daga cikin samarin da suke buga kwallo tare ba su yi sa'a ba; harsashin maharan ya raba su da rayuwarsu.
Kabir ya ce:
"Allah ya kaddara zan rayu, in ba haka ba da yanzu ina daya daga cikin wadanda aka birne."
Gwamnati da jami’an tsaro sun tabbatar da cewa wadannan maharan ’yan ta’adda ne, wadanda suka kai harin saboda mazauna garin sun ki amincewa da "bakuwar akidarsu."

Source: Twitter
Yadda maharan suka yi amfani da masallaci
Wani wanda ya tsira, Razaq Abdulazeez, ya ce yana kan hanyar komawa gida ne ya ga mutane na gudu daga kauyen. Da jin abin da ke faruwa, ya ruga gidansa don ceton iyalinsa.
Abdulazeez ya kara da cewa mutane da dama da ba su samu damar guduwa ba sun hau kan bishiyoyi don boyewa, cewar rahoton Vanguard.
Wani rahoton hukuma ya bayyana cewa, a daya daga cikin kauyukan, ’yan ta’addan sun shiga masallaci suka yi kiran salla, sannan suka harbe duk wanda ya amsa kiran ya zo masallacin.
Tinubu ya tura bataliyar sojoji Kwara
A wani labarin, kun ji cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin tura bataliyar sojoji zuwa Woro a karamar hukumar Kaiama, domin dakile hare-haren yan ta'adda.

Kara karanta wannan
Attajiri lamba 1 a duniya, Elon Musk ya bayyana abin da kudi ba za su iya saye ba
Shugaban kasar ya yi kakkausar suka kan harin,m da kai Woro, inda ya bayyana shi a matsayin abin kunya da rashin tausayi.
Ya ce manufar tura sojojin ita ce tabbatar da tsaro mai dorewa a yankin da kuma hana sake aukuwar irin wannan mummunan hari.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

