Tinubu Ya Tura Shettima Kwara da Muhimmin Sako bayan Kisan Musulmai

Tinubu Ya Tura Shettima Kwara da Muhimmin Sako bayan Kisan Musulmai

  • Kashim Shettima ya isa birnin Ilorin domin jajanta wa al’ummar Woro bayan kisan gilla da ya yi sanadiyyar rasa rayukan sama da mutum 100
  • Ziyarar ta zo ne bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na tura rundunar sojoji zuwa yankin da abin ya faru domin daƙile ta’addanci
  • Ana sa ran Shettima zai gana da sarakuna, jami’an tsaro da sauran masu ruwa da tsaki domin tattauna hanyoyin dawo da zaman lafiya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kwara – Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya isa Ilorin, babban birnin jihar Kwara, domin jajanta wa gwamnati da al’ummar jihar bisa mummunan harin da aka kai a ƙauyen Woro da ke ƙaramar hukumar Kaiama.

Rahotanni sun nuna cewa harin, wanda ake zargin ‘yan Boko Haram ne suka kai, ya yi sanadiyyar rasa rayukan sama da mutum 100, tare da lalata gidaje da kadarori masu yawa a yankin.

Kara karanta wannan

Yadda ƴan ta'adda suka rubuta wa Sarki wasiƙu kan shirin hari kafin hallaka Musulmai a Kwara

Mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima
Yadda aka ajiye gawa a Woro da Kashim Shettima a dama. Hoto: Light Oriye Tamunotonye|Kashim Shettima
Source: Facebook

Hadimin Sanata Kashim Shettima, Stanley Nkwocha ya wallafa bidiyon isar mataimakin shugaban kasa Kwara a shafinsa na X.

Kashim Shettima ya isa jihar Kwara

Shettima ya sauka ne a filin jirgin sama na Tunde Idiagbon da ke Ilorin, inda Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, tare da Sanatan Kwara ta Arewa, Sadiq Umar, da sauran manyan jami’an gwamnati suka tarbe shi.

Rahotanni sun bayyana cewa ziyarar na da nufin nuna goyon bayan gwamnatin tarayya ga al’ummar da abin ya rutsa da su, tare da jajanta musu kan irin wannan mummunan lamari da ya girgiza jihar.

Ziyarar ta Mataimakin Shugaban Ƙasar ta biyo bayan umarnin Shugaba Bola Ahmed Tinubu na ɗaukar matakan gaggawa domin magance matsalar tsaro da kuma nuna alhini ga iyalan waɗanda abin ya shafa.

Abin da Shettima zai yi a Kwara

TVC ta wallafa cewa ana sa ran Mataimakin Shugaban Ƙasar zai gana da sarkin gargajiya na Woro, Sarkin Kaiama, jami’an ƙaramar hukuma, da kuma shugabannin tsaro domin tattauna halin da ake ciki.

Kara karanta wannan

Tarihin yaron Shekau da ya jagoranci kashe Musulmai kusan 200 a Kwara

Haka zalika, ganawar za ta mayar da hankali ne kan matakan da za a ɗauka domin dawo da zaman lafiya, tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi, da kuma hana sake faruwar irin wannan hari a nan gaba.

Tun da farko, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bayar da umarnin gaggawa na tura rundunar sojoji mai ƙarfi zuwa yankin da harin ya afku. Matakin na da nufin murƙushe ‘yan ta’adda da kuma kare sauran al’ummomi da ke yankin.

Yadda aka birne mutane a Woro
Yadda aka yi jana'izar Musulman da aka kashe a Kwara. Hoto: Reuters|BBC
Source: Facebook

Shugaban ya bayyana cewa gwamnan jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaq, ya riga ya yi masa cikakken bayani kan harin da ya faru a Woro, inda ya nuna alhini tare da ta’aziyya ga iyalan waɗanda suka rasa rayukansu.

Bidiyon isar Shettima Kwara:

Yaron Shekau ya kashe Musulmai

A wani labarin, kun ji cewa yaron tsohon shugaban 'yan ta'addan Boko Haram Abubakar Shekau, Abubakar Sadiq ya ne ya kai hari Kwara.

Wani rahoto ya nuna cewa Abubakar Sadiq ya shafe shekaru yana ta'addanci tare da Abubakar Shekau a Arewa maso Gabas.

An bayyana cewa dan ta'addan ya koma rayuwa Arewa ta Tsakiya bisa umarnin shekau domin fadada ta'addancin Boko Haram.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng