Yadda Ƴan Ta'adda Suka Rubuta wa Sarki Wasiƙu kan Shirin Hari kafin Hallaka Musulmai
- ‘Yan ta’adda sun aika wasiƙa ga al’ummar Nuru da Woro a Kwara, suna sanar da niyyarsu ta wa’azi kafin kai hari mai muni
- Akalla mutane kusan 200 sun mutu, gidaje da dama sun ƙone, yayin da gwamnan Kwara ya danganta harin da tsattsauran ra’ayin addini
- Basarake ya ce an sace iyalansa, yara biyu suka mutu, inda ‘yan ta’addan suka bukaci jama’a su guji gwamnatin Najeriya
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kwara - Rahotanni sun bayyana cewa ‘yan ta’adda sun rubuta wasiƙa ga mazauna Nuru da Woro a jihar Kwara, suna bayyana shirin wa’azi kafin kai hari.
A ranar Laraba 4 ga watan Fabrairun 2026, akalla mutane 200 ne suka rasa rayukansu, yayin da aka kona gidaje da dama lokacin harin da aka kai a karamar hukumar Kaiama.

Source: Facebook
Gwamnatin Kwara ta gano dalilin hari a jihar
Gwamnan Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya danganta hare-haren da ‘yan tsattsauran ra’ayin addinin Musulunci da ke kokarin tayar da tarzoma, cewar TheCable.
Shugaba Bola Tinubu daga bisani ya bayar da umarnin tura rundunar sojoji ta bataliya zuwa yankin domin magance barazanar tsaro.
Har ila yau, Gwamna Abdul Rahman AbdulRazaq na Kwarai ya niki gari zuwa fadar shugaban kasa inda ya gana da Bola Tinubu domin neman mafita.

Source: Original
Wasikar da Sarki ya samu daga yan ta'adda
BBC ta ruwaito cewa ‘yan ta’addan sun aike da wasiƙa ga Sarkin Woro, Umar Bio Salihu, suna sanar da shi manufarsu.
An ce koyarwarsu tana da alaƙa da tsattsauran ra’ayi, wanda ya saba da fahimtar addinin Musulunci da yawancin mazauna yankin ke bi.
Salihu, wanda ba ya gida lokacin harin, ya ce ‘yan ta’addan sun fara zuwa gidansa inda suka sace matarsa da ’ya’yansa.
Abin da basaraken ya tarar a gidansa
Da ya dawo, ya tarar da gidansa ya ƙone kurmus, tare da gano gawarwakin yara biyu daga cikin ‘ya’yansa da aka kashe.
Ya ce ‘yan ta’addan sun bukaci al’umma su guji gwamnatin Najeriya su bi koyarwarsu, yana mai cewa hakan ya saba da koyarwar Alkur’ani.
Wani mazaunin Woro, Abdulla Umar Usman, ya ce ‘yan ta’addan sun shigo ƙauyukan da yawa, suna kai farmaki ba tare da tausayi ba.
Ya ce an kashe 'ya’yan basaraken biyu wadanda dalibai ne a bangaren likitanci a gaban gidansu kafin ‘yan ta’addan su banka masa wuta.
Lamarin ba a cewa komai - Mazaunin Kaiama
Wani malami da yake zaune a garin Kaiama, inda 'yan ta'addan suka yi wannan barna ya bayyana cewa ta'adin da suka gani ya yi muni ainun.
Ba tare da ya bari an kama sunansa ba, malamin makarantar ya shaida wa Legit Hausa cewa adadin wadanda aka hallaka za su iya zarce 200.
A cewarsa, jami'an tsaro sun yi nasarar fara kama wasu mutane shida da ake zargi da hannu a kashe mutane a kauyukan na Kaima a makon nan.
Yaron Shekau ya kashe Musulmi a Kwara
Mun ba ku labarin cewa majiyoyi sun gano cewa kisan gillar da aka yi wa Musumai kusan 200 a Woro da ke karamar hukumar Kaiama ta Kwara na da alaƙa da tsattsauran ra'ayi.
Rahotanni sun danganta harin da Abubakar Saidu, wanda aka fi sani da Sadiku, wani babban dan ta'adda da ke da alaka da Abubakar Shekau.
Masana tsaro sun ce kwararan shaidu na nuna yadda yankin Kainji ya zama sabuwar mafakar ‘yan ta’adda a Arewa ta Tsakiyan Najeriya.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


